Taron FEC: Tinubu Ya Rantsar da Sabon Shugaban NASC da Wasu Mutum 14 a Aso Villa

Taron FEC: Tinubu Ya Rantsar da Sabon Shugaban NASC da Wasu Mutum 14 a Aso Villa

  • Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da sabon shugaban hukumar NASC, Dakta Enyiekere, kwamishinoni 12 da manyan sakatarori biyu
  • Dakta Enyiekere, ƙwararre a fannin muhalli, da kwamishinoni 12, waɗanda suka fito daga shiyoyin siyasa shida, za su yi aiki na shekaru biyar da za a iya sabuntawa.
  • Bayan rantsar da NASC, Tinubu ya rantsar da sakatarori biyu daga Oyo da Jigawa, kuma an yi shiru don girmama tsohon minista Dubem Onyia a taron FEC.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da sabon shugaban hukumar majalisar tarayya (NASC), Dakta Saviour Enyiekere, kwamishinoni 12, da manyan sakatarori biyu.

Bikin rantsarwar, wanda ya gudana a Fadar Aso Rock Abuja, ya kasance a sassa biyu kafin a fara taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC).

Kara karanta wannan

Musa Kwankwaso ya faɗi maƙarƙashiyar da ake shiryawa NAHCON, Sheikh Pakistan

Tinubu ya rantsar da sababbin shugabannin hukumar NASC da manyan sakatarori 2
Shugaba Tinubu yana jagorantar taron majalisar zartarwa na Najeriya a Aso Villa, Abuja. Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Tinubu ya rantsar da shugabannin NASC

A tashin farko, Tinubu ya fara rantsar da Dakta Enyiekere da kwamishinoni 12, waɗanda suka fito daga shiyoyin siyasa shida, kamar yadda aka wallafa a shafin gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce Dakta Enyiekere ya kasance ƙwararre a fannin muhalli, kuma shi ne tsohon mataimakin shugaban ma’aikatan shugaban majalisar dattawa.

Kwamishinonin da aka rantsar na hukumar sun haɗa:

  1. Suleiman Othman Hunkuyi - Arewa maso Yamma
  2. Yusuf A. Yusuf Tabuka - Arewa maso Yamma
  3. Aminu Ibrahim Malle - Arewa maso Gabas
  4. Alhaji Lawan Maina Mahmud - Arewa maso Gabas
  5. Mark Hanmation Tersoo - Arewa ta Tsakiya
  6. Salihu Umar Agboola Balogun - Arewa ta Tsakiya
  7. Taiwo Olukemi Oluga - Kudu maso Yamma
  8. Afeez Ipeza-Balogun - Kudu maso Yamma
  9. Dakta Nnanna Uzor Kalu - Kudu maso Gabas
  10. Festus Ifesinachi Odii - Kudu maso Gabas
  11. Patrick A. Giwa - Kudu maso Kudu
  12. Mrs. Mary Ekpenyong - Kudu maso Kudu

Kara karanta wannan

Wike ya zargi gwamna Fubara da jawo wulakanta matar Tinubu a Rivers

Rahoton ya kara da cewa sabon shugaban hukumar da kwamishinonin za su yi aiki na tsawon shekaru biyar, wanda da za a iya sabuntawa.

Tinubu ya rantsar da manyan sakatarori 2

Bayan rantsar da shugaban NASC da kwamishinoni, Tinubu ya rantsar da manyan sakatarori biyu na tarayya:

  • Mista Rafiu Olarinre Adeladan - Oyo
  • Dakta Muktar Mohammed - Jigawa.

Kafin fara taron FEC, mambobin majalisar sun girmama tsohon ministan harkokin waje, Dubem Onyia, wanda ya rasu a ranar 10 ga Maris.

Taron FEC, wanda shugaban ƙasa ya jagoranta, ya samu halartar mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da shugaban ma’aikatan shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Wadanda suka halarci taron FEC

Sauran wadanda suka halarta sun hada da sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume, da mai ba Tinubu shawara kan harkokin tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu.

Ministocin da suka halarci taron sun haɗa da ministan kuɗi da tattalin arziki, Wale Edun; ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki, Sanata Atiku Bagudu, da ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristocin Najeriya ta dare gida 2, an samu hatsaniya kan Seyi Tinubu

Taron FEC na jiya shi ne taro na farko tun ranar 3 ga Maris, lokacin da majalisar ta amince da Naira biliyan 2.5 don sayen kayan aikin sa ido da za su taimaka a dakile hakar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba a faɗin Najeriya.

A zaman na ranar 3 ga Maris, gwamnati ta kuma amince da fitar da Naira biliyan 1.09 don inshorar muhimman kadarori da ma'aikata a filayen jiragen sama na tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com