Dattawan Zamfara Sun Taso Gwamna Dauda a Gaba ana Batun Dokar Ta Baci
- Ƙungiyar dattawan Zamfara ta nuna damuwa kan yadda ake muzgunawa wasu zaɓaɓɓun ƴan majalisar dokokin jihar
- A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta zargi Dauda Lawal da yin amfani da ɓangaren shari'a domin ƙuntatawa ƴan majalisar
- Ƙungiyar ta buƙaci gwamnan da ya bi hanyar neman sulhu domin warware rikicin da ke tsakaninsa da ƴan majalisar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Ƙungiyar dattawan Zamfara ta nuna yatsa ga Gwamna Dauda Lawal na jihar.
Ƙungigar ta zargi Gwamna Dauda Lawal da shirya wani ƙullin siyasa da ake yi wa ƴan majalisar dokokin jihar guda tara ta hanyar amfani da kotu domin danne musu haƙƙinsu.

Source: Twitter
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin ƙungiyar, Dr. Abdulmumin Kamil Gusau, ya fitar a ranar Lahadi, 4 ga watan Mayun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dattawan Zamfara sun jefi gwamna da zargi
Dr. Abdulmumin Kamil Gusau ya bayyana matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka a matsayin abin damuwa kuma abin kunya.
Ƙungiyar ta zargi babbar alƙalin kotun majistare, Halima Jaafar Mikaila, da bayar da sammacin kama ƴan majalisar ba tare da ba su takarda ko gabatar da tuhuma a hukumance ba, wanda hakan ya saɓawa doka.
“Muna cikin damuwa kan yadda gwamnatin jihar ke amfani da kotu wajen cin zarafin ƴan majalisar da aka zaɓa bisa doka."
"Waɗannan ƴan majalisa ana muzanta su ne saboda suna yin ayyukansu bisa tsarin doka tare da fito da kura-kurai kan yadda ake tafiyar da mulki domin amfanin jama’a."
- Dr. Abdulmumin Kamil Gusau
Ƙungiyar ta bayyana cewa ƴan majalisar da abin ya shafa waɗanda suka fito daga jam’iyyar PDP mai mulki da kuma APC da ke adawa, sun riga sun shigar da ƙara a kotun ɗaukaka ƙara da ke Sokoto.
Haka kuma sun kai ƙorafi ga hukumomi da dama, ciki har da Sufeto Janar na ƴan sanda, Darakta Janar na hukumar DSS, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro da majalisar tarayya, domin neman shiga cikin lamarin.
Duk da waɗannan matakai da suka dauka, kungiyar ta zargi kotun majistare da ci gaba da bayar da umarnin kama su, wanda hakan a cewarta ya saɓa doka.

Source: Facebook
Wace shawara aka ba Gwamna Dauda?
Ƙungiyar ta buƙaci Gwamna Dauda Lawal da ya dakatar da muzguna musu sannan ya nemi zaman sulhu da ƴan majalisar domin warware rikicin cikin lumana.
"Jam’iyyar APC za ta ci gaba da tsayawa kan doka, kuma ba za ta lamunci amfani da kotu domin cimma manufar siyasa ba."
"Mun jajirce wajen ƙin yarda da duk wani yunkuri na razana ƴan majalisa saboda suna magana kan taɓarɓarewar tsaro a yankunansu, matsalar da gwamnatin jihar ta kasa magancewa."
- Dr. Abdulmumin Kamil Gusau
Gwamna Dauda ya musanta shirin barin PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi magana kan jita-jitar da ake yaɗawa mai cewa zai bar jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan
Hadakar Atiku ta fara gigita APC, an fallasa abin da Tinubu ke kullawa 'yan adawa
Gwamna Dauda Lawal ya ƙaryata jita-jitar inda ya ce ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a cikinta.
Ya ba da tabbacin cewa shi cikakken mamba ne a PDP kuma sannan zai ci gaba da kasancewa a cikinta.
Asali: Legit.ng

