Kwana Ya Kare: Najeriya Ta Sake Rasa Jagora, Wani Basarake Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Jihar Oyo da Najeriya sun yi rashin jagoran al'umma, Baale na Unguwar Oluyole da ke ƙaramar hukumar Ibadan ta Kudu maso Yamma ya rasu
- Rahotanni sun tabbatar da cewa Cif Yemi Ogunyemi ya riga mu gidan gaskiya ne da safiyar yau Laraba, 7 ga watan Mayu, 2025
- Marigayin fitaccen ɗan jarida ne wanda ya shafe shekaru yana aiki da gidan talabijin na tarayya watau NTA
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ibadan, jihar Oyo - Ɗaya daga cikin masu rike da sarautar "Baale" a ƙasar Ibadan, Baale na Oluyole Estate da ke ƙaramar hukumar Ibadan ta Kudu maso Yamma, Cif Yemi Ogunyemi ya rasu.
An sanar da rasuwar basaraken ne da safiyar yau Laraba, 7 ga watan Mayu, 2027 a Ibadan, babban birnin jihar Oyo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan
Rikicin shugabanci: Jam'iyya ta dakatar da gwamna da ƴan Majalisar Tarayya 5 nan take

Source: Facebook
Marigayin wanda fitaccen ɗan jarida ne, ya shafe shekaru da dama yana aiki da gidan talabijin na Tarayya watau NTA, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har zuwa lokacin rasuwarsa, Ogunyemi yana daga cikin manyan mambobin Majalisar sarakunan Baale ta Ibadanland.
Ya kuma kasance ɗaya daga cikin masu fafutukar raya al’adun Yarbawa. Rasuwarsa babban rashi ne ga al’umma da kuma kafafen yaɗa labarai a Najeriya.
Majalisar Baale ta tabbatar da mutuwar
Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Ibadanland, Baale Wasiu Aare, ya tabbatar da rasuwar Ogunyemi a wata sanarwa da ya fitar yau Laraba a Ibadan.
Ya ce kafin rasuwarsa, Cif Yemi Ogunyemi shi ne mataimakin shugaban Majalisar sarakunan Baale na yankin ƙasar Ibadan a jihar Oyo.
Basaraken ya kasance masani a fagen watsa labarai, tsohon ɗan jarida kuma ɗaya daga cikin manyan masu ba da gudummawa wajen ci gaban al’adun Yarbawa da Ibadan gaba ɗaya.
Majalisar ta baygana rashinsa a matsayin babban rashi ga al’ummar Ibadan, jihar Oyo da ma Najeriya baki ɗaya, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Sarakuna sun miƙa ta'aziyya ga iyalan mamacin
Har ila yau majalisar sarakunan ta ce marigayin mutum ne nagari, wanda al'ummarsa suka daɗe suna alfahari da shi.
Sanarwar ta ce:
“Cike da alhini, Majalisar Sarakunan Gargajiya na Ibadanland na sanar da rasuwar mataimakin shugaban mu, jigo a Ibadan, ƙwararren ɗan jarida, tsohon mai watsa shirye-shirye da aka fi sani da Enbalaya, uba gare mu kuma jagora, Baale Yemi Ogunyemi, Baale na Oluyole.”
Tuni da mutane daga ɓangarori daban-daban musamman a jihar Oyo suka fara jimami tare da miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwan marigayin.
Tsofaffin shugabanni 2 sun rasu a Filato
A wani rahoton, kun ji cewa jihar Filato ta rasa jagorori biyu kusan lokaci guda da tsohon mataimakin gwamna da tsohon shugaban ƙaramar hukuma suka rasu.
Gwamnan jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang ya kai ziyara gidajen mamatan, inda ya rarrashi iyalansa ta'aziyya da addu'ar Allah ya ba su haƙurin wannan rashi.
Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana mutanen biyu a matsayin jarumai da suka yi wa al'umma hidima a lokacin rayuwarsu.
Asali: Legit.ng
