Ko Me Ya Yi Zafi?: Gwamna Ya Ɗauki Mataki mai Tsauri, Ya Kori Kwamishinan Shari'a

Ko Me Ya Yi Zafi?: Gwamna Ya Ɗauki Mataki mai Tsauri, Ya Kori Kwamishinan Shari'a

  • Gwamnan Imo kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC mai mulki, Hope Uzodinma ya sallami Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na jihar
  • Kwamishinan yaɗa labarai da dabaru na jihar Imo, Cif Declan Emelumba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Litinin, 26 ga watan Mayu
  • Sanarwar ba ta faɗi dalilin da ya sa gwamnan ya kori kwamishinan ba amma wata majiya daga gidan gwamnati ta ce Uzodinma na da iko naɗawa ko saukewa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Imo - Gwamnan Imo, Sanata Hope Uzodimma, ya kori Kwamishinan Shari’a kuma Antoni Janar na jihar, Barista Cyprian Akaolisa, daga mukaminsa a yau Litinin, 26 ga watan Yuni.

An tabbatar da sallamar kwamishinan ne a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da dabaru na jihar Imo, Cif Declan Emelumba ya fitar yau Litinin da tsakar rana.

Kara karanta wannan

China ta hango tarin arziki a Najeriya, ta fara gina manyan kamfanoni 2 a Arewa

Hope Uzodinma.
Gwamna Uzodimma ya sauke kwamishinan shari'a na jihar Imo, Bar. Cyprian Akaolisa Hoto: Hope Uzodinma
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta tattaro cewa sanarwar ba ta yi bayanin dalilin da ya sa Mai girma gwamna ya tsige Barista Akaolisa daga mukaminsa ba.

Gwamna Uzodinma ya umarci kwamishina ya bar ofis

Sai dai Gwamna Uzodinma ya umarci tsohon kwamishinan da ya miƙa duka kayayyaki da kadororin gwamnati da ke hannunsa ga babban sakataren ma'aikstar shari'a.

Bugu da ƙari, sanarwar ta bayyana cewa wannan mataki zai fara aiki ne nan take watau daga yau Litinin, 26 ga watan Mayu, 2027.

Sanarwar ta ce:

“Gwamnan Jihar Imo, Mai Girma Sanata Hope Uzodimma, CON, ya amince da sauke Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Imo, Barista C.O.C Akaolisa, daga mukaminsa nan take.
“An umurce shi da ya mika duk kadarorin gwamnati da ke hannunsa ga lauyan gwamnatin Imo da babban sakataren ma'aikatar shari'a, sannan ya bar ofis ba tare da ɓata lokaci ba."

Meyasa gwamnan ya ɗauki wannan mataki?

Kara karanta wannan

"Ba zan lamunta ba," Gwamna ya dakatar da mai martaba Sarki, ya umarci a kama ƴaƴansa 2

Barista C.O.C Akaolisa dai ya kasance na kusa sosai ga Gwamna Uzodimma, shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar APC.

Rahotanni sun nuna cewa Uzodinma ya naɗa Akaopisa a matsayin ɗan takarar mataimaki na rikon ƙwarya gabannin zaɓen Imo na 2019 saboda kusancinsa da shi.

Gwamna Uzodinma.
Gwamnatin Imo ta umarci tsohon kwamishinan shari'a ya ajiye kayayyakin da ke hannunsa Hoto: Hope Uzodinma
Source: Facebook

Kawo yanzu, babu wani bayani daga bangaren gwamnati ko daga Akaolisa kan musabbabin tsige shi daga muƙami.

Sai dai wata majiya daga fadar gwamnatin jihar Imo ta bayyana cewa mai girma gwamna na da cikakken ikon saukewa ko naɗa mutum a mukami, rahoton The Nation.

Gwamnan Imo ya yi fatali da haɗakar Atiku

A wani labarin, mun kawo maku rahoton cewa Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya ce yunƙurin haɗaka da ƴan adawa ke yi a Najeriya ba zai kai ga nasara ba.

Gwamnan ya jaddada cewa jam'iyyar APC na nan da karfinta kuma ba ta damu da shirye-shiryen da ƴan adawa ke yi ba domin a ganinsa ba za su iya kayar da Tinubu ba.

Sanata Uzodinma ya ce ƴan Najeriya ne za su yanke hukunci a ranar zaɓe amma kafin hakan, ya tunawa ƴan adawa cewa gwamnatin Tinubu ja da shekaru biyu nan gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262