Sojoji Sun Ƙara Samun Matsala, Jirgin Yaƙi Ya Yi Kuskuren Sakin Wuta a Jihar Zamfara
- Jirgin yakin rundunar sojin Najeriya ya sake kuskuren kashe ƴan sa-kai a yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara
- Rahotanni daga yankin sun ce ƴan sa-kai sun yi koƙarin bin sawun ƴan bindiga ne bayan sun kawo hari, kwatsam jirgin ya sojoji ya kawo ɗauki
- A cewar rundunar sojoji, jirgin ya hallaka ƴan bindiga 20 amma an samu kuskuren kashe ƴan sa-kai biyar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara - A kalla ’yan sa-kai 20 ake zargin sojoji sun kashe bisa kuskure a wani hari da jirgin yakin sojin Najeriya ya kai a jihar Zamfara.
Wannan mummunan lamari ya faru ne a kauyen Garin Mani, karamar hukumar Maru, bayan harin da ƴan bindiga suka kai wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Source: Original
Yadda ƴan bindiga suka fara kai hari
A cewar ganau, wasu mahara dauke da bindigu sun dira kauyen a kan babura da rana tsaka, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wani, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin da ya jefa jama’a cikin firgici kuma ƴan bindigar sun yi nasarar awon gaba da mutane sama da 50, mafi yawansu manoma da ke aiki gonakinsu.
A kokarinsu na kare al’umma, wasu daga cikin ’yan sa-kai suka bi sawun ’yan bindigar domin ceto mutanen da aka sace.
Jirgin sojoji ya kashe ƴan sa-kai a Zamfara
Amma abin takaici, wani jirgin yaki da aka tura wajen domin kai ɗauki ya yi kuskuren sakin luguden wuta kan jami'an rundunar ƴan sa-kai.
Wani daga cikin waɗanda suka tsira ya shaidawa BBC Hausa cewa:
“Muna bin ’yan bindigar ne sai muka ga jirgi ya doso. Ya gangaro kasa sosai sai ya fara harbin mu. Wasu daga cikinmu sun kwanta kasa kamar an harbe su domin tsira da rayuwa. Bayan jirgin ya tashi, sai muka gudu muka tsira.”
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai bayyana bakin cikinsa game da yadda ba a samu bayani daga bangaren sojoji ba.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna a Zamfara, an samu asarar rayuka
“Mun fahimci kuskure ne, amma sojoji su fito fili su amince da abin da ya faru, su kuma tuntubi iyalan wadanda lamarin ya shafa,” inji shi.
Sojoji sun musanta kashe ƴan sa-kai 20
A bangaren sojoji, an tabbatar da cewa fiye da ’yan bindiga 20 ne aka kashe a harin da jirgin ya kai a kauyukan Maraya da Wabi a Maru, a ranar Asabar 31 ga Mayu.
Rahotan da Zagazola Makama ya wallafa a shafin X, ya nuna cewa bayan kashe ƴan bindigar, jirgin sojojin ya taɓa ƴan sa-kai bisa kuskure.

Source: Facebook
Wata majiya daga rundunar soji ta bayyana cewa:
“An tabbatar da mutuwar fiye da ’yan bindiga 20 da lalata babura da kayan aikin su. Amma abin bakin ciki, an kashe ’yan sa-kai biyar, yayin da wasu da dama suka samu raunuka."
Rahoton ya kara da cewa shugabannin ’yan sa-kai sun dauki alhakin abin da ya faru, inda suka ce sun sabawa umarnin da aka ba su na janyewa daga bakin gari kafin a kai harin sama.
An kashe jami'an CJTF a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa ƴan bindiga sun yi kwantan ɓauna, sun farmaki dakarun rundunar ƴan banga watau CJTF a jihar Zamfara.
An ruwaito cewa maharan sun hallaka ƴan dakarun CJTF biyu da wani jami'an rundunar asakarawan jihar Zamfara guda ɗaya.
Majiyoyi sun bayyana cewa an kawo jami’an CJTF daga Maiduguri ne domin taimakawa wajen daƙile hare-haren da ke ci gaba da faruwa a ƙaramar hukumar Kaura Namoda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

