Duk da Wike Ya Rufe Ofishin Jam'iyyarsa, PDP Ta Gudanar da Babban Taronta a Abuja

Duk da Wike Ya Rufe Ofishin Jam'iyyarsa, PDP Ta Gudanar da Babban Taronta a Abuja

  • Garkame sakatariyar PDP da hukumomin Abuja a karkashin Nyesom Wike bai hana jam'iyyar gudanar da babban taronta ba
  • Da fari, an fara gudanar da taron a gidan gwamnan Bauchi, AbdulKadir Bala Mohammed dake Abuja domin duba makomar PDP
  • Amma daga bisani an dauke taron zuwa sakatariyar PDP na legacy house, inda manyan baki ke ci gaba da sauka don halartar taron

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Babbar jam’iyyar adawa PDP ta fara gudanar da taron babban taronta na kasa a gidan Gwamnan Bauchi da ke Abuja, a babban birnin tarayya.

Taron da aka yi a ranar Talata ya biyo bayan dage taron ranar Litinin, bayan jam’iyyar ta kammala batutuwan da ke cikin jadawalin taronta, ciki har da na babban taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC).

Kara karanta wannan

Hasashen El Rufai ya tabbata, SDP mai kokarin kwace mulki ta shiga Matsala

Taron PDP
Rufe sakatariyar PDP bai hana babban taronta na kasa ba Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

A cikin wata sanarwa da PDP ta wallafa a shafinta na X, ta ce bayan wannan taron, za a ci gaba da babban taron majalisar zartawarwarta.

Jam’iyyar ta fara shirin gudanar da taron da misalin karfe 12.00 na rana, amma daga bisani aka daga shi zuwa karfe 2:00 na rana.

PDP ta dawo gudanar da taronta a sakatariya

Channels Television ta ruwaito cewa PDP ta koma gudanar da taronta a wani bangare na sakatariyarta, wato Legacy House, inda ake ci gaba da tattauna muhimman batutuwan da suka hana a kammala taron a baya.

A cewar jam'iyyar PDP, babban burin taron NEC shi ne tattauna matsalolin da ke damun jam’iyyar da kuma dabarun da za su taimaka wajen shirin jam’iyyar a harkokin siyasa da ke tafe.

Taron NEC na daya daga cikin mafi girma wajen yanke shawara a jam’iyyar PDP, kuma yana kunshe da shugaban jam’iyyar na kasa da sauran 'yan kwamitin zartarwata.

Kara karanta wannan

Hadakar adawa: Atiku, Obi sun baza koma, an gana da 'yan siyasar Arewa

Jam'iyya
Manyan jam'iyyar PDP na ci gaba da sauka a babban taronta a Abuja Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Sauran sun hada da gwamnonin jihohi, da tsofaffin shugabannin kasa da mataimakan shugabannin kasa da kuma shugaba da sakataren kwamitin amintattu na jam’iyyar (BoT).

Sai kuma manyan ‘yan majalisar dokokin tarayya, shugabannin PDP a jihohi, tsofaffin gwamnoni da kuma wadanda suka assasa jam’iyyar.

Jam'yyar PDP ta caccaki Ministan Abuja

A wani lamari kuma, PDP ta bayyana rashin jin dadinta kan matakin Hukumar Raya Birnin Tarayya (FCTDA) na rufe sakatariyar ta kasa da ke Wadata Plaza a ranar Litinin.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron jam'iyyar, shugaban riko na PDP, Umar Damagum, ya bayyana wannan mataki a matsayin rashin gaskiya.

Ya kara ewa matakin tsantsar rashin iya shugabanci ne, inda ya sha alwashin cewa jam’iyyar za ta kalubalanci wannan mataki.

A ranar Litinin ne jami’an FCTA suka rufe Wadata Plaza, gine-ginen da ke dauke da sakatariyar PDP ta kasa a Abuja, bisa zargin rashin biyan kudin haya da kudin mallakar fili.

Kara karanta wannan

Yadda mata suka karbi haramta bikin 'kauyawa day' a Jihar Kano

An zargi gwamnan Bauchi da haddasa rikicin PDP

A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Binuwai kuma Sanata a majalisar tarayya, Gabriel Suswam, ya bayyana wasu manyan PDP biyu da cewa su ne ke haddasa masu rikici.

Ya ce Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi da shugaban rikon ƙwarya na jam’iyyar PDP, Ambasada Umar Damagum, su ne manyan matsalolin da ke janyo rikici a cikin jam’iyyar.

A cewar Suswam, ba daidai ba ne a dinga dora laifi kacokan kan tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike, dangane da matsalolin da ke ci gaba da kunno kai cikin jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng