'Ku Kiyaye': Sheikh Ya Ja Kunnen Bulama Bukarti kan Kisan Limami a Zamfara

'Ku Kiyaye': Sheikh Ya Ja Kunnen Bulama Bukarti kan Kisan Limami a Zamfara

  • Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya caccaki Bulama Bukarti kan zargin cewa malamai sun yi shiru bayan kisan limamin Maru da iyalansa a Zamfara
  • A cewar Shehin, ba dole ba ne malamai su yi magana kan kowanne lamari, kuma bai dace a ci mutuncin su ba haka kawai
  • Ya ce mutane da dama, ciki har da malamai, ba su san an kashe limamin ba, amma wasu yan jarida suna zagin su da rashin yin magana

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya yi martani ga kalaman Bulama Bukarti bayan kisan limami a Zamfara.

Sheikh ya ce abin takaici ne kowa ya debo bola sai ya jibge kan malamai ba tare da yi musu adalci ba.

Sheikh ya gargadi Bulama Bukarti
Sheikh Aliyu ya ja kunnen Bulama Bukarti kan kisan limami. Hoto: Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna, Bulama Bukarti.
Source: Facebook

Sheikh Aliyu Kaduna ya fadi haka ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Zancen kisan Hausawa a Edo ya dawo sabo, Sanata Barau ya yi magana a majalisa

Abin da Bulama Bukarti ya ce kan malamai

Hakan ya biyo bayan zargin da Bulama Bukarti ya yi a wani bidiyo cewa babu malamin da ya yi magana bayan kisan limamin a Zamfara.

Bukarti na magana ne bayan kisan limamin Maru a Zamfara da yan bindiga suka yi da iyalansa.

Sai dai kalaman Bukarti sun jawo magana inda aka yi ta masa raddi da kawo shaidar cewa wasu malamai sun yi magana kamar Sheikh Murtala Bello Asada.

Sheikh Aliyu Kaduna ya yi martani ga Bulama

Shehin malamin ya ja kunnen yan jarida da masu kiran kansu masu fashin baki da su kiyayi cin mutuncin malamai haka nan.

'Karkashin wannan muke jan kunnen yan jaridu da wadanda ke kiran kansu yan fashin baki su kiyayi cin mutuncin malamai.
"Da yawa daga cikin malamai ba su ma san abin da ke gudana ba, amma wai ana zargin an kashe limami amma duk malamai sun yi tsit.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi halin da matsalolin Najeriya suka jefa shi a farkon mulkinsa

"Wannan ba mutuntawa ba ne, saboda ko wadanda ba Musulmi ba aka kashe malamai ba su yi shiru, dk duniya babu inda ya kai malaman Najeriya tsayawa kan hakkin wanda aka cutar da shi.
"Yanzu wannan magana da nake yi wani a lokacin zai san an kashe limamin saboda bai ma san hakan ya faru ba, amma wani dan jarida dan dadi baki kawai ya ce malamai sun yi shiru."
Sheikh ya ja kunnen Bulama Bukarti kan kisan liman
Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya gargadi Bulama Bukarti. Hoto: Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna.
Source: Facebook

Sheikh Aliyu ya gargadi mutane game da malamai

Malamin ya ce bai kamata kowa ya debo bola ya zo ya jibge kan malamai ba saboda ba hakkinsu ba ne dole sai sun yi magana.

"Na farko a sani ba hakkin malamai ba ne yin magana duk lokacin da aka kashe wani mutum, ka da ka ɗauka cewa wajibin malamai ne.
"Babu wanda ya siyawa malami waya ko data da zai ce sai sun yi magana ya ji, mutane suna sha'awa da jin dadi su fito su ci mutuncin malamai."

Sheikh Aliyu ya jinjinawa ɗaliban Dutsen Tanshi

A baya, mun ba ku labarin cewa Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya yabawa daliban marigayi Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi bisa mutunta wasiyyar da ya bari.

Kara karanta wannan

'Babu wuta ko aljanna': Malamin addini ya kawo sabuwar huduba yayin ibada

Shehin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a Facebook, ranar Asabar 5 ga watan Afrilu 2025, bayan rasuwar malamin.

Sheikh Ibrahim ya ce abin yabawa ne ganin yadda daliban suka tsaya kan wasiyyar malaminsu lokacin ta'aziyyarsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.