NNPCL: Naira Biliyan 500 Ta Ɓata kafin Ta Shiga Asusun Najeriya, SERAP Ta Dura Kotu
- Kungiyar SERAP ta nuna damuwa kan yadda Naira biliyan 500 ta ɓata daga NNPCL zuwa asusun gwamnatin tarayya
- SEPAP ta maka kamfanin NNPCL a gaban kotun, inda ta buƙaci ya yi bayanin inda waɗannan kudi suka maƙale a shekarar 20204
- Kuɗin dai suna daga cikin kudin shiga da NNPCL ya tara N1.1trn a 2024, kamfanin ya tura Naira biliyan 600 zuwa baitul mali
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Kungiyar SERAP mai bin diddiga yadda ake kashe kudin gwamnati ta maka kamfanin mai na kasa watau NNPCL a gaban babbar kotun tarayya da ke Legas.
SERAP ta shigar da ƙara ne tana tuhumar Kamfanin NNPCL da ƙin tura kudi kimanin Naira biliyan 500 na kuɗaɗen shiga zuwa asusun gwamnatin Najeriya a 2024.

Source: Twitter
Jaridar Guardian ta ce wannan ƙara na zuwa ne bayan zargin da Bankin Duniya ya yi kwanan nan cewa NNPCL bai saka duka kudin da ya samu a 2024 a asusun Najeriya ba.
Bankin ya ce daga cikin N1.1trn da aka samu daga sayar da danyen mai da sauran hanyoyin samun kuɗi a 2024, NNPCL ya tura Naira biliyan 600 kacal zuwa baitul mali, sauran Naira biliyan 500 kuma sun yi ɓatan dabo.
NNPCL: Abin da SERAP ke nema a kotu
Sai dai a cikin ƙarar da SERAP ta shigar mai lamba FHC/L/MSC/553/2025, kungiyar ta buƙaci kotu na tilasta wa NNPCL ya yi bayanin inda Naira biliyan 500 suka maƙale.
SERAP ta nemi kotu ta umarci NNPCL da ya bayar da cikakken bayani kan inda kudi Naira biliyan 500 suka shiga kuma ta umarci hukumomin yaki da cin hanci su binciki yadda kudin suka ɓata.
Sannan ƙungiyar ta buƙaci kotu ta sa a binciko wadanda ke da alhakin batan kudin, a tuhume su sannan a gurfanar da su gaban ƙuliya domin doka ta yi aikinta.
SERAP ta kafa hujjoji da kundin tsarin mulki
SERAP ta ce:
"Wajibi ne NNPCL ya bi dokar tsarin mulki ta Najeriya ta 1999, dokar bayanai ta FoI, da kuma alkawarin da Najeriya ta ɗauka na kare haƙƙin ɗan adam da yaƙi da cin hanci.
"Rashin tura wannan kuɗi baitul mali ya ta’azzara matsin tattalin arziki da Najeriya ke ciki, ya kuma kara yawan bashin da gwamnati ke ci da kuma karin gibin kasafin kuɗi.

Source: Twitter
Kungiyar ta ce hakan na nuna cewa NNPCL ya gaza gudanar da ayyukansa bisa gaskiya da rikon amana, lamarin da ya tauye hakkokin tattalin arziki na 'yan Najeriya.
SERAP ta kuma tuna da hukunci da kotun koli ta yanke kwanan nan kan dokar FoI, wanda ƙungiyar ta ce dokar ta shafi duk wasu bayanan gwamnati da na hukumomin tarayya, ciki har da na NNPCL.
Lauyoyin da Suka Shigar da ƙarar a madadin ƙungiyar SERAP sun haɗa da, Kolawole Oluwadare, Ms Oluwakemi Oni da Ms Valentina Adegoke inji rahoton Leadership.
An taso Mele Kyari bayan ya bar NNPCL
A wani rahoton, kun ji cewa wata kungiyar 'yan ƙasa masu kishin Najeriya ta bukaci a binciki tsohon shugaban NNPCL, Mele Kyari, kan yadda aka kashe $1.5bn a matatar Fatakwal.
Shugaban kungiyar, Michael Omoba ya ce ce ya zama dole su jawo hankalin shugabanni na cikin gida da na waje kan zargin badaƙalar da aka tafka a NNPCL karkashin Mele Kyari.
Omoba ya ce abin takaici ne yadda aka zuba makudan kudi a matatar da bata aiki maimakon amfani da su wajen inganta kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


