'Zan Kare Kai Na': An Hango Sheikh Bello Yabo Dauke da Bindiga a Wajen Wa'azi
- Sheikh Muhammad Bello Yabo ya janyo cece-kuce bayan bullar wani bidiyo da aka ga malamin yana wa’azin addinin rike da bindiga
- Malamin ya ce idan har yana rike da bindiga, to babu wani bata gari da zai iya firgita shi, yana mai cewa a shirye yake ya kare kansa
- Yayin da wasu ke goyon bayan aikin malamin na kare kansa daga 'yan bindiga, wasu na ganin hakan zai iya tayar da zaune tsaye
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Babban malamin Musulunci a Sokoto, Sheikh Muhammad Bello Yabo, ya tayar da kura bayan an ganshi a cikin wani bidiyo dauke da bindiga yayin da yake wa'azi.
Bidiyon na mintuna biyu da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna malamin yana nuni ga jama’a da su kare kansu daga hare-haren miyagun 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan
'Ni kaɗai zan yi': Sarki ya haramta layya saboda tsadar rayuwa, zai yi wa ƴan kasa

Source: Facebook
"Ba na jin tsoron mutuwa" - Bello Yabo
Sheikh Bello Yabo wanda aka fi sani da yin wa’azi mai zafi da sukar gwamnati, ya ce ya shirya kare kansa, domin babu wanda zai tunkare shi idan da bindiga a hannunsa, inji rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da ya yake rike da bindigar a hannunsa, malamin ya nuna bukatar al’umma su dauki matakan kare kai, yana mai jaddada cewar rashin tsaro ya yi kamari a kasar.
“Ba na jin tsoron mutuwa ko da a daren nan ne. Amma duk wanda ya zo neman raina, ya tabbata ya shirya. Ga abin a hannuna.”
- Sheikh Bello Yabo.
Yayin da ya ke jinjina bindigar da ke hannunsa, Bello Yabo ya kara da cewa:
“Muddin ina da wannan, ban ga wanda ke da wuƙa da zai iya taɓa ni ba ko da yana cikin maye ne. Amma idan ya gwada, to ni ma na shirya.”
Martanin mutane bayan ganin Yabo da bindiga
Bayyanar bidiyon ya haddasa cece-kuce a fadin Najeriya. Masu mara masa baya na cewa hakan da ya yi ya nuna yadda ake fama da matsin lamba daga ‘yan ta’adda.
Sai dai wasu na sukar yadda malamin ya fito da bindiga a wurin wa'azi, suna masu cewa hakan na iya tayar da zaune tsaye ko gurbata tunanin matasa.
@Lewis0075 ya rubuta cewa:
“Wannan shi ne mafita. Gwamnati ba za ta iya kare mutane ba. Wawa ne kawai zai ajiye makami yana jiran ɗan ta'adda ya ajiye nashi.”
@mayorlistik ya ce:
“An kama wani fasto da ya yi irin hakan a baya. Muna jira mu gani ko za a kama wannan malamin Musuluncin yanzu.”

Source: UGC
Wanne hukunci za a dauka kan Bello Yabo?
Sokoto na daya daga cikin jihohin da suke fama da hare-haren ‘yan bindiga, inda ake yawan samun sace-sace da kashe-kashe a kauyuka da ma cikin birnin.
Har yanzu dai babu wata sanarwa daga gwamnatin jihar Sokoto ko hukumomin tsaro dangane da bidiyon Sheikh Bello Yabo, kuma ba a tabbatar ko za a hukunta malamin ko a’a ba.
Yayin da ake ci gaba da tattauna batun, ’yan Najeriya na sa ido kan ko wannan batu na Sheikh Yabo zai janyo sauyi ko ya kara rura wutar rashin tsaro a kasar.
Alakar Bello Yabo da marigayi Dr. Idris
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sheikh Bello Yabo, ya bayyana irin kyakkyawar alaka ta kusanci da ya yi da marigayi Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi.
A cewar Sheikh Yabo, marigayin yana daya daga cikin fitattun malaman da suka taimake shi matuka a rayuwarsa, tare da ba shi kariya da shawarwari masu amfani.
Bayan miƙa ta’aziyya, Sheikh Yabo ya shawarci daliban Dr. Idris da su ci gaba da yada wa'azinsa da kuma yi masa addu’a koyaushe yayin da yake tuno alakarsu ta shekaru 30.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

