Tallafin Fetur: Kawu Sumaila Ya Wanke Tinubu, Ya Daurawa Buhari Laifi
- Sanata Kawu Sumaila ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya cire tallafin mai, ba Shugaba Bola Tinubu ba
- Ya ce kasafin kudin shekarar 2023 ya tanadi kudin tallafi ne kawai daga Janairu zuwa Yuni, kuma daga lokacin aka dakatar da tallafin gaba daya
- Sumaila ya ce sauya jam’iyya daga NNPP zuwa APC ba sabon abu ba ne a siyasar Najeriya, domin mutane da dama suna sauya sheka a lokuta dabam
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Abdulrahman Kawu Sumaila ya tayar da kura bayan bayyana cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ce ta cire tallafin man fetur, ba ta Bola Tinubu ba.
Sanatan ya kuma yi bayani kan sauya sheka da ya yi daga jam'iyyar NNPP mai mulki a Kano zuwa APC.

Source: Facebook
Kawu Sumaila ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV, wanda Legit Hausa ta bibiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cire tallafin man da Tinubu ya sanar ranar farko da ya hau mulki a watan Mayu 2023 ya jawo karuwar farashin abinci da sufuri a fadin Najeriya.
Buhari ya cire tallafin mai inji Kawu Sumaila
A cewar Kawu Sumaila, gwamnatin Buhari ce ta cire tallafin mai tun kafin mika mulki, domin babu kudin tallafi a rabin karshe na kasafin kudin shekarar 2023.
Sanatan ya ce:
“Tallafin mai a kasafin kudin Buhari na 2023 daga Janairu zuwa Yuni ne kawai.
"Bayan wannan lokaci babu kudin tallafi. Abin da Shugaba Tinubu ya yi kawai sanarwa ce ta cire tallafi.”
A cewarsa, wannan na nufin gwamnati ta dade ba ta biyan tallafin mai ba tun bayan karshen Yuni 2023, kafin Tinubu ya bayyana hakan a fili.
Halin da aka shiga bayan cire tallafin mai
Cire tallafin man fetur ya jefa Najeriya cikin matsin tattalin arziki da jama’a ke fuskanta wanda ya hada da tashin farashin kayayyaki da dama.
'Yan Najeriya sun yi kira ga Bola Tinubu ya maido da tallafin amma ya ce ya kawo tsare tsare da za su rage radadin cire tallafin da ya yi.

Source: Twitter
Sauya shekar Sumaila daga NNPP zuwa APC
Game da sauya jam’iyya da ya yi daga NNPP zuwa APC, Sanata Sumaila ya ce siyasar Najeriya ba a kan akida take ba, don haka canjin jam’iyya ba abin mamaki ba ne.
Tribune ta wallafa cewa Sanata Kawu Sumaila ya ce:
“Jam’iyyun Najeriya ba su da akida a tsare-tsarensu. Wannan ya sa sauya sheka ba wani sabon abu ba ne a siyasar kasar nan.”
Kamfanonin shinkafa sun kokawa Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan kasuwa masu casar shinkafa sun yi kira ga Bola Ahmed Tinubu kan karyewar farashi.
Masu gyara shinkafa a Arewacin Najeriya sun bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta sake nazari kan tsare tsaren gwamnatin Muhammadu Buhari.
Wani mai masana'antar sarrafa shinkafa a jihar Kebbi ya ce sun fara rufe wuraren aiki saboda karyewar farashin kayan abinci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


