Bayan Rufe Ofishin PDP, Wike Ya Fadi Babbar Matsalar da Yake Fuskanta a Abuja
- Nyesom Wike ya bayyana cewa babbar matsalarsa a Abuja ita ce mazauna birnin na kin biyan haraji duk da ana kokarin kawo ci gaba
- Ministan Abujan ya bayyana hakan lokacin da ya duba manyan ayyukan da Shugaba Bola Tinubu zai kaddamar da suka hada da AICC
- Wike ya ce yawancin masu kadarori a Abuja sun ki biyan haraji fiye da shekaru 30, kuma FCTA za ta tabbatar ta yi aikinta yadda ya dace
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa kin biyan haraji da mazauna Abuje ke yi, shi ne babbar matsalarsa a matsayin minista.
Wike ya bayyana hakan ne bayan da ya duba wasu ayyukan da ake kan kammalawa a birnin Abuja domin shirin bikin cikar Shugaba Bola Tinubu shekaru biyu a mulki.

Kara karanta wannan
"Ba ɗan ƙunar baƙin wake ba ne," Ministan Tinubu ya gano mutumin da ya tashi 'bam' a Abuja

Source: Facebook
Manyan ayyukan da Wike ya yi a Abuja
Daga cikin ayyukan da ya duba akwai cibiyar taro ta kasa (AICC), da kuma fadada titin Obafemi Awolowo (N5), daga Life Camp zuwa Ring Road III, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma, an duba gadoji da hanyoyin da aka kammala a NICON Junction, rukunin gidajen alkalai, da hanyar Wole Soyinka da aka kammala kwanan nan.
Ministan ya ce mutane na so su ga ingantattun abubuwan more rayuwa, amma ba sa damuwa da inda gwamnati ke samo kudin da ake gudanar da ayyuka da su.
Wike ya caccaki masu kin biyan haraji
Ya jaddada cewa Abuja ba ta daga cikin jihohin da ke samun kudin mai, don haka haraji ne babban tushen kudaden shiga da take dogara da su.
Ya soki wasu masu hannu da shunu da ke da gidaje a kasashen waje kuma suna biyan haraji a can, amma a gida suna kin bin doka da kin biyan haraji.
"A nan gida ba kowa ke son bin doka ba, saboda kowa na tunanin ba za a hukunta shi ba,"
- Inji ministan Abuja.
Wike ya kara da cewa:
"Na taba fada, cewa saboda ba a dauki mataki jiya ba, ba yana nufin ba za a dauka gobe ba, kowace gwamnati da na ta tsarin"
FCTA za ta kara harajin kasa a Abuja
Ya jaddada cewa dole ne kowa ya taka rawa wajen tallafa wa gwamnati domin samun kayayyakin more rayuwa da ake bukata a babban birnin kasar.
Ya bayyana cewa yawancin masu gidaje da filaye a Abuja ba su biya harajin kasa na fiye da shekaru 30 ba, kuma ba a kara kudin ba tsawon lokacin nan.
Sai dai ya ce gwamnatin birnin tarayyar na duba yiwuwar kara yawan kudin domin daidaita harajin da halin tatta;in arziki da ake ciki a yanzu, kamar yadda kafar labaran NAN ta ruwaito.

Source: Twitter
Wike ya yi martani kan umarnin Tinubu
Dangane da wa’adin mako biyu da Shugaba Bola Tinubu ya bayar ga wadanda ake bi bashi, Wike ya ce ba wani barazana ko shisshigi da zai hana gwamnati daukar matakin da ya dace.
“Kar kowa ya yi zaton barazana za ta hana mu aiki. Za mu yi abin da ya dace, domin wannan shugabanci ne, hakkinmu ne yin abin da ya dace."
- Nyesom Wike.
Wike ya jaddada cewa duk wanda ya ki biyan kudin harajin fili, gida, shago ko wata kadararsa, to FCTA za ta kwace kadarorin, kuma ba yadda mutum zai yi.
Har yanzu FCTA ba ta bude ofishin PDP ba
A wani labarin, mun ruwaito cewa, duk da umarnin shugaba Bola Tinubu na bude wuraren da aka rufe, FCTA ta ki bude hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Wuse Zone 5, Abuja.
Wasu daga cikin ma’aikatan jam’iyyar sun nuna damuwa, inda wani ya ce akwai wani dalili da aka ɓoye da ya sa aka ƙi buɗe ofishin har yanzu.
Mukaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana matakin FCTA a matsayin cin mutunci ga dimokuraɗiyya, yana mai cewa jam’iyyar ba za ta yarda da hakan ba.
Asali: Legit.ng

