Nuhu Ribadu Ya Koka kan Rashin Tsaro, Ya Fadi Adadin 'Yan Najeriya da Matsalar Ta Shafa
- Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), ya bayyana tasirin da matsalar rashin tsaro ta yi wa ƴan Najeriya
- Nuhu Ribadu ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro ta yi wa fannoni da dama illa musamman a ɓangaren saboda ƴan Najeriya manoma ne
- Mai ba shugaban ƙasan shawara ya nuna cewa miliyoyin ƴan Najeriya matsalar ta shafa wanda ya kawo cikas ga yadda suke gudanar da rayuwarsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya yi magana kan rashin tsaro a Najeriya.
Nuhu Ribadu ya bayyana cewa aƙalla mutane miliyan 150 ne matsalar rashin tsaro ta shafa a Najeriya.

Source: Facebook
Ribadu ya bayyana hakan ne a Abuja yayin rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya tsakanin cibiyar yaƙi da ta’addanci ƙasa da cibiyar International Institute of Tropical Agriculture, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan
Kudin mazaɓa: Tinubu ya ba kowane ɗan Majalisar Tarayya Naira biliyan 1? Bayanai sun fito
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manufar yarjejeniyar ita ce bunƙasa harkar kasuwancin noma da ƙarfafa hanyoyin rayuwa ga al’ummomin da ayyukan ta’addanci suka shafa.
Me Ribadu ya ce kan rashin tsaro?
Ribadu ya ce rashin tsaro ya yi matuƙar lahanta fannin noma, wanda shi ne babbar sana’a ga mafi yawan ƴan Najeriya.
“Rashin tsaro shi ne babbar matsalar da muke fuskanta a dukkan fannoni, amma fannin da yafi fuskantar mummunan tasiri shi ne noma. Saboda da ya zo, ya shafi rayuwar mu. Ƴan Najeriya manoma ne."
“Ko dai kai manomi ne, ko kuma ka fito daga gidan manoma. Saboda haka ya shafi kowane ɗayan mu ta wata hanya ko wata. Rashin tsaro ya jefa rayuwar mu cikin ruɗani. Abin da ya fi shi ne mu haɗa kai. Dole ne mu haɗu domin mayar wa mutanen mu da rayuwarsu."
“Mutanen mu na cikin mawuyacin hali. Ban ga wata ƙasa a duniya da take fuskantar ƙalubalen da muke fuskanta ba. Saboda mu manya ne, kuma mutanenmu na da yawa. Yawan mutanen da rashin tsaro ya shafa a Najeriya na iya wuce miliyan 120 zuwa 150."
- Nuhu Ribadu

Source: Twitter
Ribadu ya ba da shawara kan rashin tsaro
Ya yi kira da a ɗauki mataki a matsayin al'umma don magance tushen matsalolin rashin tsaro, ciki har da talauci da rashin samun damarmaki.
Ribadu ya gargaɗin cewa rashin tsaro na barazana ga zaman lafiyar ƙasa, yana mai jaddada cewa rugujewar wasu ƙasashe makwabta a yankin Sahel ya samo asali ne daga matsalolin ƴan tawayen da suka addabe su.
Nuhu Ribadu ya ce an kashe ƴan ta'adda 13,543
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana adadin ƴan ta'addan da aka kashe.
Nuhu Ribadu ya bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya sun kashe ƴan ta'adda 13,543 a cikin shekara biyu da suka gabata.
Mai ba shugaban ƙasan shawara kan harkokin tsaron ya ce nasarar ta samu ne bayan aiwatar da dabarun tsaro, haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da kuma jajircewa wajen dakile ƴan ta’adda a sassan Najeriya.
Asali: Legit.ng
