Ma'aikatan Wike Sun Bijire wa Umarnin Shugaba Tinubu, Sun Ki Bude Hedikwatar PDP
- Duk da umarnin Shugaba Bola Tinubu na bude wuraren da aka rufe, FCTA ta ki bude hedikwatar PDP da ke Wuse Zone 5, Abuja
- Wasu ma’aikatan PDP sun bayyana damuwa kan lamarin, inda wani ya yi zargin cewa akwai wata boyayyar kan kin bude ofishin
- Umar Damagum ya bayyana matakin FCTA a matsayin cin mutunci ga dimokuraɗiyya, yana mai cewa PDP ba za ta lamunci haka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Har yanzu, ma'aikatan hukumar kula da birnin tarayya (FCTA) ba su bude hedikwatar jam'iyyar PDP da suka rufe a ranar Litinin ba.
FCTA ta ki bude hedikwatar PDP duk da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarni na bude inda aka rufe saboda rashin biyan harajin filaye.

Source: Twitter
Bola Tinubu ya ba da umarnin bude ofishin PDP
A ranar Litinin ne ma’aikatan FCTA suka rufe kadarori da dama, lamarin da ya janyo suka daga sassa daban-daban, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai daga baya, Shugaba Tinubu ya sa baki tare da bayar da umarni na a bude wuraren da aka rufe, yayin da ya umarci wadanda ake bi bashi, su biya kafin wa’adin kwanaki 14.
Ya kuma shawarci duk masu filaye da su tabbatar da daidaita takardunsu kafin wa’adin ya cika domin gujewa irin matakin da FCTA ta dauka.
Har yanzu FCTA ba ta bude ofishin PDP ba
Amma a ziyarar da wakilin jaridar ya kai hedikwatar PDP da ke Wuse Zone 5, Abuja, da misalin karfe 10:15 na safiyar Laraba, an tarar har yanzu kofar na a kulle, kuma takardar da FCTA ta makala na rufe wurin na manne a jikin ƙofar.
An tarar da wasu ma’aikatan hedikwatar jam’iyyar a zazzaune a wajen ƙofar, yayin da wasu ke yawo a wurin suna nuna damuwa kan halin da ake ciki.
Wani ma’aikacin jam’iyyar da ya yi magana da manema labarai, ya bayyana cewa yana zargin akwai wani umarni na boye da ya hana bude ofishin PDP.
Ma'aikacin ya ce:
“Na ga yadda jami’an FCTA suka bude ofisoshin FIRS, Otal din Ibro, da NAPTIP. Amma da suka iso PDP, sai kawai suka juya motarsu suka tafi.
“Na bi su har ofishinsu na kasa da kasa, amma daraktan kula da filaye ya ce suna jiran umarni daga AGIS kafin su bude hedikwatar PDP.”

Source: Twitter
Martanin da PDP ta yi bayan rufe hedikwatarta
Bayan an rufe ginin a ranar Litinin, mukaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana matakin FCTA a matsayin “rashin sanin ya kamata” daga gwamnatin tarayya.
“Wannan babban rashin sanin ya kamata ne, kuma ko da za su kama mu baki ɗaya, mu a shirya muke,” inji Damagum.
Mun ruwaito cewa Damagum ya ƙara da cewa PDP ba za ta lamunci irin wannan abu da ya ce yana barazana ga dimokuraɗiyya ba.
“Wannan yunkuri ne na lalata dimokuraɗiyya. Ba za mu yarda da hakan ba, kuma muna shirye mu kare kanmu."
- Umar Damagum.
PDP ta gudanar da taro bayan rufe ofishinta
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam'iyyar PDP ta gudanar da babban taronta na musamman duk da cewa ma’aikatan FCTA karkashin Nyesom Wike sun rufe hedikwatarta a Abuja.
A farko, an fara gudanar da zaman ne a gidan gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, da ke Abuja, domin tattauna makomar jam’iyyar PDP a fadin ƙasa.
Daga baya, aka mayar da wurin taron zuwa Legacy House, daya daga cikin gine-ginen PDP, inda manyan jiga-jigan jam’iyyar suka halarci taron a ranar Talata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


