Ibrahim Dahiru Bauchi da Tawagar Tijjaniyya Sun Yi wa Gwamna Radda Addu'oi a Katsina

Ibrahim Dahiru Bauchi da Tawagar Tijjaniyya Sun Yi wa Gwamna Radda Addu'oi a Katsina

  • An gudanar da taron addu’a na musamman a gidan gwamnatin jihar Katsina domin neman zaman lafiya da kawar da matsalar tsaro
  • Sheikh Ibrahim Ɗahiru Bauchi ne ya jagoranci addu’ar yayin ziyarar girmamawa da ya kai Katsina tare da mabiya darikar Tijjaniyya
  • Gwamnan Katsina ya yi godiya bisa wannan ziyara da addu’o’in da aka gudanar, yana mai yabawa da kokarin Darikar wajen zaman lafiya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - An gudanar da wani taron addu’o’i na musamman a gidan gwamnatin jihar Katsina domin neman rahamar Allah wajen kawo zaman lafiya da kawar da matsalar tsaro.

Sheikh Ibrahim Ɗahiru Usman Bauchi, ɗan fitaccen malamin darikar Tijjaniyya, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, ne ya jagoranci addu’ar.

Katsina
Ibrahim Dahiru Bauchi ya ziyarci Dikko Radda a Katsina. Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan taron addu'ar ne a cikin wani sako da mai magana dayawun gwamna Katsina, Ibrahim Kaulaha Mohammed ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaro a Katsina, an samu asarar rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Darikar Tijjaniyya sun ziyarci Katsina

Sheikh Ibrahim Ɗahiru Usman Bauchi tare da gagarumar tawaga da suka haɗa da dattawa, ‘yan uwa da mabiya Tijjaniyya sama da 50 ne suka gabatar da addu'ar.

Taron ya gudana ne a ƙarƙashin jagorancin mai bai wa gwamna shawara kan harkokin Darika, Malam Mahi Muhammad Bello.

Rahotanni sun nuna cewa an roƙi Allah da ya kawo zaman lafiya da haɗin kai a jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya.

An roƙawa mahaifiyar Dikko Radda gafara

Baya ga addu’o’in zaman lafiya da tsaro, Sheikh Ibrahim Ɗahiru Bauchi ya gabatar da addu’o’i na musamman domin roƙon rahamar Allah ga mahaifiyar gwamnan Katsina.

Legit ta rahoto cewa mahaifiyar gwamna Dikko Umaru Radda, Hajiya Safarau, ta rasu a kwanakin baya, kuma an birne ta Katsina.

Shehin malamin ya bayyana cewa wannan addu’a ta musamman na daga cikin kyautatawa da darikar Tijjaniyya ke yi ga jagororin al’umma, tare da fatan Allah ya jikan mamaciyar.

Kara karanta wannan

Hajjin bana: Malamai sun yi wa Bola Tinubu addu'a a birnin Madina

Radda
Dikko Radda ya yaba wa tawagar Darikar Tijjaniyya yayin da suka ziyarce shi. Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Ziyarar da kuma addu’ar sun kasance masu cike da tasiri, inda aka bayyana wannan lokaci a matsayin wanda ya kawo ƙarfafa guiwa da nuni da muhimmancin addu’a a rayuwar al’umma.

Dikko Radda ya nuna farin ciki da godiya

Gwamnan jihar Katsina ya karɓi bakuncin tawagar darikar cikin farin ciki, inda ya bayyana godiya bisa ziyarar da kuma addu’o’in da aka yi domin jihar da al’umarta.

Daga cikin manyan jami’an gwamnati da suka halarci taron akwai Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Katsina, Abdulkadir Mamman Nasir.

Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai, Alhaji Kabir Bature da mai bai wa gwamna shawara kan harkokin ƙungiyoyi, Aminu Ubale Funtua sun halarci zaman.

Malamai sun yi wa Tinubu addu'a a Madina

A wani rahoton, kun ji cewa tawagar malaman Musulumci da suke aiki tare da hukumar NAHCON ta yi taron addu'a a Madina.

Shugaban tawagar ya ce sun yi wa shugaba Bola Tinubu addu'ar samun nasara da rokon Allah ya yaye matsalolin Najeriya.

Limaman sun yaba da yadda hukumar NAHCON ta ke shirye shirye da jagorantar harkokin aikin Hajji a shekarar 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng