Ambaliya: Mutum 12 daga Gida Daya Sun Rasu, Ana Zargin Almajirai 50 Sun Nutse a Neja

Ambaliya: Mutum 12 daga Gida Daya Sun Rasu, Ana Zargin Almajirai 50 Sun Nutse a Neja

  • Mutane 12 daga gida daya sun mutu a ambaliya da ta afku a Tiffin Maza da Anguwan Hausawa a karamar hukumar Mokwa, jihar Neja
  • Ana fargabar mutum fiye da 60 sun koma gidan gaskiya, ciki har da almajirai sama da 50 da har yanzu ba a kai ga gano inda suke ba
  • Ambaliya ta katse hanyar Arewa da Kudu, lamarin da ya haddasa cunkoso a babbar hanyar Mokwa yayin da ake ci gaba laluben jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Akalla mutum 12 daga gida daya na cikin wadanda suka rasa rayukansu a ambaliya da ta afku a yankin Tiffin Maza da Anguwan Hausawa na karamar hukumar Mokwa da ke jihar Neja.

Ambaliyar, wadda aka ce ta haddasa ɓacewar mutane da dama ciki har da almajirai fiye da 50, ta lalata gidaje da dama a yankin.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 36 sun nuna damuwa bayan ambaliya ta ruguza gidaje da mutane a Neja

Jihar
Mutane 12 yan gida daya sun rasu a Neja Hoto: Ɗulfa'ilu Ibn AbdulAzeez
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito Mokwa na daga cikin wuraren da direbobi da matafiya ke tsayawa domin hutu, lamarin da ya sa ya kasance cikin garuruwan da suka fi cunkoso a jihar Neja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa ambaliyar da aka ce ta samo asali ne daga ruwan sama mai karfi da aka yi a daren Laraba, ta fi shafar yara da mata.

Ana fargabar mutum fiye da 60 sun mutu

BBC Hausa ta wallafa cewa hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane 21, amma mazauna yankin na fargabar cewa adadin na iya haura 60.

Wata daliba mai suna Binta, wadda ta je Mokwa hutun makaranta, na daga cikin wadanda suka mutu, kuma rahotanni sun ce an gano gawarta.

Wata mazauniyar yankin, Hajiya Hassana Mokwa, ta ce mutane 12 daga cikin 13 na danginta sun mutu a ambaliyar, yayin da daya kacal ya tsira kuma yana asibiti.

Kara karanta wannan

An kama boka yana kokarin arcewa daga Najeriya bayan samun kabari a gidansa

Umar Bago
Ana tsoron almajirai sama da 50 sun mutu a ambaliyar Neja Hoto: Suleiman Ibrahim/Umar Bago
Source: Facebook

Ta kara da cewa har ila yau ambaliyar ta kashe almajirai da dama daga wani makarantar allo mallakin dan uwanta.

Ta ce:

“Yawancin almajirai daga makarantar dan uwana sun mutu. Babu wanda ya tsira daga cikin su, kuma ginin gaba daya ya nutse. Idan ka je wurin yanzu, ba za ka gane cewa an taba gina wani gida a wurin ba.”

Jama’a sun shiga firgici a Neja

Wani mazaunin yankin, Malam Hamza Mahmud, ya ce an gano gawar mutane biyu daga cikin iyalinsa, yayin da uku har yanzu ba a same su ba.

Rahotanni sun ce an gano gawar wata mata mai ciki da misalin 6.00 na yamma, kuma 'ya'yanta hudu na daga cikin wadanda ba a same su ba.

Fiye da almajirai 50 daga wata makarantar allo ba a san inda suke ba har zuwa karfe 7:00 na yammacin jiya.

Wani daga cikin majiyoyi, Alhaji Baba Adamu, ya ce:

Kara karanta wannan

Ambaliya: Ana tsoron rayuka sama da 50 sun salwanta bayan gano gawarwaki 15 a Neja

“Yawancin wadanda suka mutu mata da yara ne. Akwai maza amma ba su kai yawan matan da yara ba. Har yanzu yara da dama daga wata makarantar allo ba a same su ba.”

Ambaliya ta mamaye gari a Neja

A baya, mun wallafa cewa mazauna garin Mokwa da ke jihar Neja na cikin halin kakanikayi bayan wata mummunar ambaliya da ta afku sakamakon ruwan sama mai karfi.

Ambaliyar ta lalata manyan gidaje a garin, yayin da ta shafe wasu tare da katse babbar hanyar da ke hade Arewa da Kudancin Najeriya, wacce ke wucewa ta cikin garin Mokwa.

Shugaban karamar hukumar Mokwa, Hon. Jibrin Abdullahi Muregi, ya bayyana cewa duk da ana samun ambaliya a yankin, amma wannan ne karin farko da aka samu wanda ya yi muni.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng