Majalisar Kano Ta Yarda da Kafa Hukumar Lantarki, Jihohin Arewa 3 za Su Fita a Duhu

Majalisar Kano Ta Yarda da Kafa Hukumar Lantarki, Jihohin Arewa 3 za Su Fita a Duhu

  • Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kudurin kafa hukumar lantarki, wacce za ta hada Kano, Katsina da Jigawa a karkashin inuwa daya
  • Wannan doka za ta ba jihohin dama wajen amfani da hanyoyin samar da wutar lantarki kamar rana, iska da ruwa domin inganta rayuwar al’umma
  • Baya ga haka, majalisar dokokin ta bukaci gwamnatin Kano ta taimakawa gidaje sama da 200 da ambaliya ta shafa a karamar hukumar Doguwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kudurin kafa Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Kano a zaman majalisar na ranar Litinin, 5 ga Mayu, 2025.

Rahotanni sun nuna cewa shugaban majalisar, Rt. Hon. Ismail Falgore ne ya jagoranci zaman majalisar yayin amincewa da kudirin.

Kara karanta wannan

Bashin Naira tiriliyan 4: Gwamnatin Najeriya ta fara hararo karin kudin wuta

Majalisar Kano ta amince da kafa hukumar samar da wutar lantarki.
Majalisar Kano ta amince da kafa hukumar samar da wutar lantarki. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Leadership ta rahoto cewa kudirin ya samu goyon baya daga yawancin ‘yan majalisar jihar, kuma yanzu ya zama doka da ke shirin tafiya zuwa hannun gwamna domin sa hannu.

Dokar za ta ba jihohin Kano, Katsina da Jigawa damar inganta samar da wutar lantarki ta hanyoyi daban-daban na zamani don taimaka wa rayuwar al’umma da bunkasa tattalin arziki.

Ayyukan hukumar lantarki ta jihar Kano

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon. Lawan Husseini, ya bayyana wa manema labarai cewa dokar za ta kawo ci gaba mai ma’ana ga jihohin uku; Kano, Jigawa da Katsina.

Jihohin za su amfana ta hanyar rage farashin wuta da kuma karfafa masana’antu da cibiyoyin kiwon lafiya da tsaftar ruwa.

Hon. Lawan Husseini ya ce hukumar za ta kunshi shugaba, daraktan gudanarwa da mataimakinsa.

Kowace jiha za ta ba da wakilai uku a kwamitin gudanarwa, kuma shugabancin hukumar zai zama na karba-karba daga ihohin uku domin yin wa’adin shekara hudu.

Kara karanta wannan

Wike ya zargi gwamna Fubara da jawo wulakanta matar Tinubu a Rivers

Wanene wanda zai shugabanci hukumar

Dangane da cancantar daraktan gudanarwa, Hon. Lawan Husseini ya ce dole ne ya kasance yana da gogewa a harkar samarwa, rabawa da kula da lantarki na akalla shekara 10.

Hon. Lawan ya ce wannan zai taimaka wa kananan masana’antu da manyan cibiyoyi su samu wuta sosai, kuma zai rage dogaro da tsarin raba wuta na kasa da ya dade yana fama da matsaloli.

Majalisar Kano ta bukaci agaji bayan ambaliya

A wani bangare na zaman, majalisar ta bukaci gwamnatin Kano ta hanzarta kai agaji ga gidaje fiye da 200 da iftila’in ambaliya ya shafa a garin Doguwa.

Dan majalisa mai wakiltar yankin, Hon. Salisu Mohammed, ya ce abin ya fi shafar al’ummomin Bahuwa, Rafin Dadi, Maraku da Asada da ke unguwar Tsohuwa.

Abba Kabir
Majalisar Kano ta bukaci Abba ya tallafawa wadanda ambaliya ta shafa. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Ko da yake babu asarar rai, ya bayyana cewa gidaje, makarantun gwamnati da wuraren ibada sun lalace, inda ambaliya ta yaye rufin gine-gine da dama.

Minista ya ce a saurari karin kudin wuta

Kara karanta wannan

An kama wanda aka dauka haya domin kashe kashe a Filato da bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa ministan makamashin Najeriya, Bayo Adelabu ya ce dole ne a samu karin kudin wuta.

Bayo Adelabu ya bukaci 'yan Najeriya da su zauna cikin shiri domin biyan cikakken kudin wutar da suke sha.

Adelabu ya ce dole hukuma ta dauki matakin da ya dace wajen tabbatar da cewa harkokin wutar lantarki basu lalace ba a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng