Da Duminsa: Gwamnatin Zamfara Ta Umarci Jama'a Dasu Mallaki Bindigu da Makaman Yakar 'Yan Ta'adda

Da Duminsa: Gwamnatin Zamfara Ta Umarci Jama'a Dasu Mallaki Bindigu da Makaman Yakar 'Yan Ta'adda

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta yi kira ga mazauna jihar da su nemi bindigu da makamai domin kare kansu daga 'yan bindiga
  • Kamar yadda gwamnatin ta bayyana, ta aikewa kwamishinan 'yan sanda bukatar fara bada lasisin rike bindigu ga jama'ar jihar
  • Bayan nan, tace ta shirya samar da makaman bai wa kai kariya ga jama'ar jihar ganin cewa ta'addancin 'yan bindiga ya ki karewa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta yi kira ga mazauna jihar da su dauka makamai tare da bai wa kansu kariya daga 'yan bindiga.

A yayin da korafi kan tabarbarewar tsaro ta yawaita a jihar, hukumomin Zamfara sun umarci kwamishinan 'yan sandan jihar sa ya bada lasisin rike bindigu ga wadanda suka dace su rike a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Labari Da Duminsa
Da Duminsa: Gwamnatin Zamfara Ta Umarci Jama'a Dasu Mallaki Bindigu da Makaman Yakar 'Yan Ta'adda
Asali: Original

Gwamnatin tace a shirye take da ta tabbatar da jama'a sun samu makamai ballantana manoma, domin bai wa kansu kariya.

Kara karanta wannan

Kebbi: Bagudu Butulu ne, Yana Yakar Wadanda Suka Masa Halacci, Shugaban APC

"Bayan karuwar lamurran 'yan ta'adda a sassan jihar da kuma kokarin gwamnati na samar da isasshen tsaro ga rayuka da kadarorin 'yan jihar, ballantana a lokacin damina, gwamnati ta yanke hukuncin daukar matakan shawo kan farmakin da suka yawaita, garkuwa da mutane da kuma harajin dole da 'yan ta'adda ke sanyawa al'ummomi."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Wannan ta'addancin abun damuwa ne ga jama'a da gwamnatin jihar. A don haka, domin shawo kan lamarin a al'ummomin da hakan ta shafa, gwamnati bata da wani zabi da ya wuce ta dauka wadannan matakan:
"Daga yanzu gwamnati ta umarci jama'a da su shirya tare da samun bindigogi domin kare kansu daga 'yan bindiga, yayin da gwamnatin ta umarci kwamishinan 'yan sanda da ya bada lasisi ga duk wadanda ya dace su samu bindigogi domin kare kansu. A shirye gwamnati take wurin samar da makaman da suka dace domin kare kai. Gwamnati ta riga da ta shirya raba fom 500 a kowacce masarauta daga cikin masarautu 19 na jihar ga wadanda ke son mallakar bindigar kare kansu.

Kara karanta wannan

Nasara: Sojojin Najeriya sun damke kasurgumin mai sayar wa Boko Haram kayan aiki

"Dole ne jama'a su nema lasisi daga kwamishinan 'yan sanda domin rike bindiga da sauran makamai da zasu yi amfani da su wurin kare kansu. Za a kafa sakateriya ko cibiya ta karbar bayanan sirri kan al'amuran masu kai wa 'yan bindiga bayanai.
"Ana shawartar jama'a da su tabbatar da bayanan masu kai wa 'yan bindiga bayanan sirri da zasu kawo gaskiya ne tsagwaronta tare da cikakkun bayanan wanda ake zargin da suka hada da hotuna, sunaye cikakku, adireshi, aikin yi da shaida wanda zai tabbatar da ingancin bayanan. Gwamnati za ta matukar daukar mataki kan duk wanda ta kama da kasancewa mai bai wa 'yan bindiga bayanan sirri. Duk wanda ya bada bayanan karya kan wani, zai fuskanci makamancin hukuncin da ake wa masu kai wa 'yan bindigan bayanan sirri.
"Gwamnati ta bukaci majalisar jihar da ta amince da gaggawa kan bukatar ladabtar da masu bai wa 'yan bindiga bayanan sirri domin samun damar daukar mummunan mataki a kansu.

Kara karanta wannan

Dakarun NAF Sun Dakile Yunkurin Satar Shanu, Sun Halaka 'Yan Ta'adda Masu Yawa

"Gwamnati ta umarci diban karin ma'aikata 200 a kowacce daga cikin masarautu 19 na jihar domin gadi, wanda hakan ya mayar da jimillar 500 a kowacce masarauta domin magance 'yan bindiga," Ibrahim Dosara, kwamishinan yada labarai yace a takardar da ya fitar.

Gwamnatin ta kara da kafa kwamiti domin tabbatar da an aiwatar da wadannan matakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel