Buhari Ya Shilla Ganin Likita, Ya Aika Sako ga Shugabannin Afrika a Taron ECOWAS

Buhari Ya Shilla Ganin Likita, Ya Aika Sako ga Shugabannin Afrika a Taron ECOWAS

  • Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai samu damar halartar bikin cika shekaru 50 da kafa Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ba
  • An gudanar da babban taron wanda shugabannin kasashen Afrika da sauran jagorori a yankin suka halarta ranar Laraba a jihar Legas
  • Ta cikin wasikar da ya aika wa shugaban kasa, Bola Tinubu, Buhari ya nemi a yi masa uzuri, yayin da ya aika sakon taya murna ga jagororin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bai halarci bikin cika shekaru 50 da kafuwar Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) ba.

An gudanar da babban taron a jihar Legas domin murnar ci gaban kungiyar da aka kafa da zummar samar da ci gaba a yankin Afrika ta yamma.

Kara karanta wannan

Bayanin da Bola Tinubu ya yi wa Najeriya bayan cika shekara 2 a kan mulki

ECOWAS
Buhari bai halarci taron ECOWAS a Legas ba Hoto: Muhammadu Buhari/Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa taron ya samu halartar shugabannin kasashen yammacin Afrika da dama, ciki har da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin shugabannin da suka halarci taron su ne: Shugaba Faure Gnassingbé na Togo, Shugaba Joseph Boakai na Liberia da kuma Shugaban Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embaló.

Dalilin Buhari na rashin halartar taron ECOWAS

Vanguard News ta wallafa cewa a cikin wata wasika da aka aika wa Shugaba Bola Tinubu, Buhari ya bayyana takaici a kan rashin halartar taron mai cike da tarihi.

Ya kara da yabawa da juriyar kungiyar ECOWAS da kuma abubuwan da ta cimma tsawon shekaru 50 da kafuwarta.

Wani bangare na wasikar da Tinubu ya karanta ya ce:

“Kamar yadda ka sani, ina Birtaniya a halin yanzu ana duba lafiyar ta kamar yadda nake yi akai-akai, don haka ba zan iya halartar wannan taro na tarihi ba.”

Duk da rashin halartarsa, tsohon shugaba Buhari ya mika sakon taya murna ga shugabanni da al’ummomin kasashen yammacin Afrika na ganin shekaru 50 da kafuwar ECOWAS.

Kara karanta wannan

Tinubu zai kaddamar da manyan ayyuka a Kano da Legas kafin sallar layya

ECOWAS
An gudanar da taron cikar ECOWAS shekaru 50 da kafuwa Hoto: ECOWAS
Source: Facebook

Ya bayyana kungiyar a matsayin wata alama ta hadin kai, cigaba da juriya, duk da kalubale da yankin ke fuskanta.

Ya ce:

“Ina taya yallabai da sauran shugabannin kasashe murna bisa wannan muhimmin lokaci na cika shekaru 50 na ECOWAS.”

Buhari ya yabawa tsohon shugaban Najeriya

Tsohon shugaban ya kuma yi amfani da wannan dama wajen jinjinawa tsohon shugaban kasa Janar Yakubu Gowon mai ritaya, wanda shi ne kadai wanda ya rage daga cikin wadanda suka kafa ECOWAS.

Ya yaba da rawar da Gowon ya taka wajen kafuwar kungiyar da kuma irin yadda ya jajirce wajen tabbatar da hadin kan yankin, yana mai cewa:

“Ina mika sakon taya murna ta musamman ga Janar Gowon, wanda shi ne kadai da ya rage daga cikin wadanda suka kafa wannan kungiya mai albarka.”

Ya kammala wasikar da kalmomin goyon baya da fatan alheri ga Shugaba Tinubu da sauran shugabannin yammacin Afrika.

Buhari ya aika sako ga Bola Tinubu

Kara karanta wannan

NEC: Atiku, Wike da wasu jiga jigan PDP sun yi watsi da babban taron jam'iyya

A baya, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya taya Shugaba Bola Tinubu murnar cika shekaru biyu da ya yi yana jagorantar Najeriya a matsayinsa na shugaban ƙasa.

A cewar tsohon shugaban ƙasan, nasarorin da ake ƙoƙarin cimmawa a mulkin Tinubu ba za su zo dare ɗaya ba, sai dai ta hanyar sauye-sauyen wanda sai an yi hakuri da su.

Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da goyon bayan jam’iyyar APC da gwamnatin Bola Tinubu domin ganin sauye-sauyen da ake ƙoƙarin aiwatarwa sun kai ga nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng