Musulmi Sun Yi Babban Rashi, Sarki Mai Martaba a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Musulmi Sun Yi Babban Rashi, Sarki Mai Martaba a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Sarkin Epe da ke jihar Legaas, Mai Martaba Shefiu Ọlatunji Adewale ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 86 a ban ƙasa
  • An ruwaito cewa basaraken wanda ya hau karagar mulki a shekarar 2009, ya ba da gudummuwa mai tarin yawa wajen ci gaban Epe
  • Masarautar Epe ba ta fitar da sanarwa a hukumance game da rasuwar ba amma bayanai sun nuna za a masa jana'iza bisa koyarwar musulunci yau Asabar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Mai Martaba Sarkin Epe da ke Jihar Legas (Olu-Epe na Epe), Shefiu Ọlatunji Adewale Eshilokun I, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 86 a duniya.

Marigayi Sarkin, wanda ya hau karagar mulki a shekarar 2009, tsohon ma’aikacin gwamnati ne da ya shafe tsawon shekaru 37 kafin ya yi ritaya.

Kara karanta wannan

'Akwai babbar barazana ga APC,' Babban lauya ya fadi abin da zai kifar da Tinubu

Oba Shefiu Ọlatunji Adewale.
Sarki Epe a jihar Legas, Shefiu Ọlatunji Adewale Eshilokun I, ya rasu Hoto: Scouter Aliu Amisu
Source: Facebook

Tribune Nigeria ta tattaro cewa daga cikin muƙaman da ya riƙe akwai kwamishina a hukumar kula da jin daɗin ma'aikata.

Sarki Shefiu Ọlatunji Adewale ya rasu

Duk da babu wata sanarwa a hukumance daga fadar basaraken, bayanai sun nuna cewa za a yi jana'izar sarkin yau Asabar kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Marigayi Oba Adewale, shugaba ne na kwarai wanda ake ganin ya sadaukar da rayuwarsa don ci gaban masarautar Epe, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ya samu girmamawa sosai daga jama'ar yankin masarautar saboda hikima, iya shugabanci, da kuma yadda yake maida hankali kan aikin taimakon jama'a.

Oba Adewale ya kasance mai kishin zaman lafiya da hadin kai, inda ko yaushe yake jaddada muhimmancin haɗin kan ‘yan asalin kabilar Yarbawa da ke zaune a Epe.

Sarkin Epe.
Za a yi jana'izar Sarkin Epe kamar yadda addinin musulunci ya tanada Hoto: Aliu Amisu
Source: Facebook

Abubuwan da sarkin ya maida hankali a mulkinsa

A wata hira da aka yi da shi a 2017, basaraken ya bayyana manufar mulkinsa, tare da kiraye-kirayen zaman lafiya da girmama juna tsakanin al’ummar Epe a jihar Legas da Ogun.

Kara karanta wannan

Nahiyar Afirka ta yi babban rashi, fitaccen marubuci ya riga mu gidan gaskiya

A cewar marigayin:

“Muna da kyakkyawar alaka ta girmama juna, babu wariya tsakanin mutane. Duk lokacin da muke gudanar da bukukuwanmu na shekara-shekara na KayoKayo bayan bikin Ileya, mutane da yawa na halarta.
"Matasanmu na mu’amala da juna cikin 'yanci suna jin daɗin bukukuwan. Haka nan muna halartar bukukuwan Ebi da na masu rufe fuska a matsayin nuna hadin kai.
"Don haka, muna rayuwa cikin zaman lafiya ba tare da kiyayya ba. Abin da ke da muhimmanci shi ne samun ci gaba da yadda za mu kara bude Epe ga masu zuba jari duba da kusancinta Legas.

Turakin Dawakin Zazzau ya kwanta dama

A wani rahoton, kun ji cewa Turakin Dawakin Zazzau, Alhaji Ramalan Yero, mahaifin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero ya rasu.

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya yi alhinin wannan rashi trae da miƙa ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwan marigayin.

Uba Sani ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai daraja al’ada, addini da kuma dattijo, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262