Ana Kiki Kaka kan Zarginsa da Cin Zarafi, Akpabio Ya Goyi bayan Karo Mata a Majalisa
- Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya goyi bayan karin kujeru ga mata a majalisa domin dafa masu wajen tabbatar da ci gaban al'umma
- Kudirin na neman ƙara kujeru na musamman ga mata daga kowace jiha da Abuja, sannan a samar da na 'yan majalisu mata uku a majalisar dokokin jihohi
- A yanzu haka, mata 18 ne kawai a cikin wakilai 469, lamarin da ta bayyana yadda aka mayar a mata saniyar ware a harkokin majalisar kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga kudirin karin kujeru na musamman ga mata.
Kudirin, wanda aka jima ana fafutukar tabbatar da shi na neman bai wa mata karin wakilci a matakai daban-daban na dokoki a Najeriya.

Source: Facebook
The Cable ta ruwaito, kudirin yana neman ƙara kujera daya ta musamman ga mata daga kowace jiha da kuma babban birnin tarayya a majalisar dattawa da ta wakilai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan zai tabbatar da karin wakilcin mata a kowanne matakin dokoki na kasa, yayin da ake kukan ana tauye su a siyasa.
Abin da kudirin majalisa ya kunsa
Nigerian Tribune ta wallafa cewa kudirin ya tanadi a samar da kujera uku na musamman ga mata a kowace majalisar dokoki ta jihohi.
Ana sa ran fara aiwatar da shi bayan wa'adin wannan majalisa ya kare, sannan za a rika sake duba dokar bayan shekaru 16 domin tantance yadda ta yi tasiri.

Source: Facebook
Akpabio ya bayyana goyon bayansa ne a ranar Alhamis yayin da wata tawagar masu rajin kare hakkin mata, ƙarƙashin jagorancin Osasu Igbinedion-Ogwuche, ta kai masa ziyara.
Ziyarar ta samu halartar kungiyoyin fafutukar kare hakkin mata kamar UN Women, Women in Politics Forum, Nigerian League of Women Voters, da kuma wakilan gidauniyar Gates.

Kara karanta wannan
Ambaliya: Ana tsoron rayuka sama da 50 sun salwanta bayan gano gawarwaki 15 a Neja
An nemi majalisa ta taimaka wa mata
A yayin ganawar, Osasu ta bayyana cewa adadin mata a harkokin siyasa musamman a majalisar dokoki, abin damuwa ne matuka.
Ta ce:
“Mata na da kasa da kashi biyar cikin dari a majalisar dokoki. A yanzu haka mata 18 ne kawai cikin wakilai 469, a ƙasar da mata ke kusan rabin yawan jama'a."
Wadanda suka halarci taron sun hada da Sanata Abdul Ningi, Sanata Abba Moro, Sanata Ipalibo Harry-Banigo, Sanata Enyinnaya Abaribe da wasu 'yan majalisar dattawa.
An fara gabatar da kudirin tun a zangon majalisa na tara ta hannun Nkeiruka Onyejeocha, amma yanzu Benjamin Kalu, mataimakin kakakin majalisar wakilai, da wasu 12 ne fafutuka kan batun.
Majalisa: Bayanai sun fito kan bidiyon lalata
A baya, mun wallafa cewa wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya haddasa ce-ce-ku-ce a tsakanin 'yan Najeriya, inda aka nuna wani dan majalisa yana sumbutar wata.
Bidiyon, wanda ya dauki tsawon mintuna biyu da daƙiƙa 10, ya bayyana wani mutumi da aka ce sanata ne mai ci tare da wata mace a cikin wani ofis da ake zargin na majalisa ne.
A wata sanarwa da ya fitar, kakakin majalisar dattawa kuma shugaban kwamitin hulda da jama’a, Sanata Yemi Adaramodu, ya bayyana cewa bidiyon ba na wani sanata ba ne.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
