Kano: Kotu Ta Shirya Yanke Hukunci a kan Matashin da Ya Babbake Masallata 25

Kano: Kotu Ta Shirya Yanke Hukunci a kan Matashin da Ya Babbake Masallata 25

  • Babbar Kotun Shari’ar musulunci za ta ci gaba da shari'ar Shafi’u Abubakar Gadan, wanda ake zargi da kona masallata a Gezawa
  • Ana zargin matashin ya cinnawa masallaci wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 17 a wurin, sannan wasu suka rasu daga baya
  • Shafi’u ya amsa tuhumar kisan kai da jikkata jama’a, inda kotu ta ba da umarnin a tsare shi har zuwa lokacin yanke hukunci da za a zartar a yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – A yau Litinin, Babbar Kotu ta Shari’ar Musulunci da ke Kano za ta yanke hukunci a shari’ar da ake yi wa Shafiu Abubakar Gadan.

Ana zargin matashin da kona masallaci a lokacin sallar asuba a karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano, abin da ya jawo asarar rayuka da dama.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Yadda wani babban malami ya rasu ana tsaka da ruwan sama a jihar Neja

Jihar Kano
An shirya yanke hukunci a kan wanda ya kashe masallata a Kano Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daily Trust ta wallafa cewa wannan lamarin mai tayar da hankali ya faru ne a ranar 16 ga Mayu, 2024, inda mutane 17 suka mutu nan take.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashi ya hallaka masallata a garin Kano

Trust rediyo ta wallafa cewa karin wasu mutum takwas sun rasu daga bisani sakamakon raunin da suka samu a gobarar, wanda hakan ya kai adadin wadanda suka mutu zuwa 25.

A cewar rahoton, Shafiu na fuskantar tuhuma guda uku, daga ciki har da haddasa rauni mai tsanani da kuma kisan kai.

A baya, ya amsa laifi a zaman farko, wanda hakan ya sa alkalin da ke shari’ar, Khadi Dalhatu Huza’i Zakariya, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali har sai an yanke hukunci.

Gwamnatin Kano ta jajantawa iyalan masallata

Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Kano, Haruna Isah Dederi, ne ke jagorantar gabatar da kara bayan ya bayyana takaici a kan al'amarin.

Kara karanta wannan

Jerin wadanda ke goyon bayan Shugaba Bola Tinubu ya zarce a 2027

A baya, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyara ga wadanda suka jikkata a Asibitin Musamman na Murtala da ke Kano.

Gwamna
Gwamnan Kano ya yi takaicin kisan masallata Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Bayan ya bayyana alhini a kan batun, ya kuma tabbatar wa iyalan wadanda suka mutu cewa gwamnati za ta tabbatar da an yi adalci a wannan lamari.

Gwamnan ya bayyana cewa rikicin bai da nasaba da ta’addanci ko rikicin siyasa, illa dai rikicin cikin gida ne tsakanin ‘yan uwa da ya rikide zuwa tashin hankali.

Matashi ya amsa kisan masallata a Kano

A baya, mun wallafa cewa matashin nan da ake zargi da kisan wasu masallata a Kano, Shafiu Abubakar Gadan ya amsa laifinsa bayan an karanto masa tuhumomin kisan kai da jikkata jama'a.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a masallacin da ke garin Gadan, Larabar Abasawa a Kano, inda ake zargin matashin da watsa fetur a cikin masallacin, ya kunna wuta.

Lauyan gwamnati, Barista Salisu Tahir, ya bukaci kotu ta ba su dama su sabunta tuhumar da ake yi wa Shafi’u tare da saka sunayen dukkannin mutane 23 da suka mutu a yayin harin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng