"Ya Gaza": Tsohon Gwamna Ya Caccaki Tinubu kan Kuntatawa 'Yan Najeriya
- Tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam, ya taso Shugaba Bola Tinubu a gaba bayan cikarsa shekara biyu kan mulki
- Suswam ya bayyana cewa shugaban ƙasan bai taɓuka komai ba face kawo tsare-tsare waɗanda suka jefa ƴan Najeriya cikin wahala
- Tsohon Sanatan ya shawarci Tinubu da kada ya biyewa masu zuga shi kan ya nemi tazarce a 2027, domin ba zai kai labari ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Yayin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke bikin cika shekaru biyu a mulkinsa, tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam, ya yi magana kan mulkinsa.
Gabriel Suswam ya bayyana cewa shugaban ƙasar bai yi ƙoƙari ba wajen rage wahalar da ƴan Najeriya ke fuskanta.

Source: Facebook
Suswam ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Politics Today' na tashar Channels Tv a ranar Laraba, 28 ga watan Mayun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Suswam ya soki salon mulkin Tinubu
Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu bai ɗauki matakan rage raɗaɗin wahalhalun da manufofin gwamnatin jam’iyyar APC suka haifar ba.
A cewarsa, gwamnatin APC wacce Tinubu ke jagoranta ba ta nuna kulawa da damuwar ƴan Najeriya ba.
“A matsayina na ɗan Najeriya, kuma kamar yadda yawancin mutane za su gani, ba su taɓuka abin a zo a gani ba. Hakan kuwa a bayyane yake duba da halin da ake ciki."
“A matsayina na ɗalibin ilmi kan tattalin arziƙin duniya, zan iya cewa idan za ka aiwatar da wasu manufofin tattalin arziƙi da za su yi mummunan tasiri ga rayuwar talakawa, to ya kamata a lokaci guda ka samar da hanyoyi da za su rage wannan raɗaɗi."
“Abin takaici, kun rage darajar kudin ƙasar nan, kun cire tallafin makamashi da sufuri. Ba wata ƙasa, musamman irin ta mu mai tasowa, da za ta iya jure irin wannan yanayi, musamman ma ganin cewa ba mu samar da abubuwan da muke buƙata da kanmu."

Kara karanta wannan
Malamin addini ya fito karara ya gayawa Tinubu abin da zai hana shi tazarce a 2207
- Gabriel Suswam
Gabriel Suswam ya ba Tinubu shawara
Sai dai kuma, tsohon gwamnan ya shawarci shugaban ƙasa da ya manta da zuga shi da wasu ke yi na neman tazarce, musamman ganin cewa ƴan Najeriya ne ke yanke hukunci a zaɓe, ba jam’iyyun siyasa kaɗai ba.

Source: Facebook
"Ni ba ni da wata matsala da shugaban ƙasa da ke kan mulki ya sake tsayawa takara idan komai yana tafiya daidai."
"Ana maganar haɗaka, wanene ya taɓa tunanin Peter Obi, wanda babu gwamnoni ko sanata a bayansa, zai iya samun ƙuri’u milyan biyar?"
“A wurare da dama, an ce shi ne ya ci zaɓe, amma an yi masa maguɗi. Saboda haka, mafi muni a cikin zaɓuɓɓuka shi ne wanda kake fafatawa da jama’a kai tsaye, ba fafatawa da jam'iyyu ba."
“Don haka shawara ta ga shugaban ƙasa ita ce, ya fuskanci ƴan Najeriya. Ya manta da ƴan kore waɗanda ke goya masa baya ko maganganun jam’iyyun siyasa."

Kara karanta wannan
"Kuɗin kamfe," Ɗan Atiku ya tayar da ƙura, ya jero abubuwa 3 da Tinubu zai yi da bashin N40trn
"A wurare da dama inda aka cire manyan shugabanni daga mulki, jam’iyyun siyasa ne suka cire su. Saboda haka ya fi muni ka fafata da jama'a fiye da jam'iyyun siyasa."
- Gabriel Suswam
Onaiyekan ya caccaki Bola Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanannen malamin addnin Kirista, Cardinal John Onaiyekan, ya soki salon mulkin Shugaba Bola Tinubu.
Malamin na ɗarikar Katolika ya bayyana cewa shugaban ƙasan ya jefa ƴan Najeriya cikin wahala a shekaru biyu da ya kwashe kan mulki.
Ya bayyana cewa idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka, ba zai yi nasara ba idan har an shirya sahihin zaɓe a shekarar 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
