Tsadar Rayuwa: An Sanya Ranar Fara Sabuwar Zanga Zangar Adawa da Mulkin Tinubu

Tsadar Rayuwa: An Sanya Ranar Fara Sabuwar Zanga Zangar Adawa da Mulkin Tinubu

  • Kungiyar #EndBadGovernance ta shirya zanga-zanga a ranar 12 ga Yuni, domin nuna bacin ran ‘yan ƙasa kan gwamnatin Bola Tinubu
  • Comrade Hassan Soweto ya ce cire tallafin mai da faduwar Naira sun haddasa fatara mai tsanani, inda tsadar abinci ta zarce kashi 40
  • Kungiyar ta bukaci jami'an tsaro su tabbatar da zaman lafiya yayin zanga-zangar, tana mai zargin gwamnati da take dimokuradiyya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Kungiyar #EndBadGovernance ta sanar da shirinta na gudanar da zanga-zangar kasa baki daya a ranar 12 ga Yuni, 2025, wadda ta yi daidai da ranar dimokuradiyya.

Shugaban kungiyar, Comrade Hassan Soweto, ya bayyana hakan a Legas, a ranar 29 ga Mayu, inda ya ce zanga-zangar za ta bayyana bacin ran ‘yan kasa kan gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

'Akwai babbar barazana ga APC,' Babban lauya ya fadi abin da zai kifar da Tinubu

Matasa sun shirya gudanarf da sabuwar zanga-zangar adawa da gwamantin Tinubu a Yuni
Matasa na zanga-zangar tsadar rayuwa a watan Agusta, 2024 a sassan Najeriya. Hoto: Supers
Source: Facebook

'Mulkin Tinubu bala'i ne' - Soweto

Hassan Soweto ya bayyana cewa gyare-gyaren tattalin arzikin Tinubu, musamman cire tallafin mai da karya farashin Naira, sun jefa miliyoyin mutane cikin talauci, inji rahoton Daily Trust.

Ya ce manufofin da aka ce za su jawo hannun jarin waje sun haddasa faduwar darajar Naira da 70% da hauhawar farashin abinci da ya zarce 40%.

Jagoran kungiyar ya bayyana mulkin Bola Tinubu na shekaru biyu da cewa “bala’i ne,” inda ya ce sauye-sauyen tsarin kasuwanci sun rusa rayuwar jama’a da tattalin arzikin kasa.

Ya kara da cewa matsalolin da kungiyar ke kuka da su ba na tattalin arziki kadai ba ne, har da “take dimokuradiyya” da gwamnatin Tinubu ke yi da sunan mulkin farar hula.

An zargi Tinubu da lalata tattalin arziki

Comrade Soweto ya ce gwamnatin ta rage damarmakin ‘yan kasa wajen bayyana ra’ayinsu, lamarin da ya kwatanta da kama-karya irin ta mulkin soja a cikin dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

Hakeem Baba ya sake sukar gwamnati, ya fadi masifar da Tinubu zai jefa talaka

“A bayyane muke fadin cewa shekaru biyu na mulkin Tinubu bala’i ne ga mafi rinjayen al’umma. Manufofinsa masu cutar da talakawa sun lalata tattalin arziki.”

- Hassan Soweto.

Ya ce cire tallafin mai da faduwar Naira sun lalata tattalin arzikin kasa gaba daya, kuma an hana jama’a ‘yancin rayuwa da dimokuradiyya ta tanadar.

Soweto ya bukaci sufeto janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, da kwamishinan ‘yan sanda na Legas, Olohundare Moshood Jimoh, su tabbatar da zaman lafiya yayin zanga-zangar.

An zargi gwamnatin Bola Tinubu da lalata tattalin arziki da jefa 'yan kasa a talauci
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Matasa za su yi zanga-zanga a Yuni, 2025

Ya tuna yadda jami’an tsaro suka harba barkonon tsohuwa da harsasai ga masu zanga-zanga a shekarar 2024, yana mai cewa hakan ya ci karo da kare hakkin dan Adam.

Kungiyar ta bukaci a hukunta jami’an da suka kashe mutane a zanga-zangar 2024 tare da bai wa iyalan wadanda aka kashe diyya, kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

“A yau ‘yan Najeriya suna rayuwa kamar bayi, inda ‘yancin fadin albarkacin baki da na siyasa da aka yi wa fama a baya, an soke su baki daya.”

- Soweto.

Kara karanta wannan

NEC: Atiku, Wike da wasu jiga jigan PDP sun yi watsi da babban taron jam'iyya

Ya ce kungiyar tana cikin shirin sabunta dabarunta domin karfafa fafutukar da za su ci gaba da yi a ranar 12 ga Yuni da kuma bayan hakan.

'An kashe mutane 24 a zanga-zangar 2024' - Amnesty

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Amnesty International ta ce an kashe mutane 24 a Najeriya yayin zanga-zangar #EndBadGovernance daga 1 zuwa 10 ga watan Agusta.

A cewar rahoton, fiye da mutum 1,200 ne aka kama a lokacin zanga-zangar, inda aka jiyo cewa an azabtar tare da cin zarafinsu, ciki har da kananan yara da matasa.

Amnesty ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya kafa kwamitin bincike kan wannan take hakkin bil’adama tare da ɗaukar mataki don samun adalci ga waɗanda aka zalunta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com