'Ni Kaɗai Zan Yi': Sarki Ya Haramta Layya saboda Tsadar Rayuwa, Zai Yi Wa Ƴan Kasa

'Ni Kaɗai Zan Yi': Sarki Ya Haramta Layya saboda Tsadar Rayuwa, Zai Yi Wa Ƴan Kasa

  • Sarkin Morocco, Mai Martaba Muhammad VI ya bukaci marasa karfi a kasar da su dakatar da yin layya saboda tsadar rayuwa da ake ciki
  • Sarkin ya ce fari da karancin dabbobi sun haddasa tsada, don haka ya kamata marasa hali su jingine layya domin saukaka wa kansu
  • Mai Martaba zai yanka raguna biyu, daya a karan kansa daya kuma na al’umma, yana mai cewa ya yi hakan don bin sunnan Annabi Muhammad (SAW)

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Rabat, Morocco - Sarkin Morocco ya hana al'ummar kasar yanka a babbar sallah saboda tsadar rayuwa da ake ciki a halin yanzu.

Sarki Muhammad VI ya bukaci marasa galihu da su kauracewa yin layya tun da ba wajibi ba ne a cikin addinin Musulunci.

Sarkin Morocco ya hana yin layya
Sarkin Morocco ya haramta layya saboda tsadar rayuwa. Hoto: @M_RoyalFamily.
Source: Twitter

Sarkin Morocco ya fadi dalilin hana layya

Kara karanta wannan

'Zan kare kai na': An hango Sheikh Bello Yabo dauke da bindiga a wajen Wa'azi

Shafin DW Hausa ne ya bayyana rahoton a cikin wani faifan bidiyon YouTube da aka wallafa a yau Talata 3 ga watan Yunin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani mataki na tabbatar da sauki cikin addini, Sarki ya kirayi ‘yan kasar marasa galihu da su hakura da yin layya a bana.

Basaraken ya ce hakan bai rasa nasaba da karancin raguna da kuma tsada sakamakon ‘farı’ da ya addabı kaşar shekaru bakwai a jere.

Sarki Muhammad VI, ya ce duk mai halin yin layya zai iya yi daidai gwargwado ba a hana shi ba.

Sarki ya fadi dalilin hana yan kasarsa yin layya
Sarkin Morocco ya ce zai yi wa kowa yanka a sallar layya. Hoto: The Muslim 500.
Source: UGC

Sarki ya daukewa yan kasa yin layya

Sai dai ya ce zai yanka raguna guda biyu daya na shi, daya kuma na al'ummar kasar baki daya.

Ya ce:

"Kasancewar layya sunna ce mai ƙarfi ga wanda ke da ikon yi, idan muka ce za mu yi da dabbobin da muke da su, za mu yi fama da ƙarancin cimaka a kasuwanninmu.
"Ina kira ga ilahirin yan kasa su jingine yin layya a bana, a matsayina na jagoransu, zan yanka raguna biyu, daya a kaina daya kuma ga al'umma ta.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Yadda wani mahaifi ya dirkawa dansa bindiga har lahira

"Na yi haka ne domin koyi da kakana, Annabi Muhammad (SAW) wanda bayan ya yi yanka ya ce daya na shi ne daya kuma na al'ummarsa."

An taba hana layyah a kasar Morocco

Rahotanni sun ce tun a baya, lokacin Sarki Muhammad V, an taba soke yin layya saboda karancin dabbobi.

Marigayin wanda shi ne mahaifin wannan Sarki na yanzu ya soke yin layya a jere har shekaru uku.

Lamarin ya faru ne bayan kasar Algeria ta hana shigo da dabbobi cikin Morocco a wancan lokaci bayan alaƙa ta yi tsami a tsakaninsu.

Layya a addinin Islama

Layya wata muhimmiyar ibada ce a cikin addinin Musulunci wadda ake gudanarwa a lokacin Babbar Sallah — wato Sallar Idi.

Wannan ibada tana da ma’anar kaskantar da kai ga Allah ta hanyar yanka dabba kamar rago, saniya ko raƙumi a ranakun sallah bayan kammala sallar Idi.

A cewar malamai, layya sunnah ce mai ƙarfi ga wanda ke da iko da hali, kuma tana daga cikin hanyoyin da Musulmai ke nuna biyayya da godiya ga Allah.

Asalin layya yana da tushe ne daga labarin Annabi Ibrahim (AS), wanda Allah ya umurce shi da yanka ɗansa Isma'il (AS) a matsayin jarabawa.

Kara karanta wannan

Aikin hajji: Saudiyya ta hana maniyyata sama da 200,000 sauke farali

Amma kafin ya yanka shi, Allah ya saukar da rago daga sama don ya maye gurbin ɗan nasa. Daga nan ne Musulmai ke bin wannan tarihi a kowace shekara a lokacin Idi ta layya.

Layya tana da girma a zuciyar Musulmai, domin tana ɗauke da darussa da dama — kamar nuna tausayi, ciyar da mabukata, da kuma tabbatar da haɗin kai da soyayya tsakanin mambobin al’umma.

A kasashe da dama, layya na ɗaya daga cikin manyan bukukuwa da ke tara Musulmai wuri guda don sallah, hadin kai, da rabon nama ga mabukata.

Farashin ragunan layya ya tashi a Najeriya

Mun ba ku labarin cewa yan kasuwa masu sayar da raguna sun koka da rashin kasuwa yayin da ake shirin gudanar da bukukuwan babbar sallah a Najeriya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa farashin raguna ya karu da fiye da kashi 85 a birnin Abuja wanda ake zargin rashin tsaro ya ba da gudunmawa sosai.

Wasu masu siye sun ce rashin kudi da halin tattalin arziki ya hana su siyan raguna, inda wasu suka ce za su nemi wata hanyar domin samun sauƙi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.