NiMet Ta Lissafa Kano da Jihohin Arewa 7 da Za a Iya Samun Ambaliya a Watan Yuni

NiMet Ta Lissafa Kano da Jihohin Arewa 7 da Za a Iya Samun Ambaliya a Watan Yuni

  • Hukumar NiMet ta yi gargaɗin yiwuwar ambaliya a wasu jihohi a Yuni 2025, yayin da kasar ke shiga tsakiyar damina da ruwan sama mai tsanani
  • Jihohin da aka fi fargabar ambaliya sun haɗa da Kano, Kaduna, Neja, Nasarawa, Kwara, Sokoto, Filato da FCT, inda ruwa zai sauka da karfi
  • NiMet ta bukaci manoma su yi shiri, a dakile ambaliya ta hanyar share magudanan ruwa da bin sabbin hanyoyin noma masu dacewa da yanayi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargadin cewa za a iya samun ambaliya a wasu jihohi yayin da kasar ke shiga tsakiyar damina.

NiMet ta yi hasashen saukar ruwan sama mai karfi da yiwuwar ambaliya a jihohi da dama a cikin watan Yuni, 2025, musamman a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Duk mun koma mayunwata': Tsohon minista ya fadi abin da ke jiran Tinubu a 2027

NiMet ta yi hasashen cewa Kano, Kaduna da wasu jihohin Arewa 6 za su iya samun ambaliya a Yuni
Wasu gidaje da suka nutse a cikin ruwa bayan barkewar ambaliya a Maiduguri a 2024. Hoto: Audu Marte
Source: Getty Images

NiMet ta yi hasashen ambaliya a Yuni

A cewar hasashen wata-wata na NiMet ta wallafa a shafinta na X, ana sa ran Inter-Tropical Discontinuity (ITD), wanda ke auna damina da saukar ruwa, zai matsa zuwa Arewa cikin watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsawar ITD zuwa Arewa zai kawo karin ruwan sama a Arewacin Najeriya, yayin da yankin Kudu da Tsakiyar kasar zai fuskanci ruwan sama da hadari akai-akai.

NiMet ta ce akwai yiwuwar saukar ruwan sama ƙasa da kima da kashi 40 zuwa 50 a jihohin Kwara, Kogi, Neja, Nasarawa, Benuwai, Taraba da Adamawa.

Sauran jihohin da abin zai shafa za su haɗa da Kaduna, Kano, Katsina, Sokoto, Edo, Delta da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT), inda ake fargabar afkuwar ambaliya da fari.

Jihohi 8 da za su iya samun ambaliya

Hukumar ta jaddada yiwuwar afkuwar ambaliya ta ba-zata a jihohi takwas:

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi da wasu fitattun malamai 16 da Saudiyya ta taba hana su aikin Hajji

  1. Filato
  2. Kano
  3. Kaduna
  4. Neja
  5. Nasarawa
  6. Kwara
  7. Sokoto
  8. Da kuma FCT.

NiMet ta bukaci manoma su rungumi sababbin hanyoyin noman zamani da kula da yanayi domin rage illar sauyin yanayi da damina mai rikitarwa.

Haka kuma, hukumar ta bukaci masu kula da madatsan ruwa da su kara lura da matakin ruwa a madatsun su domin gujewa iftila’in ballewar ruwan.

NiMet ta bukaci hukumomin jihohi da kananan hukumomi su share magudanan ruwa da kwata domin dakile ambaliya a birane da gundumomi.

Sama da mutane 500 ake zargin ambaliyar ruwa ta halaka a Mokwa, jihar Neja
Wani yanki da ambaliyar ruwa ta shafe shi. Hoto: Audu Marte
Source: Getty Images

Sama da mutum 500 sun mutu a ambaliyar Neja

Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan ambaliya mai tsanani a Mokwa, jihar Neja, a ranar 28 ga Mayu, 2025, inda ruwan sama ya mamaye unguwanni gaba ɗaya.

Rahoton BBC Hausa ya nuna cewa fiye da mutane 500 sun mutu, fiye da 1,500 sun rasa matsugunninsu, kana sama da 500 sun bata a sakamakon ambaliyar a Mokwa.

Ruwan ya shanye gidaje da motoci a cikin karamin lokaci, inda hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja ta ce yankunan Tiffin Maza da Anguwan Hausawa sun fi shan wahala.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Sheikh Pantami ya yi magana kan mutuwar mutane sama da 100 a Jihar Neja

Yayin da aka shiga watan Yuni, NiMet ta ci gaba da fitar da rahotanni kan hasashen yanayi, tana mai jan hankalin 'yan Najeriya da su bi matakan kariya da kuma shiryawa daminar bana.

Buhari ya girgiza da ambaliyar Neja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna alhini kan mutuwar sama da mutane 200 sakamakon ambaliyar da ta afku a jihar Neja.

Har ila yau, Buhari ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalan ‘yan wasa da masu horar da su 22 da suka mutu a wani mummunan haɗarin mota a Kano.

Ya ce aukuwar wadannan bala’o’i a lokaci guda abu ne mai matuƙar tada hankali, yana fatan wadanda suka jikkata za su samu sauƙi cikin gaggawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com