Rikici Ya Barke a Tsakanin Matasa da Yan Sanda a Kano, Ana Fargabar Kashe DPO

Rikici Ya Barke a Tsakanin Matasa da Yan Sanda a Kano, Ana Fargabar Kashe DPO

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da barkewar rikici a karamar hukumar Rano, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba
  • Wani matashi da aka kama ya rasu bayan duka da ake zargin DPO ya masa, lamarin da ya jawo jama'a suka nufi ofishin yan sanda don daukar fansa
  • Jama'a sun zargi baturen yan sanda, Baba Ali ya harbe mutane biyu, lamarin da ya harzuka jama'a suka kone ofishin yan sandan da cinna masa wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewa an samu barkewar rikici a karamar hukumar Rano.

Lamarin ya tayar da hankalin mazauna yankin, wadanda ke ganin an hallaka baturen ‘yan sandan yankin, Baba Ali.

Kara karanta wannan

Kano: Fusatattun matasa sun cinnawa ofishin ƴan sanda wuta, an ji abin da ya faru

Yan sanda
Matasa sun kone ofishin yan sanda a Kano Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da rikicin a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa ana zurfafa bincike domin gano ainihin abin da ya faru a karamar hukumar.

Dalilin barkewar rikici a Kano

Wasu daga cikin mazauna garin da suka zanta da majiyar Legit ta wayar tarho a Kano sun bayyana dalilin rikicin.

Ɗaya daga cikin mazauna garin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce:

“Jiya akwai wani bawan Allah yana yawo a kan babur, sai aka kama shi aka kai shi wajen DPO, sai ya dake shi. Da ya ga dukan da ya yi masa, dukkan alamu ya jikkata sosai.”
“Sai ya kai shi asibiti, daga bisani sai aka ce ya mutu da safe. Jama’ar gari sai suka tafi ofishin ‘yan sanda suna son su ɗauki fansa. Sai ‘yan sanda suka fara harba barkonon tsohuwa. Jama’a kuwa sai suka tayar da wuta. DPO kuma sai ya ɗauko bindiga ya harbe mutane biyu. Su kuma jama’a sai suka kona shi.”

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta shirya yanke hukunci a kan matashin da ya babbake masallata 25

Kano: An zargi DPO da kisan jama'a

Wasu daga cikin mazauna garin sun zargi baturen ‘yan sandan, Baba Ali, da kashe aƙalla mutane goma a garin.

Kiyawa
Yan sandan Kano sun tabbatar da hargitsi a Rano Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: UGC

Duk da cewa sun amince a ɗauki muryarsu, matashin da ya zanta da majiyar Legit ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce:

“Mu mun ji daɗi, ya mutu za mu ce Allah Ya ƙara masa nauyin ƙasa. Wannan mutumin, su kansu yaransa ba su ji daɗinsa ba. Ya kashe mutane fiye da goma, nan da nan sai ya sa harbi ko ya sa kulki yana dirkar yara.”

Barnar 'yan daba a Kano

A cikin shekarun baya-bayan nan, matsalar ‘yan daba a jihar Kano, musamman a birane ta zama babban kalubale ga zaman lafiya da tsaron al’umma.

Wadannan ‘yan daba na dada samun karfi ta hanyar amfani da sanya tsoro a zuktana jama'a da barazana wajen muzanta al’umma.

Galibi matasa ne suke shiga kungiyoyin nan, kuma sukan dauki makamai irin su adduna, takubba, da sanda, suna kai farmaki a kasuwanni, unguwanni, da ma wuraren bukukuwa.

Kara karanta wannan

Fulani makiyaya: An kashe rayuka, an kona gidaje a harin ramuwar gayya a Taraba

A wasu lokutan, wadannan ‘yan daba sukan yi amfani da rikice-rikice irin na siyasa ko rashin adalci daga hukumomi wajen kaddamar da tashe-tashen hankula, inda hakan ke haifar da karin rashin zaman lafiya.

A Rano da wasu yankuna na Kano, rahotanni da dama sun nuna yadda ‘yan daba ke hadin gwiwa da wasu bata-garin jami’an tsaro 'yan rashawa, wanda ke kara tsananta halin da jama’a ke ciki.

Wannan na nuna bukatar daukar tsauraran matakai don shawo kan wannan matsala, wanda a lokuta da dama gwamnatin ke cewa tana kokarinta.

'Yan sandan Kano sun hallaka dan daba

A baya, mun wallafa cewa jami’an ‘yan sanda a Kano sun kashe wani shahararren ɗan daba, Baba Beru, wanda ake zargi da fashi da makami da tayar da zaune tsaye a jihar.

Baba Beru ya rasa ransa ne a lokacin da aka yi artabu tsakaninsu da yan sanda yayin da ya yi yunƙurin kai hari kan jami’an tsaro a unguwar Gwammaja da ke birnin Kano.

Rahotanni sun ce Baba Beru, wanda aka dade ana bibiyarsa, ya fusata lokacin da ‘yan sanda suka yi ƙoƙarin kama shi, ya fito da wuƙa ya nufi jami’an da niyyar kai musu hari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng