Ana Murnar an Samu Sauƙi, Jami'ar North West Ta Ƙara Kuɗin Makaranta a Kano
- Jami’ar North West ta sanar da ƙara kuɗin makaranta daga ₦19,700 zuwa ₦57,300 ga ɗalibai ‘yan asalin jihar Kano
- Lamarin ya daga hankalin dalibai, musamman ganin wasu sun kammala shirin fara biyan kudin karatun sabon zango
- Kungiyar dalibai ta NAKSS ta shaidawa Legit Hausa cewa tana tattaunawa da jami’ar da gwamnati domin rage kuɗin makarantar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Daliban jami'ar North West da ke Kano sun bayyana takaici bayan hukumar gudanarwar jami'ar ta yi karin kudin makaranta da kusan 300%.
Wasu daga cikin daliban sun bayyana cewa sun kammala shirin fara biyan kudin makarantarsu, sai kwatsam suka ji kari mai nauyin gaske.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta wallafa cewa jami’ar ta ƙara kuɗin makaranta ga ɗalibai ‘yan asalin jihar daga ₦19,700 da suka saba biya zuwa ₦57,300 a yammacin Lahadi 1 ga watan Yunin 2025.

Kara karanta wannan
Sojoji sun ƙara samun matsala, jirgin yaƙi ya yi kuskuren sakin wuta a jihar Zamfara
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar daliban Kano ta magantu
A hirarsa da Legit Hausa yammacin Litinin, shugaban kungiyar daliban jihar Kano (NAKSS), Isyaku Ali Kanwa, ya ce sun karbi korafin daliban jami'ar.
Ya ce:
“Mun fara karɓar koke-koke daga kowane lungu da saƙo tun daren Lahadi, inda ɗalibai ke roƙon mu shiga tsakani a duba lamarin."
Ali Kanwa ya ce sun tuntubi gwamnatin jihar Kano kuma an shaida musu cewa ba ta da hannu cikin ƙarin kuɗin.

Source: Facebook
Haka kuma, ya bayyana cewa ƙungiyar NAKSS na tattaunawa da shugabannin jami’ar North West don ganin an rage kudin zuwa yadda dalibai da iyayensu za su iya biya a cikin sauki.
Ya ce suna fatan za a samo mafita cikin gaggawa domin ɗalibai su samu damar ci gaba da karatu ba tare da matsin lamba ba.
NANS ta soki karin kudin daliban jami'ar Kano
A wata sanarwa da shugaban kungiyar daliban ta kasa (NANS) reshen Kano, Kwamred Abdulganiyu Shehu Dalhatu ya fitar, ƙungiyar ta bayyana takaicinta.
Haka kuma ta bayyana mamaki da ɓacin rai game da sabon kuɗin makarantar da ya haura 300% idan aka kwatanta da na baya.
Kwamred AbdulGaniyyu na ganin karin a yanzu bai dace ba, musamman idan aka duba halin ƙuncin da iyalai da dama ke ciki a Najeriya.
Sanarwar ta ce:
"Wannan kara kudin karatu da aka yi ba wai kawai rashin tausayi ba ne, har ma ya ci karo da hakkokin ɗalibai na samun ilimi a cikin sauki.”
NANS ta ce, idan har wannan ƙarin ya dore, to ɗalibai da dama ba za su iya ci gaba da karatu ba, kuma hakan zai lalata ƙoƙarin da Gwamnatin Jihar Kano ke yi wajen bunƙasa ilimi.
Gwamnan Kano zai biyawa dalibai kudin jarrabawa
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin jihar Kano, karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta amince da biyan kudin rajistar jarrabawa ga dalibai a makarantu 3,526.
Gwamna Abba ya yanke shawarar daukar nauyin rajistar jarrabawar ne bayan daliban sun ci jarrabawar cancanta inda ya yi umarnin a fara yi masu rajista.
Hakan zai ba daliban damar rubuta jarrabawar kammala Sakandare ta NECO da ta Hukumar Nazarin Harshe da Ilimin Addinin Musulunci (NBAIS) ba tare da biyan ko kwabo ba.
Asali: Legit.ng
