Jam'iyyar NNPP Ta Fadi Abin da Ya Jawo Asarar Rayukan 'Yan Wasan Kano 22
- NNPP ta dora alhakin hatsarin da ya kashe 'yan wasa 22 daga Kano kan lalatattun hanyoyi, tana kira da a gaggauta daukar mataki wajen gyara su
- Olufemi Ajadi Oguntoyinbo ya bayyana hatsarin a matsayin abin tausayi, yana mai cewa ‘yan wasan matasa ne masu cike da fatan dawowa ga iyalansu
- Ajadi ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan da kuma Gwamnan Kano, yana rokon Allah SWT ya ba su hakuri da jure wannan babban rashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jam’iyyar NNPP ta dora laifin hatsarin motar da ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan wasa 20 daga Kano kan rashin ingantaccen hanyoyi a jihar.
‘Yan wasan sun dawo daga gasar wasanni da aka gudanar a Jihar Ogun, inda hatsarin ya auku yayin da motarsu ta fadi daga gadar Dakatsalle a karamar hukumar Kura, Jihar Kano.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, a wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, wani jigo na jam’iyyar daga Kudu maso Yamma, Olufemi Ajadi Oguntoyinbo, yayi takaicin afkuwar hadarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPP ta yi takaicin rasuwar ‘yan wasan Kano
Daily Post ta ruwaito cewa Oguntoyinbo ya jaddada bukatar gaggauta gyaran hanyoyi domin kaucewa faruwar irin wannan mummunan lamari a nan gaba.
Ajadi ya ce:
“Abin takaici ne kwarai da gaske cewa ‘yan wasa 20 da suka wakilci Kano a gasar Gateway 2024 sun rasa rayukansu a irin wannan mummunan lamari da za a iya kaucewa.”
Ya nuna damuwa da lokaci da lamarin ya auku, kwanaki kalilan kafin bikin Sallah, inda ya ce matasan na cike da farin cikin dawowa gida ga 'yan uwansu.
NNPP ta yi ta’aziyya ga iyalan ‘yan wasan Kano
Ajadi ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan da abin ya shafa, yana cewa wannan rashi na taba zukatan iyaye da al’umma kasar nan.
Haka kuma, ya jajanta wa Gwamna Abba Kabir Yusuf da al’ummar Jihar Kano, yana rokon Allah ya ba su karfin hali wajen jure wannan babban rashi.

Source: Facebook
A cewarsa:
“Wadannan matasa fitattun hazikai ne da za su iya kawo gagarumar ci gaba ga jiharsu da kasa baki daya ta hanyar basira da kwarewarsu.”
“Abin tausayi ne ganin cewa iyalansu da suka dade suna jiran dawowarsu, ba za su kara ganinsu ba har abada. Ina mika addu’a da ta’aziyya ga danginsu a wannan lokaci mai cike da radadi.”
Ajadi ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da tarayya da su dauki matakin gaggawa wajen inganta hanyoyin mota a fadin kasar, domin kare rayukan al’umma.
Gwamnatin Kano ta tallafawa iyalan 'yan wasan Kano
A wani labarin, mun wallafa cewa gwamnatin jihar Kano ta bai wa kowanne daga cikin iyalan matasan ‘yan wasa 22 da suka rasa rayukansu a hatsarin mota tallafin kudi har ₦1,000,000.
'Yan wasan sun rasu ne a wani mummunan hatsarin mota yayin dawowa daga gasar wasannin kasa da aka gudanar a Abeokuta, jihar Ogun, inda suka wakilci Kano tare da samun nasarori.
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar, 31 ga watan Mayun 2025, yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya zuwa asibitin Nasarawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

