Zancen Kisan Hausawa a Edo Ya Dawo Sabo, Sanata Barau Ya Yi Magana a Majalisa

Zancen Kisan Hausawa a Edo Ya Dawo Sabo, Sanata Barau Ya Yi Magana a Majalisa

  • Sanata Barau Jibrin ya mara baya ga kudurin bincike kan kisan wasu mafarauta 16 da aka yi a jihar Edo cikin watan Maris 2025
  • Ya bayyana yadda lamarin ya tada hankalin al’umma a faɗin ƙasar nan, duk da gwamnatin tarayya da na jihohi sun kawo dauki
  • Barau Jibrin ya ce dole ne a gurfanar da masu laifin, tare da bukatar dokar da za ta daidaita harkokin 'yan farauta a ƙasa baki ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A zaman majalisar dattawa na ranar Talata, Sanata Barau Jibrin ya mara baya ga kudurin Sanata Kawu Sumaila dangane da kisan gilla da aka yi wa wasu mafarauta a Edo.

Mafarauta 16 ne suka rasa rayukansu a garin Uromi na jihar Edo cikin watan Maris, abin da ya tayar da kura a sassan Najeriya gaba daya.

Kara karanta wannan

Iyalan mafarutan Kano da aka babbake a Uromi sun ji shiru, sun yi zanga zanga

Barau
Barau ya yi magana kan Hausawan da aka kashe a Edo a majalisa. Hoto: Barau I Jibrin
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan ya tunatar da yadda ya kai ziyara ga iyalan mamatan a Kano, inda ya bayar da tallafin Naira miliyan 16, tare da alkawarin bin diddigin lamarin har sai an hukunta masu laifin.

Kisan Edo: Barau ya nemi hukunta masu laifi

Sanata Barau ya jaddada cewa abu mafi muhimmanci shi ne tabbatar da cewa wadanda suka aikata wannan danyen aiki sun fuskanci hukunci mai tsanani domin zama izina ga wasu.

Ya yaba da irin namijin kokarin da gwamnan jihar Edo ke yi, tare da hadin gwiwar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro, don kamo wadanda suka aikata aika-aikar da ta girgiza ƙasa.

A cewarsa, hadin kan da suka nuna ya taimaka wajen rage zafin damuwa da bacin ran da mutane ke ciki tun bayan faruwar lamarin da ya auku.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya gano yadda gwamnatocin Najeriya ke jawo talauci a kasa

Mafarauta na bukatar tsari inji Barau

Barau Jibrin ya bayyana cewa wadanda aka kashe mafarauta ne na gargajiya, wadanda sana’arsu ta kai su daga Arewa zuwa Kudancin kasar don neman namun daji.

Ya ce irin wadannan ‘yan farauta suna yawo a sassa daban-daban na Najeriya, amma rashin tsarin doka na iya jefa su cikin hadari kamar yadda ya faru.

Kuma ya bukaci majalisar dattawa da ta gaggauta amincewa da kudirin doka da ke gaban ta domin tsara ayyukan masu farauta a fadin kasar.

Sumaila
Barau ya goyi bayan kudirin Kawu Sumaila kan kisan Hausawa a Edo. Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Source: Twitter

An bukaci tantance mafarauta a jihohi

A cewarsa, idan mafarauta za su ci gaba da yawo daga jiha zuwa jiha, dole ne a samar da tsari na tantance su da kuma tabbatar da cewa ana bibiyar ayyukansu.

Ya jaddada cewa akwai bukatar a tsaftace sana’ar farauta da kuma kara tsaro ga masu sana’ar, domin kaucewa aukuwar irin wannan kisan gilla a nan gaba.

Halin da ake ciki na batun kisan Uromi

Kara karanta wannan

Amarya ta kashe mijinta kwana 9 da ɗaura masu aure a Kano, an ji abin da ya faru

A cikin watan Maris 2025, wani mummunan hari ya faru a garin Uromi, jihar Edo, inda wasu mafarauta 16 daga Arewa suka rasa rayukansu a kisan gilla da ya tayar da hankula a fadin ƙasa.

Wadanda aka kashe sun kasance mafarauta da suka tafi kudu neman namun daji, amma suka fada hannun 'yan ta'addan da suka aikata ta'asar kisa da gangan a kansu.

Wannan lamari ya jawo cece-kuce da kira ga gwamnati da ta dauki mataki, duba da mummunan aikin da aka aikata.

Sanata Barau Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattawa, ya ziyarci iyalan mamatan a Kano, inda ya bayar da tallafin Naira miliyan 16, tare da bukatar bincike mai zurfi da hukunci ga masu laifi.

Ya goyi bayan kudurin Sanata Kawu Sumaila da ke neman kafa doka don tsara harkar farauta a Najeriya, yana mai cewa rashin tsari ne ya jefa mafarautan cikin haɗari.

Gwamnatin jihar Edo da jami’an tsaro sun tabbatar da kama wasu da ake zargi, kuma gwamnati ta sha alwashin gurfanar da su.

An bukaci tantance mafarauta da saka dokokin tsaro don kare rayukan masu sana’ar. Wannan lamari ya jaddada bukatar tsare rayukan ’yan Najeriya ko ina suke.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari mai zafi Filato, sun afkawa mutane suna barci

Kwankwaso ya hadu da Barau Jibrin

A wani rahoton, kun ji cewa jagoran NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya hadu da Sanata Barau Jibrin a Abuja.

An hango Rabiu Kwankwaso da tawagar 'yan Kwankwasiyya na gaisawa tare da Barau Jibrin a filin jirgin sam a hanyar zuwa Borno.

Duk da cewa haduwa ce ta kan hanya, lamarin ya ba mutane mamaki, musamman ganin yadda suke murmushi ga junansu a lokacin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng