Babban Fasto a Arewacin Najeriya, Azzaman Ya Yi Bankwana da Duniya
- Al’ummar Kiristoci sun shiga jimami bayan rasuwar fitaccen Fasto, Ayuba Azzaman David, wanda ya rasu sakamakon hatsarin mota a ranar Asabar
- Fasto Mohammed Mohammed Bishara ne ya tabbatar da rasuwar a wani bidiyo da ya wallafa a Facebook, inda ya ce an yi babban rashi
- Bishara ya yabawa irin gudunmawar Azzaman wajen wa’azi, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikansa ya sa ya huta cikin rahama da salama
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Al'ummar Kiristoci sun tashi da jimami a yau Lahadi bayan rasuwar fitaccen Fasto a Arewacin Najeriya.
An tabbatar da mutuwar Fasto Ayuba Azzaman David a yau Lahadi 25 ga watan Mayun 2025 dalilin hatsarin mota.

Source: Facebook
An yi rashin Fasto a Arewacin Najeriya
Ɗan uwansa Fasto, Mohammed Mohammed Bishara Dole ne ya tabbatar da haka a wani bidiyo a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bishara ya nuna damuwa kan babban rashin da aka yi inda ya ce babu yadda aka iya saboda hukunci ne na Ubangiji.
Faston ya bayyana gudunmawar da Azzaman Azzaman ya bayar wurin wa'azi ga al'umma.
Matashin ya yi addu'ar Ubangiji ya jikansa ya sa ya huta su kuma in ta su ta zo ya sa su tafi a sa'a.
A cikin bidiyon, Bishara ya ce:
"Yan uwa masu bin Yesu barkanmu da yau kuma barkanmu da sake saduwa a wannan safiya na Lahadi 25 ga watan Mayun 2025.
"A wannan safiyar, zan iya cewa cikin bacin zuciya, mun tashi da mummunan labari.
"A cikin daren jiya, Ubangiji Allah ya karbi dan uwa na, abokin aiki na, Rabaran David Ayuba Azzaman wanda aka fi sani da Azzaman Azzaman.

Source: Facebook
Fasto Bishara ya yi jimamin mutuwar Azzaman
Fasto Bishara ya yi addu'ar Allah ya sa su mutu a kan hanyar da Azzaman ya bar duniya domin tsira a ranar lahira.
"Ya rasu a kan hanyarsa ta zuwa Makurdi a hatsarin mota, ya riga mu gidan gaskiya, mu na da yakinin yana da tare da Yesu Almasihu a cikin salama.
"Mu na da yakinin cewa lallai aikin da ya yi a duniya ba zai zama a banza ba, kuma mu na da yakinin cewa Ubangiji ya karbi bakuncinsa."
A ƙarshe, Bishara ya ce suna rokon Ubangiji ya yi musu ta'aziyya ya sa su mutu a irin wannan hanya.
Azzaman dai ya kasance Fasto da ya yi kaurin suna wurin muhawara da Musulmai kan fahimtar addini da ake samun sabani.
Legit Hausa ta tattauna da wani masoyin Azzaman
David Solomon da ke zaune a Gombe ya ce tabbas an yi rashin jajirtacce a Kiristanci.
Solomon ya ce Azzaman ya ba da rayuwarsa gaba daya domin fadakar da al'umma sanin Kiristanci.
Ya ce:
"Ba za mu manta da gudunmawar da bayar ba saboda ba shi da tsoro ko kadan."
Azzaman Azzaman ya caccaki Bola Tinubu
A baya , kun ji cewa malamin addini Fasto Ayuba Azzaman, ya yi magana kan rawar da ake zargin Oluremi Tinubu tana taka wa a wannan gwamnatin.
Babban Faston na cocin King Worship Chapel and Ministry ya ce Oluremi, uwargidan shugaban ƙasa, "ita ce ke juya akala" a gwamnatin nan mai ci.
Malamin ya yi iƙirarin cewa a kusa da watan Yuli 2023, ya samu "wahayi" inda ya lura da Oluremi "a tsakiyar" wani gagarumin aiki a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock.
Asali: Legit.ng


