An kai Farmaki Gidan Boka, an Kama Mutane 3 Suna Kokarin Asiri da Yarinya

An kai Farmaki Gidan Boka, an Kama Mutane 3 Suna Kokarin Asiri da Yarinya

  • Jami’an ‘yan sanda a Enugu tare da goyon bayan mazauna gari sun ceto wata yarinya ‘yar shekara 13 da aka sace domin yin asiri
  • An kama mutum uku da ake zargi da hannu a laifin, yayin da babban wanda ake zargi, wani boka mai suna Levi Onyeka Obu ya gudu
  • An gano gawa biyu da aka birne a wani wuri a gidan, lamarin da ya janyo gwamnatin Enugu rushe ginin da ake amfani da shi wajen aikata laifin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Enugu - Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta tabbatar da cewa jami’anta na yankin Umumba sun ceto wata yarinya ‘yar shekara 13 daga hannun masu satar mutane don asiri.

An gudanar da aikin ceto ne da safiyar ranar Talata, 27 ga Mayu, 2025 a Umuojor da ke ƙauyen Ishiagu, karamar hukumar Ezeagu ta jihar.

Kara karanta wannan

Yadda aka samu 'dan sandan da aka kashe a Kano da hannu a kisan 'barayin kaji' tun 2021

Enugu
An kai farmaki gidan boka a Enugu. Hoto: @Enugu_PoliceNg
Source: Twitter

Sanarwar da kakakin ‘yan sanda SP Daniel Ndukwe ya wallafa a X ta nuna cewa an kama mutum uku da ake zargi, yayin da babban wanda ake nema ya arce.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an 'yan sanda sun kai samamen ne tare da hadin gwiwar masu gadin unguwa da mazauna garin.

'Yan sanda sun kama masu asiri a Enugu

Wadanda aka kama sun hada da Uche Kingsley Agumba, Ilo Nweze Onyedikachi, da Ejike Odinwankpa, wadanda ake zargin suna aiki tare da bokan da ya tsere.

An ceto yarinya daya mintuna kafin a halaka ta, kamar yadda bincike ya tabbatar da cewa an kashe wasu mutane biyu da suka hada da mace da namiji, aka birne su a rami a cikin gidan.

An rushe gidan boka da ake asiri a Enugu

Wurin da aka ceto yarinyar yana cikin wani ginin da ba a kammala ba, wanda ake amfani da shi a matsayin wurin tsafi da kuma aikata miyagun laifuffuka.

Kara karanta wannan

Kisan sarkin Adara: Kotu ta samu El Rufa'i da laifi, an ci tarar shi N900m

Bayan samun tabbaci daga hukumomi, gwamnatin jihar Enugu ta rushe ginin da boka Levi Onyeka Obu, wanda aka fi sani da "Ezeani" ke amfani da shi.

Kwamishinan ‘yan sanda ya je gidan bokan

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Enugu, CP Mamman Bitrus Giwa, ya kai ziyara wurin da lamarin ya faru, inda ya yaba da jajircewar jami’ansa da ma’aikatan tsaro na garin.

Ya bada umarnin a kara zurfafa bincike da kokari wajen kamo bokan da ya tsere da kuma sauran wadanda suke da hannu a wannan aika-aika.

Yan sanda
'Yan sanda za su gurfanar da wadanda ake zargi da satar mutane. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Za a gurfanar da masu asiri da aka kama

Kwamishinan ya tabbatar da cewa za a gurfanar da wadanda aka kama bisa zargin satar mutane da kuma kisan kai don yin asiri.

Ya jaddada cewa rundunar ba za ta yi sassauci ba wajen ganin an hukunta duk masu hannu a laifin, don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.

An kama wanda ya kashe matar aure a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi da ake zargi da kashe wata matar aure.

Kara karanta wannan

An kama wanda ya shiga har gida ya yi wa matar aure yankan rago a Kano

Kakakin 'yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce matashin ya amsa cewa shi ya kashe matar.

A bayanin da ya yi, matashin ya ce shi ya kashe matar ta hanyar yanka wuyanta da wuka bayan ya shake ta da dankwali.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng