Gwamnatin Nigeria za ta haramta shigo da madara daga 2022 - Ministan noma

Gwamnatin Nigeria za ta haramta shigo da madara daga 2022 - Ministan noma

- Sabo Nanono,ministan noma ya jadadda aniyar gwamnatin tarayya na haramta shigo da madara cikin kasar

- Nanono ya ce daga shekarar 2022 ko shakka babu za a daina shigo da madara domin ma’aikatarsa na shirye-shiryen samar da hanyoyin sarrafa ta a cikin gida

- Zuwa yanzu ya kuma ce Najeriya ce kan gaba a wajen samar da shinkafa da rogo a duniya

Ministan noma da raya karkara, Sabo Nanono, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta haramta shigo da madara cikin kasar daga shekarar 2022.

Nanono ya bayyana hakan ne a yayinda yake zantawa da manema labarai a Abuja, a wani taro kan ranar abinci ta duniya na 2020.

Ya yi bayanin cewa ma’aikatar na shirye-shirye domin tabbatar da samar da kayayyaki don samar da madara, jaridar The Cable ta ruwaito.

Gwamnatin Nigeria za ta haramta shigo da madara daga 2022 - Ministan noma
Gwamnatin Nigeria za ta haramta shigo da madara daga 2022 - Ministan noma Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

“Muna shirye-shirye a wannan ma’aikata kuma ku zuba ido ku ga abunda na fadi, a shekaru biyu masu zuwa za mu haramta shigo da madara cikin kasar nan. Kuma ku tambaye ni dalili: Muna da shanaye miliyan 25 a kasar nan da za su samar da madara lita miliyan biyar a kullun,” in ji shi.

KU KARATA KUMA: Da ɗuminsa: APC ta kori ƴar majalisar ta mace tilo saboda zargin cin amana

“Matsalar a yanzu shine kayayyakin amfani, wanda mun fara shirye-shiryen dasa hanyar sarrafa madara a fadin kasar. Ban ga dalilin da zai sa mu shigo da madara a shekaru biyu masu zuwa ba. Ya kamata mu daina shigo da madara.”

Nanono ya kuma ce a yanzu Najeriya ce ke samar da shinkafa da rogo mafi girma a duniya.

Ya ce: “Najeriya ta habbaka shirin samar da shinkafa domin karfafa harkar noman shinkafa a cikin gida sannan ta tsare hanyar shigo da yar waje.”

KU KARANTA KUMA: Ta’addanci: Yan gudun hijira na iya komawa Baga domin akwai tsaro yanzu, gwamnatin Borno

Ministan ya ci gaba da bayyana cewa farashin kayayyaki da ya hau a yanzu saboda annobar COVID-19 zai sauko a yan watanni masu zuwa.

A gefe guda, gwamnatin tarayya zata kirkiri ayyuka miliyan 10 a fannin noma da kiwo ta shirin noma don abinci da samun ayyuka (AFJP).

Ministan noma, Muhammad Nanono ya fadi hakan a ranar Talata a Abuja lokacin da ake wata tattaunawa da shi akan shirye-shiryen murnar ranar Abinci ta duniya dake gabatowa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel