FCTA Ta Tayar da Ƙura a Abuja, Manyan Jiga Jigai Sun Tunkari Tinubu a Aso Villa

FCTA Ta Tayar da Ƙura a Abuja, Manyan Jiga Jigai Sun Tunkari Tinubu a Aso Villa

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugaban hukumar tara haraji ta ƙasa watau FIRS, Zacch Adedeji a fadarsa da ke Abuja
  • Wannan ganawa na zuwa ne bayan jami'an hukumar gudanarwar Abuja (FCTA) sun sa kwaɗo, sun rufe ofishin FIRS da ke Zone 5
  • Bayan shugaban FIRS, Bola Tinubu ya gana da ministan ma'adanai, Dele Alake da ministan kasafin kudi, Atiku Abubakar Bagudu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Litinin ya gudanar da taruka masu muhimmanci a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja

Daga cikin waɗannan taruka, Bola Tinubu ya karɓi bakuncin shugaban Hukumar Tara Haraji ta Ƙasa (FIRS), Zacch Adedeji.

Bola Tinubu da Zacch Adedeji.
Shugabam FIRS ya gana da Bola Tinubu bayan FCTA ta garkame ofishin hukumar a Abuja Hoto: @FIRSNIGERIA
Source: Twitter

Hukumar FCTA ta tayar da ƙura a Abuja

Wannan ganawar ta biyo bayan matakin da Ma’aikatar Birnin Tarayya (FCTA) ta ɗauka na kulle ofishin FIRS da ke yankin Zone 5 a Abuja, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Abuja ta ɗauki zafi, jami'an gwamnati sun kusa ba hammata iska a wurin rufe ofishin FIRS

Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa FCTA ta rufe ofishin FIRS na Abuja ne bisa zargin rashin biyan harajin kasa na tsawon shekaru 25.

An tattaro cewa an ɗan yi hatsaniya tsakanin jami'an tsaron da ke gadin FIRS da jami'an FCTA kafin daga bisani aka ba su damar garkame ofishin da kwaɗo.

Meyasa FCTA ta rufe wurare a Abuja?

Da safiyar Litinin, 26 ga watan Mayu, jami’an FCTA suka fara kulle wasu wurare a babban birnin ƙasar, ciki har da ofishin FIRS, reshen bankin Access a kasuwar Wuse, da Gidan Man Total.

Hukumar gudanarwar Abuja watau FCTA ta nanata cewa ta ɗauki wannan mataki ne sabida masu kadarorin sun gaza biyan kuɗin haraji na shekaru 30.

Sai dai hukumar FIRS ta soki matakin FCTA na kulle ofishinta, tana mai cewa zargin ana binta bashin haraji ba gaskiya ba ne.

FIRS ta fusata da rufe ofishinta a Abuja

Kara karanta wannan

"Tinubu ya dage sai an magance matsalar tsaro a 2025," Badaru ya faɗi halin da ake ciki

Aderonke Atoyebi, mai taimakawa shugaban FIRS kan harkokin watsa labarai, ya ce hukumar ta biya dukkan kuɗin haya har zuwa shekarar 2023, ya kuma tabbatar da cewa rasiɗan biyan kudin suna nan.

Hukumar FIRS ta bayyana matakin da FCTA ta ɗauka a matsayin “na ƙiyayya” da kuma “rashin kwarewa,” wanda hakan ya haifar da sabani tsakanin hukumomin biyu.

Zacch Adedeji.
Shugaba Tinubu ya gana da ministoci 2 a Abuja Hoto: @FIRSNIGERIA
Source: UGC

Bola Tinubu ya gana da ƙusoshin gwamnati

Shugaba Tinubu ya kuma gana da Ministan Harkokin Ma’adanai, Dele Alake ministan kasafin kudi da harkokin ci gaban ƙasa, Abubakar Atiku Bagudu.

Ana ganin ganawar Bola Tinubu da shugaban FIRS ba zai rasa nasaba da rufe ofishin hukumar da jami'an FCTA suka yi ba, kamar yadda Punch ta rahoto.

Shugaba Tinubu ya naɗa Shema a muƙami

A wani rahoton, kun ji cewa Mai Girma Tinubu ya nada tsohon gwamnan Katsina, Ibrahim Shehu Shema a muƙami a gwamnatinsa.

Shugaban ƙasar ya nada Shema a matsayin sabon shugaban majalisar da ke sa ido a kan ayyukan hukumar FCDA.

A cewar wata sanarwa daga fadar shugaban kasa, Tinubu ya nuna kwarin gwiwarsa kan Shema, yana cewa yana da kwarewa wajen mulki da ci gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262