'Za a Rataye Shi': Kotun Najeriya Ta Yanke wa Malamin Musulunci Hukuncin Kisa

'Za a Rataye Shi': Kotun Najeriya Ta Yanke wa Malamin Musulunci Hukuncin Kisa

  • Wata babbar kotun jihar Osun ta yanke wa Kabiru Ibrahim, malamin addini, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe Lukman Adeleke
  • Alkalin kotun, Mai shari’a Adegoke, ya ce hujjojin da masu kara suka gabatar sun tabbatar da Kabiru ya kashe Adeleke bayan karɓar kudinsa
  • Bayan ya amsa laifi, Kabiru ya kai ‘yan sanda inda aka tono gawar Adeleke cikin jaka, an yanke tafin hannunsa, kuma kotu ta karɓi hotunan hujja

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Osun - Wata babbar kotun jihar Osun da ke zamanta a garin Iwo, ta yanke wa wani malamin addinin Musulunci, Kabiru Ibrahim, hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Mai shari’a Lateef Adegoke ya ce masu gabatar da kara sun gabatar da hujjojin da suka tabbatar da cewa Kabiru ya kashe abokin huldarsa, Lukman Adeleke.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Ana tsoron rayuka sama da 50 sun salwanta bayan gano gawarwaki 15 a Neja

Kotu ta yanke wa malamin addini hukuncin kisa ta hanyar rataya a Osun
Harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja. Hoto: Federal High Court of Nigeria
Source: UGC

Kotu ta yanke wa malami hukuncin kisa

An gurfanar da Kabiru Ibrahim da laifuffukan hada baki, kisa da sata, wanda ya sabawa sashe na 324, 319(1), da 390 na dokar laifuffuka, Cap. 34, dokokin jihar Osun, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari’a Lateef, yayin da yake yanke hukunci, ya ce masu gabatar da kara sun gabatar da hujjoji kwarara da suka tabbatar da Kabiru Ibrahim ya aikata laifin.

Sakamakon kama wanda ake zargi da aikata kisan kai, alkalin kotun ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Bayanin zaman kotun da hukuncin da aka yanke na kunshe a cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar shari’a ta Osun, Opeyemi Bello, ya fitar a Osogbo a ranar Laraba.

Opeyemi ya bayyana cewa shugaban tawagar masu gabatar da kara, Abiodun Badiora, ya shaida wa kotu cewa Kabiru Ibrahim ya kasance mai yi wa mamacin ayyuka na addu'o'i.

Kara karanta wannan

An kai farmaki gidan boka, an kama mutane 3 suna kokarin asiri da yarinya

Yadda malamin ya kashe Lukman a Osun

Badiora ya bayyana cewa mamacin ya je wurin Ibrahim ne yana neman shawara kan sayen wani fili, sai Kabiru ya bukaci ya kawo kudin domin yi masa addu’a kafin ya biya mai filin.

Amma daga wannan rana, aka nemi Lukman aka rasa. Daga baya, danginsa sun samu labari daga wani da ya shaida cewa ya ga Lukman a ranar da ya ziyarci gidan Kabiru.

Sanarwar ta ce:

“Yayin da iyalansa suka tunkari Malam Kabiru Ibrahim da maganar, sai ya fara musanta cewa ya hadu da Lukman, inda ya ce sun shafe fiye da makonni biyu ba su hadu ba.
"Amma wani mazaunin unguwar ya karyata hakan, ya ce shi da kansa ya kai Lukman gidan Kabiru a ranar da ya bace.
“Bayan an kai rahoto ga ‘yan sanda, yayin tambayoyi, Ibrahim ya amsa cewa shi ne ya kashe Adeleke.
"Daga nan ya jagoranci jami’an tsaro zuwa hanyar Ilesa/Akure, aka gano gawar Adeleke a cikin wata jaka, an yanke daya daga cikin tafin hannunsa."

Kara karanta wannan

Mutane 2 sun rasu da suka ɗauko ragunan layya da Babbar Sallah a Najeriya

Kotu ta tabbatar da cewa an samu malamin Musulunci da laifin kashe wani, don haka za a rataye shi
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Osun. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Hukuncin da kotu ta yanke wa malamin

Sanarwar ta ce kotun ta karɓi hujjojin hoto da kuma jawabin malamin na amsa laifin da ya aikata a matsayin shaida.

Sanarwar ta kara da cewa lauyan da ya kare Ibrahim (wanda ba a bayyana sunansa ba) bai mayar da martani kan jawaban karshe da masu kara suka rubuta ba.

Yayin da yake yanke hukunci, Mai shari’a Adegoke ya same shi da laifin kisan kai da sata, sai ya yanke masa hukuncin dauri na shekaru bakwai saboda sata da kuma kisa ta hanyar rataya saboda kashe Lukman.

Za a rataye matashin da ya kona masallaci a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, an yanke wa Shafiu Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kotu ta same shi da laifin babbake masallata a Kano.

Mai Shari’a Halhalatun Huza’i Zakariya ta tabbatar da laifin kisan jama’a da ake zargin Shafiu da aikatawa a watan Mayun 2024, lokacin da ya kone wani masallaci.

Bayan hukuncin kisa, kotun ta kara da wasu hukunce-hukunce biyu, wanda hakan ya rufe cikakkiyar shari’ar da ake yi wa matashin a gaban kotun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com