Malamai Sun Yi Wa Alhazan Najeriya Nasiha a Saudiyya, Sun Taɓo Batun Tinubu da Shugabanni
- Malaman addinin musulunci na hukumar NAHCON sun yi wa alhazan Najeriya nasiha kan yi wa shugabanni addu'a a Saudiyya
- Malaman sun bukaci alhazan kasar nan su yi koyi da Annabi Muhammad (SAW) wajen yi wa ƙasarsu addu'a duk da abubuwa sun taɓarɓare
- Sun tuna wa maniyyatan yadda Annabi ya yi wa Makkah addu'a duk da halin ƙunci da korar da aka masa tare da sahabbansa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Saudi Arabia - Malaman Addinin Musulunci na Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) sun gargadi Mahajjata 'yan Najeriya da su daina zagin shugabannin ƙasarsu.
Da yake zantawa da 'yan jarida a Makkah ranar Alhamis, Rafee Al-Ijebuwi, babban limamin Ijebu-Igbo a jihar Ogun kuma mamba na tawagar malamai ta NAHCON, ya ce Najeriya na bukatar Allah SWT ya kawo mata ɗauki.

Kara karanta wannan
Musulmi sun yi babban rashi, Sarki mai martaba a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Source: Facebook
Sheikh Al-Ijebuwi ya ce ya kamata mahajjata su yi koyi da Annabi Muhammad (SAW), wanda ya yi wa Makkah addu’a saboda ƙaunar mahaifarsa, The Cable ta rahoto.
Malamai sun ja hankalin alhazan Najeriya
A rahoton This Day, Malamin ya ce:
“Dangane da Najeriya, kowanne mahajjaci da ya zo kasa mai tsarki, ya kamata ya nuna soyayya ga ƙasarsa kuma ya rika yi mata addu’a.”
“Ya kamata mahajjaci ya so Najeriya kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya so Makkah (duk da yadda mutanen Makkah suka masa)"
“Game da shugabanninmu, nauyi ne a kan kowane mahajjaci, mace da namiji, ya yi addu’ar Allah ya shiryar da shugabanni zuwa ga abin da zai amfani talakawa. Bai kamata a zage su ba."
Malam Garba Al-Yolawi, babban limamin masallacin Area 10 a Abuja, shima ya bukaci mahajjata da su dage da yi wa shugabannin Najeriya addu’o’i.
Najeriya na bukatar taimakon Allah
Shehin Malamin ya ce Najeriya na fama da kalubale a fannonin tsaro, tattalin arziki, tarbiyya da shugabanci, wanda ke bukatar taimakon Allah.
Ya ce:
“Muna bukatar taimako daga Allah. Idan mahajjata kusan 50,000 suka yi addu’a da gaske, Allah zai iya sauya komai.”

Source: Facebook
Ya kuma gargadi masu yi wa shugabanni mummunan fata, yana mai cewa irin wannan addu’a na iya dawowa da illa.
“Amma bai kamata mu yi wa direban motar (wato shugabanmu) addu’ar ya yi hadari ba, alhali mu ma muna cikin motar. Idan direban ya yi hadari, mu ma hakan zai shafe mu.
“Ya kamata mu rika addu’ar Allah ya shiryar da su, ya bude zukatansu zuwa alheri, su dawo hanyar da ta dace," in ji shi.
Ƴar Najeriya ta yi abun yabo a Makkah
A wani rahoton, kun ji cewa ƴar Najeriya daga cikin mahajjatan bana, Hajiya Zainab ta mayar da Dala 5,000 da ta tsinta ga mai su a Saudiyya.
Dubban dalolin da suka kai kimanin ₦8,240,000 a kudin Najeriya, Zainab ta tsince su ne a masallacin harami da ke birnin Makkah.
Wannan kyakkyawar ɗabi'a da halin kirki da mahajjaciyar ta nuna a ƙasa mai tsarki ya ja hankali, inda ake ci gaba da yaba mata.
Asali: Legit.ng
