Mutane 2 Sun Rasu da Suka Ɗauko Ragunan Layya da Babbar Sallah a Najeriya

Mutane 2 Sun Rasu da Suka Ɗauko Ragunan Layya da Babbar Sallah a Najeriya

  • Wata babbar mota da ta ɗauko raguna da shanun layya ta gamu da mummunan hatsari a jihar Osun ranar Litinin da ta gabata
  • Hukumar kiyaye haɗurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Osun ta tabbatar da cewa mutum biyu sun mutu, wasu 15 sun samu raunuka
  • Shaidu sun bayyana cewa motar kirar DAF ta faɗa ramin da ke gefen hanya sannan ta kife da mutanen da ta ɗauko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun - Akalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 15 suka jikkata a wani hadarin mota da ya faru a jihar Osun ranar Litinin.

Lamarin ya auku ne lokacin da wata babbar mota kirar DAF da ta dauko raguna da shanu na layya a Babbar Sallah daga jihar Kebbi ta kife a cikin rami a gefen hanya.

Kara karanta wannan

"Ba ɗan ƙunar baƙin wake ba ne," Ministan Tinubu ya gano mutumin da ya tashi 'bam' a Abuja

Jihar Osun.
Mutum 2 sun mutu da babbar mota ta fadi da ragunan sallah a Osun Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rahotan Vanguard ya bayyana cewa motar na kan hanyarta na zuwa garin Ikire domin siyar da dabbobin don bikin Babbar Sallah (Ileya) mai zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda hatsarin ya faru a Osun

Wani shaida mai suna Emmanuel Adegboye ya ce hadarin ya faru ne a kusa da Oke-Ofa da ke yankin Gbongan, lokacin da motar ta ci ƙarfin direban, ta faɗa rami.

“Fasinjojin wasu motocin da ke bayanta da mazauna yankin sun yi hanzarin kai ɗauki wurin domin taimakawa mutanen da ke cikin motar.
"Muna isa wurin muka tarar da wasu mutum biyu ba su motsi, wasu kuma da raunuka masu tsanani, sai muka kira ‘yan sanda da jami’an hukumar FRSC,” in ji shaidan.

FRSC ta faɗi mutanen da suka mutu

Da take tabbatar da faruwar lamarin, kakakin hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen Osun, Agnes Ogungbemi, ta ce mutane biyu, maza, sun mutu a hadarin, yayin da 15 suka jikkata.

Kara karanta wannan

Kisan sarkin Adara: Kotu ta samu El Rufa'i da laifi, an ci tarar shi N900m

“Rahotannin da muka samu sun ce direban ya kwanta barci sau biyu kafin su isa wurin da hadarin ya faru.
"Da suka wuce Osogbo, an ce barci ya ɗauke direban a karon farko suna cikin tafiya. Daga bisani, da suka kai yankin ‘Surprise Hotel’ a Gbongan, sai barcin ya sake kwace masa.
"Hakan ya sa motar ta ketare hanya, ta fada cikin rami tare da kifewa, lamarin da ya jefar da fasinjoji da dabbobi gefe guda,” in ji ta.
Jami'an FRSC.
Hukumar FRSC ta ce mutum 2 sun mutu a hatsarin, wasu 15 sun samu raunuka Hoto: @FRSC
Source: Facebook

Ta kara da cewa an kai wasu daga cikin wadanda suka jikkata da daya daga cikin gawarwakin zuwa Asibitin Adeoye Medical Centre da ke Gbongan, Punch ta rahoto.

Sannan kuma an kai sauran 13 da wata gawa daya zuwa asibitin Ariremako Medical Centre, Gbongan, yayin da motar da ta yi hatsarin na hannun ƴan sanda.

Mota ta markaɗe mutane a jihar Gombe

A wani labarin, kun ji cewa wata babbar mota ta murƙushe mabiya addinin kirista da suka fito tattakin bikin ista a ƙaramar hukumar Billiri ta jihar Gombe.

Kara karanta wannan

NEMA: Yadda ɗan ƙunar baƙin wake ya kusa tada bam a barikin sojoji a Abuja

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Gombe ta tabbatar da mutuwar mutane biyar da kuma raunata wasu a hatsarin wanda ya faru da safe.

Bayan faruwar lamarin, wasu fusatattun matasa sun kone motar da ta markaɗe mutanen, suka fasa shaguna sannan suka nufi ofishin ‘yan sanda na Billiri.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262