Na tura 'ya'yan Fulani 74 Turkiyya koyo ilimin sarrafa madara – Ganduje

Na tura 'ya'yan Fulani 74 Turkiyya koyo ilimin sarrafa madara – Ganduje

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya sanar da cewa a baya gwamnatinsa ta dau nauyin a kalla yaran Fulani makiyaya 74 zuwa kasar Turkiyya don koyo yadda ake tatso madara na zamani.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Asabar yayin kaddamar da rukunin gidaje 200 na Ruga sa za a gina wa Fulani a kauyen Dansoshiya da ke karamar hukumar Kiru ta jihar.

Ya kara da cewa, gwamnatinsa ta samar da tafkin dan Adam mai cin ruwa lita miliyan hudu don amfanin Shanun Fulanin wanda hakan zai sa rashin bukatar yawon neman ruwansu.

Kamar yadda yace, ana gayyatar Fulani makiyaya daga dukkan sassan kasar nan sa su garzaya jihar Kano son mora daga romon gwamnatinsa.

Na tura 'ya'yan Fulani 74 Turkiyya koyo ilimin sarrafa madara – Ganduje
Na tura 'ya'yan Fulani 74 Turkiyya koyo ilimin sarrafa madara – Ganduje. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Ya kara da cewa, rukunin gidaje na da dukkan kayayyakin more rayuwa wadanda da suka hada da ruwa, wurin kiwo da masana'antar tatsar madara tare da kasuwanni.

Ganduje ya nuna damuwarsa da yadda makiyayan suka dade suna wahala, kamar yadda ya ce, sun fuskanci tozarta a Najeriya ta yadda suke rasa rayukansu sannan ake sace musu Shanu.

Ganduje ya tunatar da cewa, ba a san bafulatani na gaske da hargitsi ba. Tozarcin da suke fuskanta ne yasa suka fara daukar fansa.

"A yau sai ka ga bafulatani yana fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran miyagun al'amura a rayuwa. Wannan ne yasa muka gane yana bukatar wurin zama mai dauke da dukkan ababen bukata," in ji Ganduje.

Ya kara da cewa, abun takaici ne yadda galan din madara ya fi na man fetur tsada. Wannan kadai ya isa ya sa a gane cewa Fulani na cikin wani hali a kasar nan.

"An gano cewa Fulani masu dauke da miyagun makamai na shigowa Najeriya ta kasashen Mali, Kamaru da sauran kasashen Afrika," ya kara da cewa.

A yayin jawabi a madadin wadanda suka amfana, sakataren kungiyar Miyetti Allah ta jihar Kano, Zubairu Ibrahim, ya jinjinawa gwamnan a kan cika alkawarinsa da yayi.

Ya tabbatar wa Ganduje cewa za su yi amfani da babban aikin da ya yi musu yadda ya dace.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel