Abin ba Daɗi: Ministan Tinubu Ya Bayyana Yadda Aka Kashe Mahaifinsa a Jihar Kaduna
- Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya tuna yadda mahaifinsa ya rasa rayuwarsa a rikicin addini a jihar Kaduna
- Tunji-Ojo ya ce an kashe mahaifinsa ne a lokacin da yake hanyar dawowa gida daga coci a shekarar 1992
- Ya ce rasa mahaifinsa ya tilasta masa komawa wurin mahaifiyarsa da zama, wanda hakan ya sa ya fuskanci kalubalen rayuwa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Ministan Harkokin Cikin Gida na Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana yadda mahaifinsa ya rasu sakamakon rikicin addini da ya faru a jihar Kaduna a shekarar 1992.
Dr. Tunji-Ojo ya ce lokacin da mahaifinsa ya rasu yana ɗan shekara 10 da haihuwa, inda ya ce wannan rashi ya taɓa rayuwarsa matuƙa.

Source: Twitter
Ministan ya bayyana haka a wani shiri na musamman shirin matasa' na gidan talabijin ɗin Channels tv ranar Alhamis.

Kara karanta wannan
"Ba ɗan ƙunar baƙin wake ba ne," Ministan Tinubu ya gano mutumin da ya tashi 'bam' a Abuja
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gabatar da wannan shiri na musamman da ministan ya halarta ne a wani ɓangare na bikin cikar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu shekaru biyu a kan mulki.
Yadda aka kashe mahaifin minista a Kaduna
"Na rasa mahaifina saboda matsalolin da suka shafi tsaro na cikin gida. Mahaifina an kashe shi ne a rikicin addini.
"Yana hanyar dawowa daga coci aka tare shi aka kashe shi a Kaduna a shekarar 1992."
- Olubunmi Tunji-Ojo.
Ya ce mutuwar mahaifinsa ta dagula masa rayuwa, inda hakan ya tilasta masa komawa wurin mahaifiyarsa, wacce ta raine shi tare da sauran ‘yan uwansa cikin wahala.
"Hakan ya jefa ni cikin mawuyacin hali tun daga tushe. Rayuwa ta yi mini tsanani a karkashin kulawar mahaifiyata,” in ji Tunji-Ojo.
Ministan ya bayyana cewa duk da irin wannan ƙalubale da ya fuskanta tun yana ƙarami, ya daure ya tashi da ƙarfi da azama, inda ya fara kasuwanci kuma ya ci nasara kafin daga bisani ya shiga aikin gwamnati.

Kara karanta wannan
Duk da ya haɗa kai da su Atiku, Tinubu ya aika saƙon taya murna ga Ministan Buhari

Source: Facebook
Tunji-Ojo ya yabawa shekaru 2 na Tinubu
A yayin shirin, Tunji-Ojo ya yaba da kokarin Shugaba Bola Tinubu wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa ta hanyar ɗaukar sahihan matakan gyara.
“Ina farin ciki da yadda shugaban ƙasa ya fara da ɗaukar muhimman matakai guda biyu. Kafin ya hau mulki, Najeriya ta fara kashe gobenta."
“Lokacin ina Majalisar Dokoki, mu ke nazarin kasafin kuɗi, kusan kashi 90 cikin 100 na kuɗin shiga na kasa ana kashe su ne wajen biyan ribar bashi, ba ma ainihin biyan bashin ba.
"Ba zai yiwu ka kashe kusan 90% na kudin shigarka wajen biyan bashi ba kuma ka zauna kana tunanin tattalin arziki zai bunƙasa."
Tunji-Ojo ya jaddada cewa irin wannan tsarin ba ya ɗorewa, kuma gyara ya zama dole don ceto tattalin arzikin Najeriya.
Ministan Abuja na fuskantar ƙalubale
A wani rahoton, kun ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa rashin biyan haraji ne babbar matsalar da yake fuskanta.
Wike ya faɗi hakan ne bayan da ya duba wasu ayyukan da ake dab da kammalawa a Abuja domin kaddamar da su a bikin cikar Tinubu shekara 2 a mulki.
Daga cikin ayyukan da ya duba akwai cibiyar taro ta kasa (AICC), da kuma fadada titin Obafemi Awolowo (N5), daga Life Camp zuwa Ring Road III.
Asali: Legit.ng
