Ganduje Ya ba Tinubu Satar Amsa Yadda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro a Najeriya

Ganduje Ya ba Tinubu Satar Amsa Yadda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro a Najeriya

  • Shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci gwamnati ta sauya dabarar tsaro ta hanyar mayar da dazuka sansanonin sojoji don dakile ‘yan ta’adda
  • Ganduje ya bayyana hakan ne a Yobe yayin ziyarar jaje bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai sansanin soja a Buni-Gari
  • Gwamna Mai Mala Buni ya yaba da ziyarar, ya ce za su hada kai da shugaban kasa wajen dawo da zaman lafiya a yankin Arewa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Damaturu, Yobe - Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana kan matsalar tsaro a Najeriya.

Abdullahi Ganduje a ranar Laraba, ya ce mayar da dazuka sansanonin sojoji zai hana ‘yan ta’adda mamaye su da inganta tsaro.

Ganduje ya shawarci Tinubu kan tsaro
Ganduje ya fadawa Tinubu hanyar dakile matsalar tsaro. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Shawarar da Ganduje ya ba Tinubu

Dr Abdullahi Ganduje, Shugaban APC na kasa, ya bayyana hakan ne a Damaturu yayin ziyarar jaje zuwa Yobe bayan harin da aka kai Buni-Gari, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

An fara kera makaman yaki a Najeriya, sufeton 'yan sanda ya ziyarci masana'antar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje, wanda ya jagoranci tawagar Kwamitin Gudanarwa na kasa na jam’iyyar, ya ce matsalar ta shafi kasa baki daya, tana bukatar gaggawa da hadin kai.

Ya ce harin da aka kai sansanin sojoji wata dabara ce don karkatar da hankalin gwamnati daga ayyukan cigaba zuwa martanin gaggawa.

Shugaban APC ya bukaci sauya dabarar tsaro ta kasa, yana mai cewa amfani da fasaha da na’urorin leken asiri a dazuka yana da matukar muhimmanci.

Ya ce:

“Dazuka da ke kare muhalli sun koma mafakar masu laifi. Dole ne mu ‘yanta su. A girke na’urori da sansanonin soja."
Ganduje ya ba Tinubu shawara kan matsalar tsaro
Shawarar da Ganduje ya ba Tinubu kan rashin tsaro. Hoto: All Progressives Congress.
Source: UGC

Ganduje ya jinjinawa Gwamna Mai Mala Buni

Ganduje, wanda ya kafa sansanin horas da sojoji a dajin Falgore a Kano, ya shawarci Yobe da su dauki irin wannan mataki.

Ya jinjinawa Gwamna Mai Mala Buni bisa nasarorin tsaro duk da kalubalen da ‘yan ta’adda ke haifarwa a jihar, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Boko Haram ta sauya salo, ta koma amfani da 'jirage' wajen kai hare hare Borno

Ya kara da cewa:

“Muna nan ne don yin jaje ga gwamnatin da mutanen Yobe bisa wannan mummunan hari da aka kai a Buni-Gari.

A nasa bangaren, Gwamna Buni ya gode wa Ganduje da tawagarsa bisa ziyarar, yana mai cewa hakan alamar shugabanci nagari ne.

“Ziyarar nan ba siyasa ba ce kawai, alamar kulawa ce. Harin Buni-Gari ya shafi kasa gaba daya.
“Wannan kira ne gare mu duka. Dole mu dauki mataki cikin gaggawa da hadin kai da kishin kasa."

- Cewar Gwamna Buni.

Ya goyi bayan kira da Ganduje ya yi na sauya dabarar yaki da ‘yan ta’adda, yana mai cewa matsalar ta yadu a sassa daban-daban.

Buni ya ce batun tsaro zai zama babban abu a taron Gwamnonin Arewa da za a yi a Kaduna a ranar 10 ga Mayun 2025.

Yan ta'adda sun kai hari sansanin sojoji

Kun ji cewa yan ƙungiyar ISWAP sun kai wani hari a sansanin sojoji da ke Buni-Gari a karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: An kai ruwa rana tsakanin gwamna da majalisa bayan dawowa hutu

Dakarun sojoji sun yi artabu da ƴan ta'addan na tsawon awanni bayan harin da suka kai musu da tsakar dare

Majiyoyi sun tabbatar da samun asarar rayuka daga ɓangaren dakarun sojoji da ƴan ta'addan ISWAP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.