Bikin Babbar Sallah: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Hutun Kwanaki 2
- Gwamnatin tarayya ta ayyana Juma’a, 6 da Litinin, 9 ga Yuni, 2025 a matsayin hutun domin bai wa Musulmai damar yin bikin sallah
- Minista Olubunmi Tunji-Ojo ya bukaci Musulmai da su rungumi darasin layya da biyayya kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) ya koyar
- Gwamnati ta tabbatar da cewa tana kokarin farfado da tattalin arziki karkashin tsarin Shugaba Bola Tinubu domin dawo da martabar kasa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta ayyana Juma’a, 6 ga Yuni da Litinin, 9 ga Yuni, 2025 a matsayin ranakun hutu domin bikin babbar sallah na bana.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya a wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin.

Source: Facebook
Jaridar Channels TV ta ruwaito cewa babban sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ce ta sanya hannu a kan sanarwar ranar hutun.
Sallah: Gwamnati ta nusar da musulmi
FRCN HQ ta wallafa cewa Tunji-Ojo ya taya dukkan al’ummar Musulmi, a gida da kasashen waje, murnar zagayowar wannan babbar rana ta Sallah.
Ya bukaci Musulmai da su ci gaba da rungumar darasin hadaya da biyayya kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) ya nuna, yana mai jaddada muhimmancin addu’a da sadaukarwa a irin wannan lokaci mai albarka.

Source: Facebook
Ministan ya kuma bukaci al'ummar Musulmi da sauran ‘yan kasa da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’a domin zaman lafiya da ci gaban Najeriya.
Gwamnati ta taya al’umma murnar Sallah
Tunji-Ojo ya tabbatar wa ‘yan kasa cewa gwamnatin tarayya tana kan kokarin farfado da tattalin arzikin kasa, tare da aiwatar da sauye-sauyen da ke da amfani kai tsaye ga al’umma.
“Sauye-sauyen da ake aiwatarwa a karkashin tsarin Shugaba Bola Tinubu na da nufin dawo da martabar Najeriya a matsayin kasa mai ci gaba da daraja."
Ya kara da cewa sannu a hankali za a samu nasarar da aka saka a gaba na tabbatar da cewa Najeriya ta samu bunkasar tattalin arziki da walwala.
Daga bisani, ya taya Musulmai murnar bikin Eid-ul-Adha, yana kuma kira da a hada kai da gwamnati domin dawo da darajar Najeriya a idon duniya.
Gwamnatin Kano ta ba da hutun makoki
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Jihar Kano ya ayyana Litinin, 2 ga Yuni, 2025, a matsayin ranar hutu ta musamman domin nuna alhini da jajantawa ga iyalan matasa 22 da suka rasu.
Hatsarin ya auku ne yayin da matasan ke dawowa daga gasar wasannin ƙasa da aka kammala a jihar Ogun, inda suka wakilci Kano tare da samun nasara a wasanni da dama da aka gudanar.
Sanarwar ta kara da cewa waɗanda hatsarin ya rutsa da su sun haɗa da ‘yan wasa, masu horar da su da kuma jami’an gwamnati, da suka wakilci jihar a gasar wasanni ta ƙasa da aka kammala.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

