Kwana Ya Kare: Yadda Wani Babban Malami Ya Rasu ana tsaka da Ruwan Sama a Jihar Neja
- Wani limamin cocin Katolika a Gulu, da ke ƙaramar hukumar Lapai ta jihar Neja ya mutu sakamakon ambliyar ruwa
- Rahoto ya nuna cewa malamin cocin tare da wata mata na cikin farar Hilux a lokacin da ruwa mai ƙarfi ya fara sauka, lamarin da ya haifar da ambaliya
- Rundunar ƴan sanda reshen jihar Neja ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an ciro gawarwakin waɗanda ibtila'in ya faru da su
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger - Ambaliya da ta faru sakamakon mamakon ruwa sama ta yi ajalin wani limamin cocin Katolika, Rabaran James Omeh, da wata a jihar Neja.
Limamin wanda ke jagorantar cocin St. Anthony’s Catholic Church da ke Gulu a ƙaramar hukumar Lapai ta jihar Neja, da matar mai suna, Charity John sun rasu sakamakon ibtila'in.

Source: Original
Daily Trust ta tattaro cewa, limamin cocin, wanda yana cikin jagororin ƙungiyar kiristoci (CAN) a Lapai, na kan hanya ne lokacin da ambaliyar ta yi awon gaba da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ruwa ya tafi da motar malami a Neja
An ruwaito cewa malamin tare da natar na cikin wata motar Hilux fara lokacin da ruwa ya janye motarsu a kusa da wani kogi a kan titin Lapai-Gulu.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa Fr. Omeh na kokarin zuwa Gulu ne da misalin ƙarfe 12:00 na rana lokacin da ya gano cewa gadar Lapai-Gulu da ke kusa da kauyen Duma ta ruguje.
A kokarinsa na juyawa ya koma Duma, sai ruwan sama mai ƙarfi ya ɓarke kuma ya haifar da ambaliya da ta kai ga kwasar motar da suke ciki.
Mutane sun cire gawar limamin coci
“Motar Hilux ɗin da yake tukawa ta nutse a ruwan ambaliya, ta fada cikin wani rami mai zurfi.
"Daga baya, mazauna yankin tare da taimakon Sarkin Ruwa suka gano motar da gawarwakin Rabaran Fr. Omeh da matar,” in ji wani ganau.
Mutane da dama sun nuna damuwa kan lalacewar titin Lapai-Gulu, wanda ke haɗa jihohin Neja da Kogi, sun buƙaci a gaggauta gyara titin don kare rayukan matafiya.

Source: Facebook
Hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da lamarin
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.
A rahoton AIT Online, kakakin ƴan sandan ya ce:
"A ranar 25 ga Mayu, 2025 da misalin ƙarfe 1:00 na rana, an samu labarin cewa Fr. James Omeh da Charity John na cikin farar mota Hilux a hanyar zuwa Gulu lokacin da ruwan sama mai ƙarfi ya yi awon gaba da su har suka nutse.
“’Yan sanda daga ofishin Lapai tare da taimakon al’umma sun ciro gawarwakin, kuma an mika su ga cocin domin jana’iza, sannan an tsamo motar daga cikin ruwa.
'Yan sanda sun kama dagaci a jihar Neja
A wani labarin, kun ji cewa ƴan sanda sun kama dagaci da wasu mutane 13 bisa zargin hannu a ayyukan ƴan bindiga a jihar Neja.
An tattaro cewa jami'an tsaro sun cafke waɗanda ake zargin ne a wani samame da suka kai yankin ƙaramar hukumar Mashegu.
Sauran waɗanda aka kama bayan basaraken, sun fito daga kauyuka daban-daban da ake zargin suna da alaka da ‘yan bindigan da ke addabar jama’a.
Asali: Legit.ng

