'Yan Bindiga Sun Kutsa har cikin Fada, Sun Yi Awon gaba da Basarake a Nasarawa
- Ƴan bindiga sun bi dare sun tafka ta'asa a wani harin ta'addanci da suka kai a jihar Nasarawa da ke yankin Arewa ta Tsakiya
- Miyagun ƴan bindigan sun kutsa cikin fadar basaraken a ƙaramar hukumar Kokona bayan sun yi harbi kan mai uwa da wabi
- Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da an sace basaraken yayin harin, inda ta ƙara da cewa ta fara ƙoƙarin ganin an kuɓutar da shi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Nasarawa - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi awon gaba da wani basarake a jihar Nasarawa.
Ƴan bindigan sun sace basaraken ne a wani hari da suka kai a fadarsa da ke ƙaramar hukumar Kokona ta jihar Nasarawa.

Source: Facebook
Ƴan bindiga sun sace basarake a Nasarawa
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ƴan bindigan sun yi harbi kan mai uwa da wabi kafin daga bisani suka yi awon gaba da basaraken.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu mazauna yankin sun tabbatar da cewa an sace Sangarin Dari, Mista Emmanuel Omanji, daga gidansa ne a daren ranar Laraba yayin harin da ƴan bindigan suka kai.
A cewar wata majiyar, maharan sun dirar wa gidan basaraken ne ɗauke da makamai, suka fara harbe-harbe ba tare da kakkautawa ba, sannan suka yi awon gaba da shi zuwa wani wurin da ba a sani ba.
Ƴan sanda sun fitar da bayani
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa, Ranham Nansel, ya tabbatar da faruwar lamarin, cewar rahoton tashar Channels tv.
Kakakin rundunar ya bayyana cewa kwamishinan ƴan sanda na jihar, CP Shetima Jauro Mohammed, ya tura jami’an sashen yaki da garkuwa da mutane na rundunar, tare da hadin gwiwar sojoji da ƴan sa-kai domin gudanar da aikin ceto.
Ranham Nansel ya ce za a kama waɗanda suka aikata wannan aika-aikar kuma za a ceto basaraken cikin ƙoshin lafiya.
A cewarsa, kwamishinan ya nemi duk wanda ke da wani muhimmin bayani da zai taimaka wajen gudanar da aikin ceto da ya tuntuɓi rundunar ƴan sanda ba tare da ɓata lokaci ba.
“Kwamishina ya tabbatar da cewa za a ceto basaraken cikin ƙoshin lafiya, kuma ya roƙi duk wani da ke da bayani mai muhimmanci da kada ya yi ƙasa a gwiwa wajen sanar da ƴan sanda."
- Ranham Nansel

Source: Original
Karanta wasu labaran kan hare-haren ƴan bindiga
- 'Yan bindiga sun mamaye unguwa a Abuja cikin dare, sun sace mutane da dama
- 'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaro a Katsina, an samu asarar rayuka
- Zamfara: Ƴan bindiga sun shammaci masu sallah a masallaci, sun kwashe al'umma
Ƴan bindiga sun kai hari a Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da mugayen makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Neja.
Ƴan bindigan waɗanda yawansu ya haura mutum 100, sun kai harin ne a wasu ƙauyuka guda uku na ƙaramar hukumar Munya.
Ƴan bindigan sun riƙa bi ƙauye bayan ƙauye suna cin karensu babu babbaka, inda suka kashe mutane tare da ƙona gidaje da sace kayan abinci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
