An Fara Kera Makaman Yaki a Najeriya, Sufeton 'Yan Sanda Ya Ziyarci Masana'antar
- Sufeto Janar na ‘yan sanda ya kai ziyarar gani da ido kan wasu kayayyakin tsaro da masana fasaha na cikin gida suka kirkira a Kuje, Abuja
- Ya tabbatar da rundunar ‘yan sanda na da niyyar hada gwiwa da kamfanonin fasaha na cikin gida domin bunkasa hanyoyin yaki da laifi
- Hakan na zuwa ne bayan haramta shigo da kayayyakin da ake hadawa a Najeriya daga waje da Bola Tinubu ya kafa a makon da muke ciki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A kokarinta na amfani da sababbin hanyoyin yaki da laifi, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kai wata muhimmiya ziyarar duba makaman da aka kera a Najeriya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa masana fasaha na gida Najeriya ne suka samar da kayayyakin a Kuje, babban birnin tarayya Abuja.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanan ne a cikin wani sako da rundunar 'yan sandan Najeriya ta wallafa a shafinta na X.
Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, tare da wasu manyan jami’an rundunar, ne suka kai wannan ziyarar ranar Talata, 6 ga Mayu, 2025.
A yayin ziyarar, an gabatar da wasu sababbin fasahohin leken asiri, jiragen yaki marasa matuka, da sauran na’urorin zamani da aka kirkira a gida.
’Yan sanda za su hada gwiwa da masana fasaha
IGP Egbetokun ya bayyana cewa rundunar ‘yan sanda ta shirya tsaf domin hada kai da masana fasaha na Najeriya wajen kirkirar kayan tsaro da suka dace da bukatun kasar.
Shugaban 'yan sandan ya ce:
“Wannan shiri yana cikin dabarun rundunar wajen inganta aikinta, da kuma tabbatar da amincewar jama’a ta hanyar amfani da sababbin fasahohi a yaki da laifi.”

Source: Facebook
Masana fasahar da ke cikin gida sun yaba da wannan kokari, suna masu cewa hakan zai bude kofar kirkire-kirkire da samar da ayyukan yi ga matasa.
Matakin Tinubu na karfafa kere-kere a gida
Ziyarar IGP ta zo ne bayan Bola Ahmed Tinubu ya haramta shigo da wasu kayayyaki da ake iya samar da su a cikin gida.
Shugaba Bola Tinubu ya dauki matakin ne domin bunkasa masana’antu da karfafa tattalin arzikin kasa.
Duk da cewa wasu na ganin mataki zai taimaka wajen rage dogaro da kayayyakin waje da kuma inganta amfani da wasu tsare-tsaren tsaro, wasu sun soke shi.
Rahoton Punch ya bayyana cewa Atiku Abubakar ya kalubalanci shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara aiki da motocin da aka kera a Najeriya maimakon amfani da wadanda aka kera a waje.
An kwato makamin ISWAP a Borno
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sa-kai na CJTF sun yi wani kazamin fada da mayakan 'yan ta'addan kungiyar ISWAP a jihar Borno.
Rahotanni sun tabbatar da cewa jami'an CJTF sun kwato wata babbar bindiga da 'yan ta'addan ke amfani da ita wajen harbo jirgi.
Baya ga haka, dakarun CJTF sun kashe wasu daga cikin 'yan ta'addan yayin da suka fafata kuma sun kwato wasu babura da suke aiki da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

