Rikicin NANS: Atiku Ya Janye Kalaman da Ya Yi, Ya Nemi Afuwar Ɗan Shugaban Kasa, Seyi Tinubu

Rikicin NANS: Atiku Ya Janye Kalaman da Ya Yi, Ya Nemi Afuwar Ɗan Shugaban Kasa, Seyi Tinubu

  • Shugaban tsagin ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS), Atiku Abubakar Isah ya janye zarge-zargen da ya yi wa Seyi Tinubu
  • Atiku ya nemi ɗan shugaban ƙasar ya yi haƙuri da yafe masa, yana mai cewa duk abin da ya faɗa a baya ba gaskiya ba ne
  • Ya bayyana wanda ya masa barazanar kisa kuma ya tilasta masa faɗar karairayi kan ɗan shugaban ƙasa da ministan matasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Shugaban kungiyar daliban Najeriya (NANS), Kwamared Atiku Abubakar Isah, ya janye kalamai da zarge-zargen da ya yi wa ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu.

Atiku ya kuma roki Seyi Tinubu da ya yafe masa kuskuren da ya yi, yana mai cewa tilasta shi aka yi amma ba da son ransa ya yi hakan ba.

Seyi Tinubu da shugaban NANS.
Atiku Abubakar Isah ya janye kalaman da ya yi kan Seyi Tinubu Hoto: Seyi Tinubu, Atiku Abubakar Isah
Source: Facebook

Shugaban NANS ya nemi afuwar Seyi ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Laraba, 7 ga watan Mayu, 2025.

Kara karanta wannan

"Tinubu ba zai iya ba," Jigon APC ya cire tsoro, ya faɗi wanda ya dace da mulkin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane zarge-zargi Atiku ya yi wa Seyi Tinubu?

Ya bayyana cewa zarge-zargen da ya yi a wani faifen bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta kan Mr. Seyi Tinubu da Ministan Matasa da Wasanni, Ayodele Olawande, ba gaskiya ba ne.

A cikin bidiyon, Atiku Abubakar Isah ya ce an gayyace shi zuwa Legas inda aka masa tayin Naira miliyan 100 domin ya marawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu baya, amma ya ki amincewa da tayin.

Ya kara da cewa saboda kin amincewar tasa ne aka yi garkuwa da shi a ranar 15 ga Afrilu, inda ya ce aka cire masa kaya kuma aka yi masa duka, sannan aka tilasta masa sauka daga shugabancin NANS.

Shugaban 'yan tawaren NANS ya janye kalamansa

Sai dai a sanarwar da ya fitar yau Laraba, Atiku ya janye duk wadannan zarge-zargen, yana mai cewa duk abin da da ya fada tilasta masa aka yi.

Kara karanta wannan

Ndume ya dakata da sukar Tinubu, ya kwararo yabo ga shugaban kasa

Ya ce Ladoja Olusola, wanda ke da burin karbe shugabancin NANS ne ya masa barazanar kisa da tilasta masa faɗin kalaman ƙarya kan Seyi Tinubu.

Seyi da Atiku.
Shugaban NAN ya faɗi yadda aka mass barazanat kisa Hoto: Seyi Tinubu, Atiku Abubakar Isah
Source: Twitter
"Zargin da na yi cewa Seyi Tinubu ya jagoranci 'yan daba zuwa wurin bikin rantsar da ni, yanzu na tabbatar da cewa ba gaskiya ba ne.
"Bincike na ya nuna cewa Mr. Seyi, ɗa ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bai ma je ko da kusa da wajen ba,” in ji Atiku.

Atiku ya ba Seyi Tinubu hakuri a fili

Ya kuma yi amfani da wannan dama wajen neman afuwar Seyi Tinubu da sauran wadanda zargin ya shafa.

Atiku ya bayyana cewa yanzu ya gane gaskiya, kuma yana fatan a yafe masa bisa kuskuren da ya aikata.

Gwamnan Legas ya nemi afuwar jama'a

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu , ya nemi afuwa daga ‘yan Legas da suka fuskanci matsanancin cinkoso sakamakon aikin gyaran gadar Independence.

Gwamnan ya ba da haƙuri ne yayin da ya kai ziyarar duba aikin gadar domin gane wa idonsa halin matsin da aka jefa mutane saboda cunkoso.

Ya ce ya dauki nauyin abin da ya faru a madadin gwamnati, a matakin jiha da na tarayya, amma ya kamata mutane su gane muhimmancin aikim

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262