"Sabon Man Fetur ne": Gwamna Ya Haska Ma'adanin da Najeriya Za Ta Amfana da Shi
- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya taɓo batun ma'adanin lithium da ke jibge a wasu sassan jihar
- Abdullahi Sule ya bayyana cewa Najeriya za ta amfana sosai da ma'adanin na lithium idan aka yi abin da ya dace
- Gwamnan ya buƙaci a cire siyasa a harkar domin masu zuba hannun jari damar shigowa su bunƙasa haƙo ma'adanin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce Najeriya za ta amfana matuƙa daga ma’adanin lithium da ke jihar.
Gwamna Sule ya bayyana cewa za a amfana ne muddin ba a saka siyasa cikin harkar haƙar ma’adanin ba.

Source: Facebook
Gwamna Sule ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da tashar Channels TV a ranar Lahadi, 24 ga watan Mayun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An fara rububin ma'adanin lithium
Lithium wani muhimmin ma’adani ne da ake nema sosai saboda amfaninsa wajen ƙera motoci masu amfani da lantarki da kuma yin batura.
Jihar Nasarawa na da ma’adanin lithium, musamman a ƙaramar hukumar Endo.
A ƴan kwanakin nan, masu zuba hannun jari suna nuna sha’awa sosai kan ma’adanan lithium da ke jihar domin samar da motoci masu amfani da lantarki.
Me Gwamna Sule ya ce kan ma'adanin lithium?
A yayin tattaunawar, Gwamna Sule ya ce dole ne Najeriya ta yi amfani da lithium da ke jihar Nasarawa ta hanyar kallonsa a matsayin wata harkar kasuwanci.
Gwamnan ya ce dole ne Najeriya ta taka rawar gani wajen sarrafa lithium da kuma ƙera batirin motoci masu amfani da lantarki a Yammacin Afirika.

Source: Facebook
“Yanzu ne lokacin da za mu amfana da wannan ma'adanin na lithium, mu taka rawar gani kuma mu zama jagora a Afirika, musamman a Yammacin nahiyar."
“Mu cire siyasa daga cikin wannan lamari. Masu zuba jari za su kai kamfanoninsu ne inda za su samu kasuwa da riba mafi yawa."

Kara karanta wannan
Zulum ya yi karatun ta natsu, ya fadi yadda za a kawo karshen ta'addanci a wata 6
“Nasarawa na kusa da Abuja. Ɗaya daga cikin manyan masu sayen motoci masu amfani da lantarki shi ne gwamnati. A ina za ka fi samun kamfani mai kyau? Wataƙila a Nasarawa."
“Ni na cire siyasa gaba ɗaya daga wannan al’amari. Harka ce ta kasuwanci tsantsa. Da zarar mun cire siyasa daga ciki, muka bar masu zuba jari su yanke hukunci cikin gaskiya, to ina ganin Najeriya za ta ci gajiya sosai."
“Wannan wani sabon man fetur ne da ke zuwa. Haka Allah ya yi wa Najeriya ni’ima ta musamman, kuma wannan ita ce hanyar da ya kamata a bi."
- Gwamna Abdullahi Sule
Gwamna Sule ya faɗi nadamarsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan shekara shida da ya yi a mulki.
Gwamnan ya bayyana cewa duk da ya samu nasarori a mulkinsa, akwai ayyukan da ke sanya shi cizon yatsa saboda rashin kammala su.
Abdullahi Sule ya nuna cewa da a ce zai samu yadda yake so, da waɗannan muhimman ayyukan sun kammala kafin ya bar mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
