Ma'aikata Za Su Warwasa, Gwamnatin Tinubu Ta Fara Tura Kuɗi Asusun Ƴan Najeriya
- Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta fara cika alkawarin karin albashin rage raɗaɗi ga ma'aikata bayan tsawon watanni suna jira
- Ofishin Akanta Janar na Ƙasa (OAGF) ya tabbatar da cewa ma'aikata sun fara ganin sakon shigar kudi a asusun bankunansu
- Tun farko an yi wa ma'aikatan alƙawarin karin N35,000 na tsawon watanni biyar amma sai yanzu gwamnati ta fara biyan kudin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta fara biyan bashin ƙarin albashi na ₦35,000 ga ma'aikata kamar yadda ta yi alƙawari.
Tun farko gwamnatin Najeriya ta yi alƙawarin karawa kowane ma'aikacinta N35,000 a albashinsa na wata-wata har tsawon watanni biyar, jimulla N175,00.

Source: Twitter
The Nation ta tattaro cewa gwamnatin ta yi wannan ƙarin albashi ne domin rage wa ma'aikatan raɗaɗin ƙuncin rayuwar da suka shiga bayan cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan
Kudin mazaɓa: Tinubu ya ba kowane ɗan Majalisar Tarayya Naira biliyan 1? Bayanai sun fito
Gwamnatin Tinubu ta fara cika alƙawarin N35,000
Watanni bayan gwamnati ta yi alƙawarin ƙarin, a yanzu an fara tura wa ma'aikata kudin kamar yadda wata sanarwa daga ofishin Akanta Janar ta tabbatar.
Sanarwar, wacce aka fitar yau Litinin a Abuja, tana ɗauke da sa hannun Daraktan Hulɗa da Jama'a na ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF).
A cewar sanarwar, ma’aikatan gwamnatin tarayya da dama sun riga sun karbi rabin waɗannan kudi, sauran da ba su karɓa ba za su ga saƙon kudinsu nan ba da jimawa ba.
An cire biyan kudin rage raɗadi a kasafin 2025?
OAGF ya kuma mayar da martani kan rahotannin da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai cewa an cire wannan ƙarin albashi daga kasafin kuɗin shekarar 2025.
Ofishin ya bayyana cewa, babu lokacin da aka ji Akanta Janar na Ƙasa, Mr. Babatunde Ogunjimi, ya bayyana hakan.
“Babu wani taron manema labarai da Akanta Janar ya kira dangane da batun ƙarin albashin.
“Duk wani rahoto da ake danganta masa cewa an cire ₦35,000 daga kasafin kuɗi na 2025 ƙarya ne," in ji sanarwar.

Source: Twitter
Dalilin kara wa ma'aikata N175,000
Ofishin ya ƙara da cewa, duk abin da ya rage na bashin ƙarin albashin za a biya shi kamar yadda gwamnati ta tabbatar wa da ƙungiyoyin ƙwadago da ma’aikatan gwamnati.
An ƙirƙiri wannan ƙarin albashi ne a matsayin wani matakin tallafi daga gwamnatin tarayya don rage wa ma’aikata raɗaɗin cire tallafin fetur da sauran sauye-sauyen tattalin arziki.
Fara biyan bashin ya biyo bayan dogon jira matsin lamba daga ƙungiyoyin ƙwadago, waɗanda suka dage kan cika wannan alkawari.
Wani jami'in hukumar shige da fice, Saifullahi Lawal ya tabbatarwa Legit Hausa cewa an fara tura masu waɗannan kudi amma na wata guda.
Ya buƙaci gwamnati ta taimaka ta biya duka na watanni shida domin zai taimaka masu wajen shagulgulan babbar sallah.
Saifullahi ya ce:
"Eh an fara biya amma mun yi tsammanin duka za su haɗa su tura mana saboda tsawon lokacin da aka ɗauka, ni dai na ga na wata ɗaya N35,000."

Kara karanta wannan
Malamin addini ya fito karara ya gayawa Tinubu abin da zai hana shi tazarce a 2207
Ma'aikata sun kewaye ma'aikatar kudi a Abuja
A wani labarin, kun ji cewa wasu ma’aikatan hukumar kula da harkokin nukiliya ta Najeriya sun mamaye hedikwatar ma’aikatar kudi ta tarayya da ke Abuja.
Ma'aikatan sun rufe hedikwatar, wacce ke dauke da ofishin ministan kudi , saboda rashin biyan bashin alawus da sauran hakkokinsu na albashi.
Ma'aikatan sun zargi ministan kudi, Wale Edun, da hana su hakkokin da doka ta tanada duk da roƙon da suka yi sau da dama.
Asali: Legit.ng
