Wata Sabuwa: Gwamnatin Tinubu na Takaicin Yadda 'Yan Kasa Ba Sa Shan Madara

Wata Sabuwa: Gwamnatin Tinubu na Takaicin Yadda 'Yan Kasa Ba Sa Shan Madara

  • Gwamnatin Najeriya ta damu matuka kan yadda ‘yan Najeriya bas a samun wadataccen madara a duk shekara kamar yadda ya kamata
  • Minista y ace, akalla ya kamata kowanne dan Najeriya ya sha akalla lita 10 na madara a shekara, amma hakan bay a samuwa a Najeriya
  • An kuma bayyana kididdigar kasashen da ake samun madara a duniya, Najeriya za ta iya kwaikwayon tsarin kiwonsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja, Najeriya - Gwamnatin Tarayya ta bayyana damuwa kan yadda ake shan madara ƙasa da kima a Najeriya, lamarin da take ganin yana da illa ga tattalin arziki da lafiyar al’ummar kasar.

Ministan Raya Harkar Kiwo, Idi Mukhtar Maiha, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin bikin Ranar Madara ta Duniya ta shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Abuja.

Ranar Madara ta Duniya dai an kafa ta ne a 2001 ta hannun Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO).

Tinubu ya damu da karancin shan madara a Najeriya
Yadda gwamnati ta damu 'yan Najeriya ba sa shan madara | Hoto: GettyImages
Source: Getty Images

Dalilin kafa ranar madara ta duniya

Kara karanta wannan

Hajjin bana: Za a fassara hudubar Arfah zuwa Hausa, Fulatanci da sauran harsuna 32

An kafa ta ne domin nuna muhimmancin madara a matsayin abinci na duniya da kuma irin rawar da madara ke takawa a ci gaban tattalin arziki da lafiyar duniya baki ɗaya. Ana gudanar da bikin ne kowace shekara a ranar 1 ga Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Maiha ya bayyana cewa, Najeriya na buƙatar kusan tan miliyan 1.7 na madara a kowace shekara, amma ƙasar na iya samar da kusan tan 600,000 ne kacal, wanda ke ɗaukar 35% cikin ɗari na buƙatar cikin gida.

A cewar ministan:

“Ragowar 65% cikin ɗari — wanda darajarsa ta haura dala biliyan 1.5 — ana shigowa da shi ne daga ƙasashen waje, mafi yawanci a matsayin madaran gari.
"Wannan dogaro da madarar waje yana raunana tattalin arzikimu, yana rage darajar kuɗin ƙasarmu, kuma yana hana bunƙasar masana’antun cikin gida.”

Adadin madara lita nawa ya kamata a sha?

Ya ƙara da cewa ƙarancin shan madara a tsakanin ’yan Najeriya abin damuwa ne, yana mai nuni da cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayar da shawarar cewa kowane mutum na bukatar aƙalla lita 10 na madara a shekara.

Sai dai, kididdiga ta nuna cewa, matsakaicin shan madara a Najeriya ya tsaya ne a lita 8.7 — ƙasa da matsakaicin lita 40 da ake samu a nahiyar Afirka, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 36 sun nuna damuwa bayan ambaliya ta ruguza gidaje da mutane a Neja

Dangane da haka, Ministan ya bayyana cewa nau’in shanunmu na gida da makiyaya ke kiwo, na bayar da lita 1 zuwa 2 ne a rana, sabanin wasu nau’ukan shanu na waje kamar Friesians da Jerseys da ke iya bayar da fiye da lita 20-30 a rana idan aka kula da su yadda ya kamata.

Adadin madara a India da wasu kasashen

Daga cikin kasashen, ministan ya yi tsokaci kan yadda India da kasar Afrika ta Kudu ke samar da madara fiye da Najeriya.

Ya ce:

“India, wadda ita ce ƙasar da ta fi kowacce samar da madara a duniya, na samar da fiye da tan miliyan 200 a shekara, mafi yawancinsu daga ƙanana da matsakaitan manoma ne, ta hanyar saka hannun jari a kiwon lafiya da sarrafa jinsin dabbobi.
“Har ila yau, a nahiyarmu, Afirka ta Kudu na sarrafa fiye da lita biliyan 3 na madara a kowace shekara. Waɗannan ƙasashe ne da Najeriya za ta iya kwaikwaya muddin akwai jajircewa da tsari.”

Ministan ya ƙara da cewa, domin inganta wannan fanni, Najeriya na buƙatar mai da hankali wajen bunƙasa kiwon dabbobi, inganta jinsin shanu, da kuma samar da kayan more rayuwa ga makiyaya da manoman madara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng