Aikin Hajji: Saudiyya Ta Hana Maniyyata sama da 200,000 Sauke Farali
- Saudiyya ta hana mutum 269,000 shiga Makka ba tare da izini ba, yayin da suke kokarin shiga kasar don sauke farali a wannan shekara
- Hukumomin kasar sun ce wannan wani mataki ne na dakile yawan maniyyatan da ke kokarin aikin hajji ba bisa ka’ida ba
- Laftanar Janar Mohammed al-Omari ya bayyana cewa sai wanda ke da shaidar aiki hajji za a bari ya sauke farali ko a kasar yake zaune
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Saudi Arabia – Hukumomin Saudiyya sun dakatar da mutane sama da 269,000 daga shiga birnin Makka domin aikin hajji.
Hukumomi sun bayyana cewa wadanda aka dakatar sun yi yunkurin shiga kasar ba tare da izinin shiga ba, kuma wannan wani mataki na dakile shigar da maniyyata kasa ba bisa doka ba.

Source: Facebook
Jaridar Al Arabiya English ta ruwaito cewa gwamnatin Saudiyya ta dora laifin cunkoson da ke faruwa a Hajji kan masu shiga Makka ba tare da izini ba.
Ta kara da cewa a bara, wadanda suka shiga kasar ba bisa ka'ida ba su ne suka fi yawa cikin wadanda suka rasu a zafin rana da ta afku.
Hajji: An hana maniyyata shiga Makka
21st Century Chronicle ta ce wannan adadi ya nuna yadda aka samu yawaitar kokarin shiga hajji ba bisa izini ba duk da tsauraran matakan da Saudiyya ke dauka na hana hakan.
A halin yanzu, akwai mutum miliyan 1.4 da suka samu izini mahukuntan Makka, kuma ana sa ran karin wasu za su isa birnin a cikin ‘yan kwanakin nan.
Doka ta tanadi hukunci har zuwa tarar $5,000 da kuma fitar da mutum daga kasar ga duk wanda aka kama yana yunkurin aikin hajji ba tare da izini ba – ko dan kasa ne ko mai zama a Saudiyya.
Hukumomi sun kwace lasisin kamfanonin hajji 400
A wani taron manema labarai da aka gudanar a Makka, jami’an tsaro sun bayyana cewa sai wanda ke da takardar izini kadai ne zai iya gudanar da aikin hajji.
Baya ga haka, an hukunta sama da 23,000 daga cikin mazauna Saudiyya da suka karya dokokin hajji, tare da kwace lasisin kamfanonin Hajji 400 da aka samu da aikata sabawa ka’idoji.

Source: Twitter
Laftanar Janar Mohammed al-Omari ya shaida wa manema labarai cewa:
“Alhazai na karkashin kulawarmu, kuma duk wanda ya saba doka na hannunmu.”
Hukumar kare lafiyar jama’a ta Saudiyya ta ce an fara amfani da jiragen sama marasa matuki a wannan hajjin domin sa ido da kuma kashe gobara idan ta tashi.
Sheikh Saleh zai yi hudubar Arfa a Hajji
A baya, kun ji cewa masarautar Saudiyya ta sanar da cewa an naɗa Sheikh Saleh bin Abdullah Al Humaid a matsayin limamin da zai jagoranci hudubar Arafa ta ga mahajjatan bana.
Wannan naɗi ya zo ne a daidai lokacin da alhazai daga sassa daban-daban na duniya ke shirin taruwa a filin Arafat domin sauraron hudubar ranar 9 ga Zul-Hijjah mai muhimmancin gaske.
An haifi Sheikh Saleh bin Abdullah Al Humaid a shekara ta 1950 a garin Buraidah da ke lardin Qassim, a Saudiyya, ya haddace Alƙur’ani mai tsarki tun yana da ƙarancin shekaru.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


