'Gwamnatinka Ta Jefa Talakawa a Masifa,' 'Kungiyar Yarbawa, Afenifere Ta Soki Tinubu

'Gwamnatinka Ta Jefa Talakawa a Masifa,' 'Kungiyar Yarbawa, Afenifere Ta Soki Tinubu

  • Kungiyar ci gaban Yarbawa ta Afenifere ta dira kan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu yayin da ta cika shekaru biyu a mulki
  • Sanarwar da shugaban kungiyar, Oba Oladipo Olaitan, ya sanya wa hannu ta ce Shugaba Tinubu ya lalata komai a kasar nan
  • Kungiyar ta ce gwamnati ta gaza rage yawan kashe kudi da almubazzaranci, yayin da take wa talakawa wa’azi su kara hakuri

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja Kungiyar ci gaban Yarbawa ta Afenifere ta bayyana cewa shirin ci gaba da shugaban kasa Bola Tinubu ya kawo ga ‘yan Najeriya ya rikide zuwa kunci da wahala.

A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Oba Oladipo Olaitan, da sakataren yada labarai na kasa, Justice Faloye, suka fitar a ranar Lahadi, an zargi gwamnatin Tinubu da gazawa.

Kara karanta wannan

2027: Atiku da manyan 'yan siyasa 7 da suka dauki aniyar raba Tinubu da ofis

Tinubu
Kungiyar Yarbawa ta yi kaca kaca da gwanatin Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kungiyar ta ce rahoton rabin wa’adin gwamnatin Tinubu ya nuna cewa dukkanin alkaluman ci gaban bil’adama da siyasa sun koma baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Afenifere: 'Gwamnatin Tinubu ta lalata kowanne fanni'

Punch ta ruwaito Afenifere ta ce, gwamnatin Tinubu ta fi mayar da hankali kan yada bayanan karya da ke yunkurin nuna nasarorin da babu su a kasa, ganin yadda ayyukanta suka tabarbara Najeriya.

Sanarwar ta ce:

“Rahoton rabin wa’adin mulki ya nuna cewa dukkanin fannoni na ci gaban bil’adama da siyasa sun tabarbare tun bayan hawan shugaban kasa Bola Tinubu kan mulki. Alkawarin Najeriya yajefa jama'a cikin tsanani.
“A maimakon ta dauki alhakin wahalhalun da 'yan Najeriya ke fama da su sakamakon manufofinta marasa amfani da almubazzaranci, gwamnatin Tinubu ta rungumi yada karya."

Kungiyar Afenifere ta ce Bola Tinubu ya gaza

Kungiyar Afenifere ta kara da bayyana takaici kan yadda gwamnatin Tinubu ta gaza aiwatar da rahoton Oronsaye cikin shekaru biyu da suka gabata domin rage yawan kudin gudanar da gwamnati.

Kara karanta wannan

Shekara 2 a mulki: Fadar shugaban kasa ta kausasa harshe ga Atiku kan sukar Tinubu

Ta ce maimakon haka, ana ci gaba da kashe kudi da yawa yayin da ake wa talakawa wa’azi game da halin da kasar ta shiga da bukatar yin hakuri da matsi kafin a farfado.

Tinubu
Kungiyar Yarbawa ta zargi gwamnatin Tinubu da jawo koma baya a Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Kungiyar ta kuma zargi gwamnatin da kin mika ikon kafa ‘yan sanda ga jihohi, duk da matsalolin tsaro da ke kara ta’azzara.

Sanarwar ta ce:

“A cikin shekaru biyu da suka gabata, an ga yadda gwamnatin ta kasa jurewa masu sukar ayyukanta. Masu zanga-zanga cikin lumana, dalibai da kungiyoyin kwadago na fuskantar barazana iri iri.
“A ‘yan kwanakin nan ma, an ga yadda ‘yan adawa ke sauya sheka zuwa jam’iyyar mai mulki domin kaucewa gallazawa daga hukumomi.”

'Babu cigaba a gwamnatin Tinubu,' Buba

A wani labarin, kun ji cewa jigo a jam’iyyar NNP, Injiniya Buba Galadima, ya bayyana rashin gamsuwarsa da yadda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da al’amuran kasa.

Buba Galadima ya ce babu kamshin gaskiya a ikirarin da shugaban kasa ya yi na kawo ci gaban Najeriya yayin da gwamnatinsa ta cika shekara biyu tana mulki.

Ya bayyana cewa darajar Naira a kasuwa ita ce mafi muni tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999, inda ya ce a yanzu Dala ɗaya ta kai akalla N1650.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng