Atiku Ya Tono Manyan 'Kurakuran' Tinubu a Shekara 2, Ya Yi Raddi Mai Zafi
- Atiku Abubakar ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu na daya daga cikin gwamnatocin da suka fi gazawa a tarihin dimokuraɗiyya
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya zargi gwamnatin da jefa jama’a cikin talauci, tare da kashe kudin gwamnati ba tare da tunani ba
- Ya ce ko da yake ana fafutukar kafa kawancen jam’iyyun adawa, har yanzu babu tabbas kan wace jam’iyya za a hadu a kai a 2027
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya sake caccakar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da cewar tana kara jefa jama’a cikin kunci da talauci.
Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, yayin da gwamnatin Tinubu ke cika shekaru biyu a mulki, inda ya ce ta ci amanar talakawa da alkawurran da ta dauka.

Kara karanta wannan
Tinubu ya ƙara ƙarfi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya haƙura da neman mulki a 2027

Source: Facebook
Atiku Abubakar ya wallafa a X cewa 'yan adawa ba za su zuba wa Bola Tinubu ido yana mayar da Najeriya baya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton Arise News ya nuna cewa Atiku Abubakar ya ce gwamnatin Tinubu ce mafi jefa jama'a wahala a tarihin dimokuradiyya.
Atiku ya ce ko da yake ana ƙoƙarin kafa kawancen jam’iyyun adawa, har yanzu babu cikakken tabbaci kan wace jam’iyya za ta kasance matattarar 'yan adawa a 2027.
Atiku Abubakar ya ce Tinubu ya kara talauta jama’a
Atiku ya bayyana cewa a cikin shekara biyu kacal, gwamnatin Tinubu ta nuna gazawa ta fuskar shugabanci, kula da jama’a, da kuma rashin gaskiya a harkokin gwamnati.
Business Day ta wallafa cewa Atiku ya ce babu wata gwamnati da ta taba jefa jama’a cikin irin wannan matsi, yayin da manyan jami’ai ke ci gaba da karɓar kasafi mai yawa.
Atiku ya zargi Tinubu da fifita masu hali
A cewar Atiku, manufofin gwamnatin Tinubu duk sun fi cutar da talakawa, inda ake kara wa masu hali dama, yayin da marasa galihu ke wahala wajen samun ayyuka.
Ya ambato yadda gwamnatin ta kara kudin rajistar katin dan kasa da 75%, tare da kirkiro tsarin VIP ga wadanda za su biya kudi mai yawa don musu aiki da wuri.
'Shugaba Tinubu ya ci bashi sosai' Atiku
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce bashin da ke kan Najeriya ya karu daga Naira tiriliyan 49 zuwa Naira tiriliyan 144 cikin shekara biyu kacal.
Ya ce hakan na nuna cewa gwamnatin tarayya ce ke jagorantar yawaitar bashin, sabanin gwamnatocin jihohi da suka rage basussukansu.

Source: Facebook
Tallafin mai: Atiku ya caccaki gwamnatin Tinubu
Atiku ya zargi gwamnatin da cewa cire tallafin mai ba tare da tsari ba ne ya janyo matsanancin wahala da tattalin arziki ke ciki a yanzu.
Ya ce bai kamata a ci gaba da damun talakawa da karin kudi ba, yayin da gwamnati ke zuba biliyoyin kudi wajen biyan bukatun masu rike da madafun iko.
Tinubu ya ce ya yi nasara a shekara 2
A wani rahoton, kun ji cewa, gwamnatin Bola Tinubu ta fitar da nasarorin da ya samu a shekara biyu da ya shafe a kan mulkin Najeriya.
Fadar shugaban kasa ta ce Bola Tinubu ya samar da nasarori da dama musamman saboda tsare tsaren da ya kawo.
Shugaba Bola Tinubu ya ce an tallafawa matasa wajen inganta kananan sana'o'i da ba su lamunin karatu domin zuwa jami'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

